Ticker

Ba Ta Son Wata Mu’amala Ta Haɗa Ta Da Namiji Ko Ta Soyayya Ce

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam, don Allaah wai menene illar macen da ba ta da abokan mu’amala sai mata kawai. Ba ta son wata mu’amala ta haɗa ta da namiji ko ta soyayya ce?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

A asali da ma ai abin da ya kamaci mace ke nan ta zama mai mayar da harkokinta da mu’amalarta da ’yan uwanta mata kawai. Ta yi magana da wasa da raha da cin abinci da ciniki da sauran harkoki dai da su. Wannan daidai ne, ban san wata magana da ta ƙyamatar da hakan ba.

Allaahumma! Sai dai ko in abokan hulɗa ko harkar ba matan kirki ba ne, ko kuma idan suna da shirin ƙulla waɗansu ayyukan assha ne da ba su dace da koyarwar Addini ba.

وَتَعَاوَنُوا۟ عَلَى ٱلۡبِرِّ وَٱلتَّقۡوَىٰۖ وَلَا تَعَاوَنُوا۟ عَلَى ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَ ٰ⁠نِۚ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ شَدِیدُ ٱلۡعِقَابِ

Kuma ku taimaki juna a kan alheri da taqawa, kuma kar ku taimaki juna a kan zunubi da ƙetare haddi, kuma ku ji tsoron Allaah. Haƙiƙa Allaah mai tsananin uƙuba ne. (Surah Al-Maaidah: 2)

Amma idan abin ya koma ga harkar soyayyar aure ce, to ai abu ne sananne cewa: Ita mace ba ta aure sai da namiji. Ko da kuma an ga cewa ba ta son mu’amala ta haɗa ta da wani namiji, haka nan dai za a janyo hankalinta har ta fahimci cewa: Abin da Allaah ya tsara kenan watau: Mace ta yi aure da namiji, kamar yadda Surah An-Nisaa’i: 23 ta bayyana

حُرِّمَتْ عَلَيْكُمْ أُمَّهَاتُكُمْ وَبَنَاتُكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ وَعَمَّاتُكُمْ وَخَالَاتُكُمْ وَبَنَاتُ الْأَخِ وَبَنَاتُ الْأُخْتِ وَأُمَّهَاتُكُمُ اللَّاتِي أَرْضَعْنَكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ مِنَ الرَّضَاعَةِ وَأُمَّهَاتُ نِسَائِكُمْ وَرَبَائِبُكُمُ اللَّاتِي فِي حُجُورِكُمْ مِنْ نِسَائِكُمُ اللَّاتِي دَخَلْتُمْ بِهِنَّ فَإِنْ لَمْ تَكُونُوا دَخَلْتُمْ بِهِنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ وَحَلَائِلُ أَبْنَائِكُمُ الَّذِينَ مِنْ أَصْلَابِكُمْ وَأَنْ تَجْمَعُوا بَيْنَ الْأُخْتَيْنِ إِلَّا مَا قَدْ سَلَفَ ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ غَفُورًا رَحِيمًا ٣٢۝

An haramta muku uwãyenku, da ´yã´yanku, da ´yan´uwanku mãtã, da goggonninku, da innoninku, da ´yã´yan ɗan´uwa, da ´ya´yan ´yar´uwa, da uwãyenku waɗanan da suka shãyar da ku mãma, da ´yan´uwanku mãtã na shan mãma, da uwãyen mãtanku, da agõlolinku waɗanda suke cikin ɗãkunanku daga mãtanku, waɗanda kuka yi duhũli da su, kuma idan ba ku yi duhũli da sũ ba, to, bãbu laifi a kanku, da mãtan ´yã´yanku waɗanda, suke daga tsatsonku, kuma kada ku haɗa tsakanin ´yan´uwa biyu mãtã, fãce abin da ya shige. Lalle ne, Allah Yã kasance Mai gãfara ne Mai jin ƙai. (sūratun Nisá'i : 23)

Mu’amalar da take kai wa ga saduwa a tsakanin mace da mace (maɗigo) kuwa babbar haram ce, kamar yadda na tsakanin namiji da namiji (luwaɗi) take zama haram ita ma.

Don haka wajibi ne a yi nesa da duk abin da zai kai musulmi ga faɗawa a cikin wannan alfashar. Kamar dai yadda ake haramta mu’amalar da ke kai wa ga hakan a tsakanin mace da namiji kafin aure, haka kuma ake haramtawa a bayan aure a tsakanin waɗanda babu ƙullin aure na Sunnah a tsakaninsu. Allaah ya kiyaye.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments