Daddagen Harafin /d/ a Karshen Gaɓa

    Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

    About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

    624. In aka nunka d gaɓar ƙarshe lura,

     Ba a saka ta, zan kula malam lura,

     In ko ka sa ta babu tsari ba kara,

     An kauce wa ƙa’ida, j ta yi kara,

    Shi muka ce wa daddage don ganewa.

     

    625. Harafin d a nan wurin zai rikiɗewa,

     Ba a rubuta d biɗo baƙi don sauyawa,

     Doka ta taho da tsari na yabawa,

     Marmaza sauya d a nan ga rubutawa, 

      Ya zamo j kula da kyau ga rubutawa.

     

    626. Sa natsuwa ka dubi kalmar ga ta tsada,

     Wasu in za su sai abinka, mai da tayi sada,

     Wasu ko za ka sai abinsu sai sui maka tsada,

     In ka sai abin ƙwarai kuma mai tsada,

      Tsadajje ake faɗi gun nunkawa.

     

    627. In aka ce gudu sana’ar mafarauta,

     Har ‘yan ƙwallo ma sana’ar su gudu ta,

    Sa mini ‘yan tsalle-tsalle duk sun yi abota,

    Ita kalmar gudu idan za ka faɗin ta,

    Guje-guje za ka ce wajen nunnunkawa.

     

    628. In aka so a ce gudajje shi ke nan,

     Wato wanda yab baro Zariya ɗin nan,

     Sanadin faruwar abin nan dai wannan,

     Ya yi gudu ya zam gudajje ga waɗannan.

      Duk doka guda kake nanatawa.

     

    629. Huda za ta zamto hudajje ke nan,

     Wato aikatau ya koma suna nan,

     Doka ta yi tanadin kalmar sannan

     Wai huda ta koma hudajje kan nan,

      Ko kuma huje-huje babu musantawa.

     

    630. Don haka ƙa’ida ga doka ta rubutu,

     Tilas a cika ta don  ya zan masu karatu,

     Su ji sauƙi su gane saƙo na rubutu,

     Dole ya zam an bi wanga tsari na rubutu,

    Haka aka son ganin su can ga rubutawa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.