Dajjal: Alaƙar Bayyanarsa Da Tsadar Rayuwarmu Ta Yau

    TAMBAYA (46)

    Ko da akwai alaƙa tsakanin bayyanar Dajjal da tsadar rayuwarmu ta yau ?

    AMSA

    Tabbas da akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin bayyanar Dajjal da kuma yanayin tsadar rayuwa da muka tsinci kanmu a yau. Hakan yanada nasaba da bayyanar ƙananan alamomin tashin alƙiyama waɗanda muke ganinsu a kan idanunmu

    Daya daga cikin hanyoyin da Dajjal zai bi ya samu biliyoyin magoya baya shi ne bangaren amfani da kudi, wanda a zamaninnan a kan kudi sai mutum ya yi kisan kai saboda tsabar son zuciya. To ina kuma ga idan Dajjal ya bayyana wanda zai ba ka duk abin da kake so indai har za ka yarda shi Allah ne (Wal'iyazubillah)

    Magana ake ta tsananin son kudi saboda tsadar rayuwa wanda hakan ya zama silar salwantar imanin miliyoyin musulmai, har hakan ke kaisu ga rantar kudi a wasu bankunan waɗanda suke bayarda bashi da kudin ruwa (riba). Munsan kuwa cin riba haramunne

    A shekarun baya wani babban sirri ya fito daga babban bankin duniya (World Bank wanda ake kira da Central Bank of Central Banks) ?

    A cikin sirrin an gano yanda masu manyan madafun iko suke son su mulki duniya. Michael Snyder – Global Research, February 01, 2015

    An wallafa sirrin a 30 ga watan Satumbar shekarar, 2013. Karen Hudes, wadda ta tona musu asirin, ta kammala karatunta na Lawyer daga makarantar koyon lauya ta garin Yake dake kasar Amurka, inda ta samu aiki a bangaren Legal department na bankin duniya, ta share sama da shekaru 20 tana aiki a bankin, wanda hakan ya bata damar sanin sirrika dayawa da bankin ya boye. A karshe suka kore ta don kawai ta tona asirin cin hanci da rashawa (corruption) da wasu sukayi a cikin bankin. Sirrin da ta fitar ya girgiza ya yi matuƙar girgiza gwamnatin amurka da ma sauran al'umma baki daya. Hudes, tace: Manya manyan masu madafun iko suna son amfani da ma'aikatu da makarantu don ganin sun mallaki duniya. Manufarsu shi ne su sarrafa al'umma ta hanyar tirsasawa mutane karban bashi (debt) ta yanda a karshe za su bijiro da aƙidarsu ta yanda mutane za su karba hannu bibbiyu ta hanyar amfani da tasirin bashin da suka bayar, yanda mutum ba zai iya tona musu asirin sirrinsu ba tun da daman sune suke sarrafa manyan kafafen yada labarai na duniya

    Karen, ta ci gaba da cewa: wannan fa bawai maganace daga masu ba da labarin ƙanzon kurege ba (conspiracy theories), saidai sirrine da aka sameshi daga attorney wadda ta share sama da shekaru 20 a matsayin ma'aikaciyar babban bankin duniya. Waɗannan sune muƙaman da ta riƙe, wanda an samesune kai tsaye daga shafinta;

    Ta karanci fannin shari'a (Law) a makarantar Yale da kuma fannin tattalin arziƙi (Economics) a jami'ar Amsterdam duk a kasar Amurka. ta yi aiki a bankin shige da fice na na Amurka daga shekarar 1980 zuwa 1985. ta yi aiki a Legal Department a babban bankin duniya daga shekarar 1986 zuwa 2007. Ita ce ta kirkiro Non Governmental Organization Committee na International Law sashen Bar Association na Amurka da kuma Committee a kan Multilateralism da Accountability na International Organizations na Amurka reshen kungiyar lauyoyi na duniya (International Law Association)

    Karen Hudes ta wallafa littattafai kamar haka "The World Bank: A Case Study in Corruption" (2006), "The Debt Bomb" (2008), "The Best-Kept Secrets of the Money and Banking Industry" (2010), da kuma "The World Bank: The Untold Story" (2011)

    A yanzu haka, tana ta fallasa asirin manyan shugabannin duniya waɗanda manufarsu shi ne sunfison yanda suka dama haka kowa zai sha, kamar yanda ta yi bayanin hakan a firar da New American ta yi da ita

    Tsohuwar ma'aikaciyar tace: Wasu tsirarun kungiya ne suke sarrafa tsarin jujjayawar tattalin arziƙin kasashen duniya, cin hanci da rashawa ya yi musu katutu a zuciya. Sune suka mallaki manyan kafafen yada labarai ta yanda ba za a tona musu asiri ba. Sun koreta ne a yunƙurinta na ganin ta toshe kofar cin hanci da rashawa a babban bankin na duniya, wanda kuma har yanzu tananan a kan manufarta da taimakon wasu masu irin aƙidunta

    Hudes, ta yi sharhi a kan 2011 Swiss study da wanda PLUS ONE suka wallafa "kungiyar masu son sarrafa duniya”, tace: sunanan sunata aiki tuƙuru musamman a kan manyan bankunan kasashe (central banks) don ganin sun cimma manufarsu

    Kwanakin baya da akwai binciken da aka gudanar a Swiss Federal Institute of Technology dake jihar Zurich a kasar Switzerland. An bincika alaƙar dake tsakanin kamfanoni miliyan 37 da masu zuba hannun jari. Sai aka gano akwai wasu 147 kacal waɗanda sune sukeda kaso 40% cikin 100% na kudaden da ake zubawa a hada-hadar kasuwanci na duniya gaba daya. Shi kuma babban bankin duniya da kuma sauran bankunan kasashe ananne ake sarrafa waɗannan maƙudan kudade

    Mutane dayawa ba su ma san mene ne bankin International Settlements ba, wanda saninsa yanada matuƙar muhimmanci (Musamman a wannan zamanin, wanda duniya ta zo karshe). A kwanakin baya na yi bayani a kan yanda tsarin wannan banki ya shafi dokar kowacce gwamnati da takeda hurumi da bankin. Bankin da yake sarrafa kudaden kasashe a sirrance wanda ba kowa ba ne yasan da hakan

    Bankin yana garin Basel ne dake kasar Switzerland, kuma yanada rassa a Hong Kong da Mexico. Bankine ba irin kowanne banki ba, bankine ba irin wanda aka zaba ba haka kuma ya barranta daga dukkan haraji ko kuma dokokin kowacce kasa. Wikipedia ma sunce banki ne wanda ba ya karkashin kulawar kowacce gwamnati a duniya. International Bank of Settlements sune suka taimakawa Nazis (Kungiyar Hitler) da maƙudan kudade domin aiwatar da yaƙin duniya na biyu (World War II)

    Saidai yanzu babban bankin na duniya (IBS) ya karkata akalarsane a kan yanda zai sarrafa dukiyoyin mutane su dawo karkashinsa (Ta yanda idan Dajjal ya bayyana zai samu sauƙin samun mabiya. Wal'iyazubillah). A yanzu haka da akwai manya manyan bankuna har guda 58 waɗanda suke karkashin babban bankin duniya (IBS). Wannan dalilin ne ya sa a duk duniya babu kasar da takai Amurka karbar bashi musamman mai kunshe da kudin ruwa (interest). Ke nan kunga ita kanta ma Amurka a karkashin bankin take. (Wani zai iya tambayar wai to shin su wanene suke sarrafa wannan bankin ?. Ba kowa ba ne face Banu Isra'ela wato Yahudawa, eh Yahudawa, gashidai ba su da wani yawa amman sharri da bala'insu ya yi yawa a ban kasa, tun daga zamanin Annabi Musa A. S har zuwa wannan zamanin namu na karshen rayuwar ba ni Adam)

