Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
432. Kowace tambaya da aya aka yin ta,
Don a sanar da
wanda duk za ya karanta,
Ya zama wajibi da aya ka rubuta,
Can ƙarshenta zan kula nan
aka sa ta,
Sai an sa ta
tambaya za ta fitowa.
433. In ka yi tambaya gabanin amsawa,
In niyyarka
tambaya ga rubutawa,
Jimla za ta zo a
tsarin Hausawa,
Can ƙarshenta za ta zo da
alamtawa,
Ayar tambaya a
nan za ta fitowa.
434. In ka saka ta tambaya ta cika ke nan,
Ka gamsar da wanda
za ya karatun nan,
In ya lura za ya
gan ta rubutun nan,
Ba uzuri gare shi kuma ma da sannan,
Ba sauran abin faɗi sai amsawa.
435. Ga misali ka ce: “Ina za ku mutane”?
Kun yi dako-dako,
haba kai ku yi zaune,
Kuma kun yamutse,
ku yo jerin gwane,
Na yi kira gare ku
ƙauye da birane,
Me ke sa ana kira
ba ku fitowa?
436. Wa zai rena malami ba sauna ba?
Sai ko wanda bai
yi gadon ɗa’a ba,
Kai malam yi
hattara girmama babba,
Bi shi ka
kyautata, da ɗa’a kuma duba,
Wa ka gudun ubansa bai son tsinewa?
437. Wa ke yin ruwan sama
bayan Rabbi?
Malam na da
tambaya “Wa yaɗ ɗau carbi?”
Ko an sa ma wagga kaza ƙwan zabbi?
Gyashi[1] ba a yin
sa sai an cika tumbi,
Wa zai yi shi in
ciki bai ɗauka ba?
438. Wane ne da wacce koko da waɗanne?
Kun ƙyale ni ko gidan babu
mutane?
Ko ka ji ana faɗin Aliyu waliyi ne?
Shin ka samu wanga
zance ga mutane?
Wa yac ce? Da waf faɗa? Dinga kulawa.
439. Lura gaɓa guda takan ɗau ayar nan,
Shi ma ya taho
cikin dokokin nan,
Sannan kuma in ka
duba kalmar nan,
Kwai ma’ana gareta
ga fa misali nan,
Tamkar wa? Da me? Ga mai son ganewa.
440. Matuƙar tambaya ka yo sai ka uzurta,
Aya za ka sa wurin don ka alamta,
Sai ka taho ka
duba tsari ka saka ta,
Ba uzurin da zai
hana sai ka rubuta,
Saka aya wurinta
don tantancewa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.