Daurin Tagwayen Bakake

    Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

    About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

    Ɗaurin Tagwayen Baƙaƙe

    115. Bayan ƙi-jima wanda mun ka ga tsarinshi,

     Ka ga tagwan baƙi ana iya ɗaure shi,

     To amma a lura can gun ɗaure shi,

     An yo ƙa’ida daɗai gun zana shi,

      Tamkar kowane baƙi gun Hausawa.

     

    116. Sai dai wanda za ya ɗauri ya kiyaye,

     Ƙi-jima su daban ne da tagwaye,

     Mu tuna dai baƙi biyu ke ga tagwaye,

     Sanda ka zo fage na ɗauri ga tagwaye,

    Ba dukkan tagwan ba ne aka ɗaurewa.

     

    117. Mai ɗaurin tagwan baƙi aiki na nan,

    Za shi bi ƙaidan rubutu shi ke nan,

    Ba kuma za shi sha gaba ɗaya sautin nan-

    Wato za a sa baƙin farko ke nan,

    Shi na biyun tagwan ya zan mai nashewa.

     

    118. Tsattsama ka gan ta ba tsatstsama ba,

     ‘S’ ɗin ‘t’ a nan ba za ta kasance ba,

     Sakkwato ce rubuce ba Sakwkwato ce ba,

     Ka ga daɗai tagwan ga ba za ya sake ba,

      ‘W’ ɗin nan guda ya zam ba ta fitowa.

     

    119. In ka lura mai gani ko saurare,

    Kwai doka da tash shigo dole a ware,

    To a wurin ga ga baƙaƙe uku jere,

    ‘K’, ‘k’, had da ‘w’ a nan sun zo tare,

      Ba wasali da yas shigo don kutsawa.

     

    120. Ka san Hausa itta ba ta da tsarin nan,

     Jeranton baƙi daɗai ba wasalin nan,

    In ka ga hakan ga to akwai ɗauri ke nan,

     In ba a nan ba, ba wurin da ake wannan,

    Sai na biyunsu ga shi nan zan ƙarawa.

     

    121. Duba misalin da zan daɗa ai shi nan,

    Haɗuwar ‘m’, da ‘t’, da ‘s’, tsaki ke nan,

     In ka fid da su alamar mts ke nan,

     Sauti ukku sunka zo wasali bai nan,

      Ba wasali cikinsu mai sa motsawa.

     

    122. Akwai wani ma guda da ya samu makwanci,

     In aka gwama ‘ƙ’ da ‘t’ ya zama ƙyacci,

     Duba sautukanga ba wasali mai ci,

     Ƙyacci ya fito ya bar miki zucci,

      Rai ya sosu dole ne ake ƙyaccewa.

     

    123. In an jera ‘m’ da ‘h’ wasali jaye,

     Nan ne za a samu ‘hm’, kalmar ɓoye,

     A misalan da sun ka zo duka jeranye,

     Ba wasali wurin ga duk sai a kiyaye,

    Harufan nan kawai a nan za a haɗawa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.