    Duk bayan watanni biyu, suke hada taron karawa juna sani a kan yanda za su cimma manufarsu wanda silar wannan taro da suke mutane suka matuƙar cutuwa, namiji, mace, yaro da babba amman ba wanda yake cewa komai silar hakan. (Ba haka nan aka kirkiri wannan babban banki ba, domin kuwa sun dade suna gudanardashi wanda manufarsu shi ne su kafa: "Sabuwar Dokar Duniya” (New World Order) kamar yanda hakan yake a rubuce a bayan kudin Amurka (American Dollar) babban manufarsu shi ne a cire addini a rayuwar dan Adam)

    Haka kuma Karen Hades ta fitarda article mai suna: "Su wanene suke mulkar duniya: Hujjoji ƙwarara da suke nuna masu mulkar duniya”, ta hada da abin da Professor Carrol Ƙuigley (na jami'ar Georgetown) masanin tarihi ya fada a cikin littafin da ya wallafa a shekarar 1966: "Manyan masu madafun iko suna ƙoƙarin mulkar duniya ta hanyar amfani da kudaden banki da kuma ƙaƙabawa mutane riba (interest) yayinda aka ba su rancen kudi” Wanda idan muka duba yanayin da kasashen duniya suke ciki za mu tabbatarda cewar babu shakku a cikin wannan lamarin

    Ana kiran tsarin da sunan neu-feudalism, wanda a iya kasarmu kadai za mu gasgata hakan ta hanyar duban bangaren bankunan kasarmu inda zakaga za su ba ka bashi ammanfa saidai idan ka tashi biyansu ka dora musu kudin ruwa (interest) wanda kuma sanin kanmune cewar cin kudin ruwa haramunne a addinin musulunchi. Akwai kuma bankunan da suke tsarinnan wanda idan ka ba su ajiyar kudi sai su dinga juyasu suna dora maka ladan ajiya, manufar hakan shi ne, idan mutum yafara jin dadin kudin, zai wahala ka ga bai bi tawagar Dajjal ba idan ya bayyana la'akarida idan mutum bai bi Dajjal din ba to fa shi ke nan ya rasa kudinsa. Kuma dai munsan mutum akwai son dukiya kamar yanda Allah ya fada a cikin Suratul Fajr ayata 20:

    ( وَتُحِبُّونَ الْمَالَ حُبًّا جَمًّا )

    الفجر (20) Al-Fajr

    Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa

    A yanzu haka da akwai manyan kafafan yada labarai guda 6 waɗanda suke sarrafa kaso 90% cikin 100% na labarai da rahotonnin da kuma wasanni a kasar Amurka. Wannan sune daga dalilan da ya sa suka saka tambarin ido daya na Dajjal a bayan dollar ta Amurka, tareda rubutun "Annuit Ceptus" (Yana farin ciki da tsarinmu) da kuma daya rubutun da yake daga kasan hoton triangle "Novus Ordo Seclorum" ma'ana Sabuwar Dokar Duniya

    Cin riba ya zamo ruwan dare, kuma Annabi SAW ya ce mafi ƙanƙantar illar cin riba shi ne mutum ya yi zina da mahaifiyarsa. Anata shigo mana da tsare-tsare kala-kala waɗanda sukeda alaƙa da cin riba. Idan kana amfani da Palmpay zakaga idan ka ba su ajiya (deposit) N1, 500, 000 za su juya maka kudin su ba ka N610 a matsayin kudin ruwa na kwana daya, N18, 416 a wata daya, N240, 087 a shekara guda, za su dinga ba da damar cire kudin ruwan kullum a kowacce safiya idan ka amince tsare-tsarensu. Flexi Cash suna turowa mutane saƙo ta SMS cewar za su ba ka rancen N3, 000 ba tareda kudin ruwa ba (Zero interest) dama ce ta kwana daya, ammanfa sai idan kai sabon shiga ne. Idan ka ranci N1, 000, 000 za su dinga daukan kudin ruwa (interest) N20 a kullum. Idan ka kuskura ka shiga tarkonsu to akwai yiwuwar za ka bi Dajjal la'akarida idan ya bayyana zai sarrafa waɗannan hanyoyin samun kudin ta yanda zai wahala mutum ya ƙi binsa idan ya ce ka bini, idan ka yarda ni Allah ne zan maido maka da dukiyarka. Wal'iyazubillah

