Ayar Motsin Rai (!)

    Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

    About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

    425. Motsin rai abin nufi sosa zukata,

     Kun san mun faɗe ta tsari da zubinta,

     To kuma ƙa’idar mu ta ce a sakata,

     Amma kuma dole sai ga muhallinta,

      Rai ya ɓaci dole fuska ka gwadawa.

     

    426. Fata na gare ku ku masu rubutu,

    Ku sanya ta rubuce domin a alamtu,

     Na san za ta taimaka can karatu,

    Susan rai idan ya tusga a rubutu,

      Ayar za a sa garai don ganewa.

     

    427. Ga misali ka zana tsaki ko ƙyacci,

     Ko wata kalma da ke da cikas zucci,

     Ko kuma wadda kay yi zargi ga macuci,

     Ko a taho da zantukan ɓacin zucci,

      Nan ayar ka bayyana don nunawa.

     

    428. Lura idan ka ce haba! Kayya! Yawawa!

     Mamaki ta ba ni Balkisu habawa!

     Kayya! Batun ga yanzu ai sai kwaɓewa,

     Ka lalata tarbiyarmu ta Hausawa!

      Assha! Baba hanƙure ban da bugawa.

     

    429. Shege! Ya wuce mu ya yi muna zamba,

    Sai ka ga ya fice ya faɗa bisa ɗamba,[1]

     In kuma ya shige tudu zai shiga gamba,[2]

     Eho! Bai hana wa mugu yin zamba,

      Wayyo! Bai hana ma yaro ƙarawa.

     

    430. Subhanal lazi! Idan ga ruɗewa,

     Ka yi salallami da sigar tafawa,

     Ka yi zugum a ranka ka ɗarsa tunawa,

     Mamaki ga zuciya ta yi gazawa,

      Kaico! In da tausayi dinga kulawa.

     

    431. Ka ji daki-daki wurin da ake sa ta,

     In ka zo wurin ka gane ka saka ta,

     Kuma doka ta zo ta ce sai a rubuta,

     Ka sani wansu za su ɗauka su karanta,

      Sai a kula da kyau misalan nunawa.



    [1] Ɗamba ciyawa ce da take fitowa tare da sassarƙewa a saman ruwa. Ana iya tattaka ta da sauri har a tsallake saman ruwa ba tare da an nitse ba.

    [2] Gamba nau’in ciyawa ce da take da gaɓoɓi. Tana da tsawo sosai.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.