Ticker

6/recent/ticker-posts

Bikin Takutaha a Kano

Bikin Takutaha A Kano ya cika Shekaru 700 biki ne na murnar yin nasarar rushe tsunburbura da yai dai dai da ranar Sunan manzon Allah Sallallahu Alaihiwasallam

Ana gudanar da bikin murna da zagayowar ranar sunan Annabi Muhammadu a birnin Kano da a kafi sani da Taku-taha karo na kusan ɗari bakwai.

ASALIN BIKIN TAKUTAHA A KANO

TUN DAGA ZAMANIN SARKIN KANO ALI YAJI DAN TSAMIYA.

A duk 19 ga watan Rabiul Awwal, a jihar Kano kanawa suna gudanar da wani bikin Wanda ake Kira Takutaha.

Shin menene Asalin Tarihin sa ?

Menene Alakar Bikin da Addinin musulunci ?

A wata shekara  zamanin sarkin Kano  Yaji  dan  Tsamiya,  wasu malaman Wangarawa  karkashin  jagorancin sheikh AbdurRahman Zaiti  suka zo,  Kano,  baya ga musulunci da kuma kasuwanci,  suna da dabarun  yaki da baa  san  da su  ba a Kano.   Bagaudawa suka karbi  musulunci, hannun su, su kuma  su taimaka musu don su yaki  abokan  gabarsu.  Kwana daya  da zuwansu  Sarkin Kano Yaji ya karbi musulunci,  ya kuma canjawa kansa suna zuwa Ali.  Wanda hakan ke nuna, cewa , shirin yaki zaayi,  domin ana cewa Ali bin  Abu Talib shine sarkin yakin  manzon  Allah (saw). Kafin Ali yaji ya musulunta akwai musulmai a Kano saidai basu kai ga kafa mulki ba

A farkon watan Rabiul  Awwal  na wannan shekara,  ne Yaji  ya tara dukkan  maguzawa,  ya kuma karanta  musu  dokar-ta-baci.  Inda yace musu

"Ku sani,  daga yau, komai tsakanina  daku,  sai yaki  da tsinin  mashi,  ba yaudara,  bawani  boye boye,  domin  ba mayaudari  sai  matsoraci,  ku  shirya  gani nan zuwa gareku ko ku karɓi Addinin Musulunci  kafin lokacin anyi masu wa'azi suka butulce"

Mataki  biyu  suka dauka,  na farko sunyi  kokarin  bada  cin  hanci  ga Sarki  Yaji,  amma yaki  karba,  yace  a maida  musu baya so.  Na biyu,  sai suka koma ga Tsumburbura,  domin neman nasara,  amma ta gaya musu,  cewa wannan yaki ba nasara,  domin lokacin  karshen  addininsu  a kasar Kano yazo.

Acikin  watan  dai,  rundunar  musulmi  suka fuskanci,  rundunar  maguzawa,  a gefen  Dutsen Dala,  inda suka hadu,  aka gwabza.  A wannan lokacin ne,  Jarmai  Bajere  ya samu  nasarar  Kutsa  kai cikin  shigifar  Tsumburbura,  inda ya samu  wani  halitta  na tsaye,  rike  da maciji  a hannunsa,  ya daga mashi  ya bugawa  halittar  nan,  tayi  kuwwa ta fito  a guje.  Nan da nan suka bita,  inda ta nufi  kofar  ruwa,  ta fada cikin ruwan  Dankwai.  Wannan Shi ya kawo karshen  Tsumburbura,  da kuma addinin  maguzawa a garin Kano.

Samuwar  wannan Nasara, ba karamin abu  bane  a wurin  musulman  Kano.  Wanda aka shafe  sama da shekaru  100 ana nema.  A dalilin haka ne,  ya sanya  musulman  kanawa duk  shekara,  sukan taru  su hau Dutsen  Dala domin tunawa da wannan nasara da musulunci yayi akan Maguzanci.  Su nunawa duniya cewa, addinin Allah yau ya shafe  addinin kafirai.  Domin kafin  zuwan musulunci,  ba mai hawa Dala in ba Babban limamin addinin ba. Amma zuwan musulunci,  yanzu kowa ma sai ya hau,  ya yi kashi ma aka. Wannan shine dalilin da ya sanya ake  takutaha a duk shekara a Kano.

MENENE MA'ANAR KALMAR TAKUTAHA?

An sha kai-kawo a tsakanin masana game da ma’ana ko asalin wannan kalma ta takutaha. Wannan ce ta sa aka sami mabambantan ra’ayoyi game da wannan kalma.

Daga ciki akwai Hassan (1998:94) ya nuna cewa, bayan al’ummar Kano sun rungumi wannan rana ne ta takutaha, sai Maguzawa da suke gabatar da bukukuwansu na bauta a lokacin suka damu, wasu suka bar garin zuwa ƙauyuka, suna cewa, “wannan sallar taku-ta ba tamu ba ce”. Daga nan sai aka sami kalmar takutaha.

Wasu kuwa suna ganin Kalmar ta samu ne daga ƙaulin Shehu Usmanu Danfodiyo, a lokacin da almajiransa suka yiyo  bara a ranar da  shekarar da aka haifi Annabi salallahu alaihi wasallam ta kewayo, amma sai ya ƙi daukar komai a ciki, ya ce, “ ai wannan taku ta”. Daga nan sai aka sami kalmar “takutaha”.

Wasu kuma suna ganin ma’anar Kalmar takutaha ita ce, “Allah ya maimaita mana”, wasu kuma sun ce sunan Ma’aiki ne. Haka nan, wasu suna ganin Kalmar ta samu ne daga sunan wata baiwar Allah mai suna Taku, ‘yar Malam Usman Attuman, babban waliyin nan da ya zauna a Madabo.

A dunƙule, za a iya cewa bikin takutaha yana daya daga cikin bukukuwan addini da ake yin sa a birnin Kano, duk ranar 19 ga watan Rabi’ul awwal, wato watan da aka haifi Annabi Muhammadu salallahu alaihi wasallam kuma dai-dai da ranar sunansa.

Daga:

Zauren Hikima

www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments