Ticker

    Loading......

Daurin ‘r’ A Nasaba

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

219. Harafin ‘r’ akan nasabta shi a zance,

 Kuma ‘r’ za a sa ta zauna a rubuce,

Sai dai nasabar sa na jinsin macce,

‘n’ ce ke ga masculine, ‘r’ kuma macce,

  Hasali ma ga zantukan matuntawa.

 

220. Duba yanzu ga misalin gane ta,

Rigar raraka da hular silikinta,

 Riga mace ce a lura da jinsinta,

 Haka hula macce ce a ga tsarinta,

  Gonar yakuwa tana son bushewa.

 

221. ‘R’ da ta zo a ɗaure nan sai a kula ta,

 Hular nan da silki ne aka ɗinka ta,

 Gona ko da yakuwa aka shuke ta,

 Lura a nan da ‘r’ aka daddanganta,

  Amfaninta duk a nan nasabantarwa.

 

222. In ‘r’ ta taho tana nasabantarwa,

 Dole a sa ta kana ba a sauyawa,

Ba rikiɗa takai ba nan ko nashewa,

Ba sautin da za a sa don ƙarawa,

  Ba wasali take kwaɗai ba ga tsarawa.

Post a Comment

0 Comments