Ticker

Doguwar Mallaka

 Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

243. Ita dai mallaka nufi naka na kanka,

Wanda gare shi babu mai iya kore ka,

Ba a hana ka babu mai iya tauye ka,

Kuma an yadda kai kaɗai ad da abinka,

Ko wani can ya mallakai babu musawa.

 

244. In aka mallakar da komai a wuyanka,

To kai ad da shi ka san ba a hana ka,

In kuma an ka ce a damƙa maka ɗauka,

To ka mallakai, gari ba ka da tamka,

Ko aka ba waninka duk rinƙa kulawa.

 

245. Ita dai mallakar ga zan zo da irinsu,

 A misalansu dan ya zan ka gane su,

 Ga su misalce sai ka duba ka riƙe su,

Dangoginta nawa, naka, ka gane su,

Kana muna da naku, ga namu daɗawa.

 

 

246. Sa muna nasu, nata, naki, ka ƙirga su,

 In da yawa suke da shi ya zama nasu,

 In ko macce ce ta mallakai nata irin su,

 Ko kuma naki yanzu ke ce da kalar su,

  Nasa, da nashi, duk ana iya zanawa.

 

247. Dukka irinsu mallaka sun ka kasance,

 Nan zan faɗaɗa ga jimlar mu ta zance,

 Ta sungumi nawa ga idon nata makauce,

 Nawa gidan da nasa sai an yi kwatance,

  Naka gidan da nata sauƙin ganewa.

 

248. Naki da nata ga su nan dai a tsugunne,

 Nasu da namu, duk su ne zaune,

 Nashi yana ga mai ja masa kunne,

Nawa gari da naku bakin hanya ne,

  Nasu garin yana dawa sai ratsewa.

 

249. Na gano taku malama ga ta a kwance,

 Tamu a yanzu Tanko yaya ta kasance?

 In kuma tasu ta ka gan su suna ƙwace,

Nashi hali haƙiƙa sai dai a yi dace,

  Ko yatsa a baki bai taɓa cizawa.

 

250. Dokokin ga yanzu kam mun gane su,

 Don mun zo da su, had da misalinsu,

 Kalmominsu mun saka har jimlarsu,

Kalmomin na mallaka ga bayaninsu,

Biyu-biyu ne gaɓansu ba mai zarcewa.

 

251. Za ka ji gun faɗi kamar fa a ware su,

 Ga su rubuce tare nan an ka game su,

 Za ka ji gun fitar su tamkar biyu ne su,

Ga rubutun dukansu tare ake sa su,

  Ka kiyaye dukansu don ba a rabawa.

 

252. Kar ka rubuta ‘na’ gabas ‘wa’ na yamma,

 Nawa haɗe ta za ka yi na sheda ma,

 Haka nan namu, nasu, du na ƙara ma,

 Nasa, da nashi, tasu, duk na jera ma,

  Ba tazara tsakansu can ga rubutawa.

 

253. Ka kiyaye da ƙa’ida bari ruɗa ni,

Matuƙar kar raba su ka ƙwaɓe bayani,

Ka barkata mai karatu ya shiga ruɗani,

Shi ya shiga dama kai ko ka koma hauni,

Ma’anar duk da kan nufa ba ta fitowa.

 

254. A misalai da mun ka kawo sheda ni,

 Ita dai mallakar ga nan ba saɓani,

 Mun yi ta daki-daki gaba ɗai da bayani,

Daɗa na bar ka yanzu je kai ta tunani,

  Na misalan irinsu don tantancewa.

Post a Comment

0 Comments