Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
209. Nasaba dai abin nufi sai makusanci,
Na zaman tare ne
walau dai mazumunci,
Asali shi ka sa
kare alli zai ci,
Ita
nasaba abin nufi nuna kusanci,
Na alaƙar jini walau
nasabantarwa.
210. Sa natsuwa ka duba
misalin
nan,
Ga dokin
kara da dokin ƙarhe nan,
Danbun dankali da dambun
rogo nan,
Jirgin laka, hadda keken ƙarfe nan,
Ga wundin kaba Bukar na saƙawa.
211. Su biyu an ka sa suna da kusanci ne,
Wandon ƙarfe, ganinmu ya fi a kece ne,
Jirgin leda misalce, bai keta hazon ne
Rawanin
ɓartake naɗinsa jidali ne,
Ga shi gudan tuli naɗin bai kamewa.
212. Aikin ‘n’ da ɗai ta nuna, zumunci ne,
‘Yan matan garin
ga jirgin laka ne,
Ba sa kai ka
ganga, ko kai malam ne,
Yaran
zamaninmu wandon roba ne,
Ba wani
kwankwason da ba sa kamewa.
213. In
ka fahimta duk a nan ‘n’ nasaba ce,
A misalan da mun ka sa farkon
zance,
Dokin ƙarfe an ka sanya da kwantance,
Doki wanda an ka sa ya ya
kasance?
Dokin nan kara yake nasabantarwa.
214. Shi wundin kaba, kaba ce ta haɗa shi,
Nasaba tai tana kaba an gane shi,
Ita ce assali da an ka yi saƙar shi,
‘n’ ta nuna duk
alaƙa da kabar shi,
Matuƙar ba shi ba kaba
ba zaunawa.
215. Rawanin
nan da ɓartake aka saƙa
shi,
Nasaba tai zare, da shi aka ƙera shi,
Ai asalinsa yanzu
kan an nuna shi,
Kwai dangantakar
da tan nuna silar shi,
In an zare ɓartake babu naɗawa.
216. Yaran
zamani kamar yadda akan ce,
Yaran nan a zamani sun ka kasance,
Daman dai a Hausa,
an bayyana zance,
Yara
da zamani zumuntar ƙarni ce,
Ba ƙarnin da bai da
yara na nunawa.
217. Dudduba abin ga don ka yi ganewa,
Za mu tarar da ‘n’ tana dangantawa,
Kalmomi biyun zumu
take daɗa nunawa,
Don
haka ‘n’ a nan tana nasabantarwa,
Na
bayanin abin da duk za shi biyowa.
218. A bayanai da mun ka yo na rubutawa,
‘n’ tai ƙoƙarin rawarta ta takawa,
Kuma ta fayyace
misalin nunawa,
Za ka
ji ‘n’ tana fita ba sauyawa.
Gun lafazinta ha kaza gun zanawa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.