    Mu duba mu ga yanda gwamnatinmu taketa ranto maƙudan kudade waɗanda ake bayarwa da kudin ruwa (interest) wanda a Labaran yammacin Asabar 23/09/2023CE - 08/03/1445AH gidan radio na Guarantee suka fitar da sanarwar: "Shugaban kasa ya sake karbo bashin dala miliyan 700 daga bankin duniya ". Idan ka maida kudin Naira zai koma Biliyan Dari Biyar da Arba'in da Shida (N546, 000, 000, 000). Magana ake ta fiyeda rabin tiriliyon daya. Matsalar a nan ita ce: iya masu madafun iko ne kadai suke amfana da kudin amman talakawa da ake fakewa cewar domin su ake rantowa su dinne kuma suke shan wahala domin kuwa manyan can dinne dai suke rarrabe kudin a tsakanin, ta hanyar siyen motocin hawa na miliyoyin kudi da kuma sauye sauyen kayan masarufinsu na yau da gobe waɗanda a iya wannan fannin kadai Allah ne kadai yasan biliyoyin dalolin da aka wawashe a kasa da tenuwa 3 ko 5 da suka gabata. Ku yi tunani sosai a kan wannan maganar tawa. Duk da dai akwai yunƙurin da gwamnatin tarayya take yi na ganin an sauƙaƙewa al'ummar radadin talaucin da ya yi kaka gida a taredasu ta hanyar sauya kudaden yanzu su koma sababbi (Old naira to New naira notes), wanda canjin zai fara aikine daga watan January na shekarar 2024. Muna fatan hakan yakawo sauƙi a kasar ta fuskar tattalin arziƙi. To ammanfa kada mu shagala domin kuwa shi Dajjal ba ruwansa da batun sabo ko tsohon kudi, burinsa kawai ka bishi ya ba ka duk abin da kake so (Aljannar duniya)

    Idan muka kuskura muka biyewa son zuciyarmu to tabbas za mu fada halaka, halakar da yahudawa suke son su ja mu ciki, mu bi wanda suka dade jiran bayyanarsa wato Dajjal. Daga cikin ikon da Allah SWT zai bashi, shi ne zai warkar da mara lafiya nan take, zai ce masa ta zubo da ruwa (wanda a yanzu hakama kasashen yamma irinsu China da Amurka sun fara wannan tsarin wanda ake kira da Cloud Seeding wato Artificial Rain, Dubai da wasu kasashen Gabas suma sun bi sawu), zai raba mutum gida biyu kuma ya umarce shi ya hade (Yanzu an dauko hanyar wannan ta amfanida laser ayiwa mutum CS batareda jini ya fito ba), zai tada na kabari a zahiri (Saidai a badini aljanine zai shiga gawar sai ya rudi mutane tun da har Aljanu ma za su bishi), Yahudawa 70, 000 za su fara binsa riƙe da baƙar tutarsu daga yankin Isfahan dake Iran. Zai kwace tattalin arziƙin mutane, bankunansu, kasuwanninsu, abincinsu da abin shan su, wanda ya bi shi ya samu duniya wanda ya bijire masa zai sha wahala saidai hakan jarabawace ga muminai wanda ba su bishi ba, makomarsu Aljannah silar haƙurinsu

     

    Kumadai munga abin da ke faruwa ga manoman Dutch dake kasar Netherlands, yan sanda sun tasosu a gaba sunata kashesu tareda kwace musu amfanin noma kamar yanda tashar talabijin ta France24 da wasu tashoshin suka wallafa. Ƙudirin gwamnatin Dutch shi ne ta naƙasa manoma 3, 000 kafin shekarar 2030 wai hujjarsu ta yi hakan yanada nasaba da yanda manoma suke zama silar gurbacewar yanayin muhalli. Manoman Dutch unyi zanga zanga (No Farmers, No Food, da kuma: Farming - Food & Climate Justice Now #DutchFarmers) amman matsalar bata kau ba sai ma abin da ya karu

    Wanda ita ma gwamnatin Saudi Arabi ta bi irin wannan sahun saidai ita ta ce za ta siyo hatsinne ta killace a rumbunta domin gudun afkuwar yanayin tsananin sanyi da za a shiga da kuma karancin abinci a shekaru masu zuwa. Amman a zahiri batun ba haka ba neba, domin kuwa munsan kasashen yamma dayawa waɗanda suke da aƙidar mallake bangaren noma kacokan su raba manoma da harkar ta yanda za su dinga sarrafa komai da kansu, kunga ke nan idan Dajjal ya bayyana zai samu sauƙi kwace abin da mutane suka dogara da shi su rayu wato abinci

    A bangaren bayyana boyayyun aƙidunsu, sunada alamu dayawa a kusan kowanne abunda ake amfani da shi a wannan zamanin, tun daga bangaren kimiyya har na fasaha. Saka satellite a sararin samaniya a matakin 22, 000 meters yanada alaƙa da lambar shaidan domin kuwa yana son multiple din 11 (Irinsu 22, 33, 44, 55, 66 da sauransu). Neil Armstrong shi ne ya fara zuwa duniyar wata a shekarar 1969, acan yaji kiran sallah saura kiris ya karbi musulunci musamman ma da ya kara jin kiran sallar a kasar Egypt amman kungiyar NASA (masu sarrafa da kuma tura mutane sararin samaniya) suka ce masa idan ya sake ya kara fitarda wannan sirrin to za su janye masa tallafi kuma za su cire sunansa daga tarihin mutum na farko da ya fara taka kan wata. Karshedai bai musulunta ba saboda rashin rabo da tsoron talauci. Kuma Malaman mu'ujizar Ƙur'ani sun yi bincike a kan Suratul Ƙamar aka gano tanada alaƙa da cewar wani mutum zai je duniyar wata a 1969, idan ka irga ayoyi tun daga Ƙamar zuwa Nas zakaga ayoyi 1, 389 ne wanda ya yi daidai da Gregorian calendar na lokacin saukar ayar. Allahu Akbar

    Akwai wata waƙa da Eminem ya yi mai suna "My Darling" inda ya fito da ma'anar 666. Ga kuma masu daukan selfie suna daga yan yatsunsu 2 ma'ana 11 (Daya a cikin daya, wanda mudai musulmai munsan Allah SWT shi ne daya kacal, amman shaidan ya yi musu wahayin fitarda yatsu biyu don nuna alamun kishiya ga Allah wato shirka) Wannan ilimi ne mai zaman kansa da ke kira da Numerology wato ilimin sanin sirrin lambobi. Kuma idan ba mu manta ba ai ya zo a sahihan hadisai cewar anyiwa Annabi SAW sihiri, inda akai amfani da ƙulli 11 aka tofe aka wulla rijiya. A karshe Allah ya saukarda Surorin kariya wato Falaƙi da Nasi (Wanda idan mun irga ayoyinsu zamuga guda 11 ne, silar hakan sai sihirin da akai masa, SAW, ya warware ma'ana kowacce aya daya ta warware ƙulli daya)

     

    Tasirin wancan tofin da akayi sau 11 ne ya sa ake kiran lambar da Devil's Number, bi ma'ana Lambar Shaidan. Haka kuma suna son lambata 13 saboda ita ma odd number ce, bata raba kanta da kanta, ganye (leaf) guda 13 ne a kafar dama ta angulun dake bayan American dollar haka kuma masu (arrows) guda 13 ne a kafar hagun, kuma taurari (stars) 13 ne a saman angulun, saboda tanada alaƙa da Original 13 British Colonies (Manyan jihohin amurka da ake tunƙaho dasu guda 13 waɗanda birtaniya ta yi colonizing; 1) New York, 2) Pennsylvania, 3) Virginia, 4) North Carolina, 5) South Carolina, 6) Georgia, 7) New Hampshire, 8) Massachusetts, 9) Rhode Island, 10) Connecticut, 11) New Jersey, 12, Delawale, 13) Maryland) saboda suna da alaƙa da Mithrah da Deciples dinsa su 13, wannan dalilin ya sa a benayen Amurka babu hawa na 13 saidai na 12 na samansa kuma sai su rubuta 14. Ido 1 da yake a saman pyramid na dolar Amurka ba su sauko da shi ba saboda har yanzu babban Dajjal din bai bayyana ba, gwamnatin ta amince da fitarda wannan tambari na Pyrmid ne a shekarar 1782, a shekarar 1776 aka ƙirƙiro wannan aƙida da gudunmawar Christopher Columbus wanda ya yi descovering USA kamar yanda suka rubuta da Roman number (MDCCLXXVI)

    Peter wanda ya fito a matsayin jarumin film din Spiderman na Marvel company, ya kasance a film din wanda gizo-gizo ya cijeshi silar hakan shi ma ya dabi'antu da yin yana yana jefawa yana tashi sama, illar film din ita ce: Spiderman din yana amfanida yan yatsu 2 ne, manuniya da kuma dan ƙurya (yatsan karshe) wanda hakan ke nuna lamba 11, wato lambar shaidan. Ya gwada sakin babban yatsa da sauran yatsunsa a kan yanar ta fito amman bata fito ba har saida ya saki yan yatsu 2 a lokaci guda sannan yanar ta fito. Shaidanci da shirka ta bayyana. Munsan cewar Allah SWT ya ce gida mafi rauni shi ne gidan gizo-gizo:

    ( مَثَلُ الَّذِينَ اتَّخَذُوا مِن دُونِ اللَّهِ أَوْلِيَاءَ كَمَثَلِ الْعَنكَبُوتِ اتَّخَذَتْ بَيْتًا ۖ وَإِنَّ أَوْهَنَ الْبُيُوتِ لَبَيْتُ الْعَنكَبُوتِ ۖ لَوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ )

    العنكبوت (41) Al-Ankaboot

    Misãlin waɗanda suka riƙi waɗansu masõya waɗanda bã Allah ba, kamar misãlin gizõgizo ne wanda ya riƙi wani ɗan gida, alhãli kuwa lalle mafi raunin gidãje, shĩ ne gidan gizogizo, dã sun kasance sunã sane

    Sharrin yahudawa da Nasara ne ya sa suke fito na fito da wannan ayar, bawai gizo-gizo ba, sai suka tsara yanda za su ƙaryata waccan ayar ta hanyar wasan kwaikwayo suka fitarda mutumin gizo-gizo (Spiderman) wanda yake da dabi'ar taimakon mutane alhalin a zahiri munsan waccan ayar ta tabbatarda raunin gidan gizo-gizo la'akarida iska kadai idan ta kada za ta rusahsi. Ƙalubale ga wasu matasan zamani masu mashin din Adaidaita Sahu da suke saka hoton Spiderman a jikin mashin dinsu

    Celebrities waɗanda suke cikin ƙungiyoyin bautar shaidan (Freemasons) sun hada da Madonna, Hannah Montanah, Nicki Minaj, John Lennon, Rihanna, Ketty Perry, Lady Gaga, Aliester Crowley, Miley, Marilyn Manson ga kuma Anton Lavey wanda shi ne ministan chochin Shaidan a Amurka. Duk suna rudar mutanene da daukakarsu ta hanyar amfani da kide kide da waƙe waƙe, wannan kadai ya isa ya tabbatarwa da mutane jin kida haramunne domin kuwa idan mutum bai tuba ba akwai yiwuwar idan Dajjal ya bayyana kaima ko kuma kema ki zamo mabiyinsa. Ƙalubale ga masana'antar Kannywood. Tun da ya tabbata a cikin sahihayn cewar Dajjal zaizo har nan inda kake karanta wannan rubutun, zai zagaye duniya a cikin kwanaki 40, kwana 1 kamar shekara, kwana na 2 kamar wata, kwana na 3 kamar sati sai kuma ragowar kwanaki 37 kamar na yau da gobe, saidai Makka da Madina ne kawai ba zai iya shiga ba suma saboda zaiga Mala'iku suna gadin kofofin ta, kuma a hakan sai wasu sun fito daga waɗannan kasashe masu daraja sunbiyoshi don kawai son zuciya. Wanda kuma mata sune za su fi yawa a cikin mabiyansa saboda mata sunfi maza sakaci musamman bangaren addini kuma daman Annabi SAW ya ce sune suka fi yawa a Jahannama. Wal'iyazubillah

    Bari na tsaya iya haka saboda gudun kada in ja lokacin mai karatu da yawa duk da cewar akwai bayanai dayawa waɗanda lokaci ba zai sa na rubutasu ba. Amman inason na yi amfani da wannan damar don janyo hankalinmu a kan mu koma mu damƙe karatu da sanin ma'anar Ƙur'aninmu da sunnar ma'aiki SAW domin kuwa su kadaine tafarkin tsira. Mu yawaita karanta addu'ar da Annabi SAW ya koyar mu dinga karantawa a duk bayan kowacce sallar farillah

    An karbo daga Abu Hurairah (RA) da Nana Aisha (RA) sunce Annabi SAW yana karantarda wannan addu'ar a cikin kowacce sallarsa ta farillah (Bayan Tahiyya kafin sallama):

    ﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺍِﻧِّﻲ ﺍَﻋُﻮْﺫُ ﺑِﻚَ ﻣِﻦْ ﻋَﺬَﺍﺏِ ﺟَﻬَﻨَّﻢَ ﻭَﻣِﻦْ ﻋَﺬَﺍﺏِ ﺍﻟْﻘَﺒْﺮِ ﻭَﻣِﻦْ ﻓِﺘْﻨَﺔِ

    ﺍﻟْﻤَﺤْﻴَﺎ ﻭَﺍﻟْﻤَﻤَﺎﺕِ ﻭَﻣِﻦْ ﺷَﺮِّ ﻓِﺘْﻨَﺔِ ﺍﻟْﻤَﺴِﻴْﺢِ ﺍﻟﺪَّﺟَّﺎﻝِ

    Allaahumma inni a’oodhu bika min ‘adhaab jahannam wa min ‘adhaab al-ƙabri wa min fitnat il-mahyaa wa’l-mamaat wa min sharri fitnat al-maseeh al-dajjaal”

    Ya Allah, ka rabani da azabar jahannama, da azabar kabari, da masifar rayuwa da mutuwa, da kuma sharrin masifar Dajjal"

    (Sahih Muslim 588a)

    A hadisin Ibn Abbas (RA) kuma ya kara da cewar: Muslim Ibn Hajjaj ya ce: Tawus ya tambayi dan sa shin kayi wannan addu'ar a cikin sallarka ? ya ce: A'a. Sai ya ce masa je ka maimaita sallar gaba dayanta

    (Sahih Muslim 590)

    Muna roƙon Allah ya kiyayemu daga sharrin kawunanmu da kuma tarkon iblis. Allah ka amshi rayuwarmu muna musulmai. A daure a yada wannan rubuta domin kuwa Allah SWT kadai yasan waɗanda za su amfana dashi, kuma dan Allah kada a canja ko da harafi guda daya

    Domin neman hujjojin abin da na rubuta sai a duba:

    1) Looking into the eye of the Dajjal by Abu Muhammad Ibn Dawod, 2) The Ƙuran Dajjal and the Jasad by Imran N. Hosein, 3) Albidaya wan Nihaya by Abubakar Alhafiz Ibn Khathir, 4) Talbis iblis by Imam Ibn al-Jawzy, 5) Signs Of The Last Day by Harun Yahya, 6) The Signs of the Hour and What after Death, 7) Ƙuran and Modern Science by Dr. Bashir Sokoto 8) The Evils of Music The Devils Voice and Instrument by Ibn-al-Ƙayyim-al-Jawziyah, 9) Rational Believer YouTube Channel 10) Sense Islam YouTube Channel

    Wallahu ta'ala a'alam

    Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

    Amsawa:

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.