Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
Dokokin Ɗauri
106 Ɗauri na da ƙa’ida in mun lura,
A gaɓar Hausa mai baƙi wasali tara,
Saka sauti gaban wasal ɗuko ƙara,
Duk ɗaurin da za a yi
Hausa a lura,
Kar ya wuce tsawon gaɓoɓin Hausawa.
107. Dokoki na ɗora ɗauri ba kushe,
Ɗauri na zuwa ga kalma
koyaushe,
Bai da wuri guda da ya
bar shi a yashe,
Ba a yi shamaki ba farko ko ƙarshe,
Ko farkonta, ko tsakan, ko a tuƙewa.
108. Duba za mu faɗaɗa ga misali ne,
Babba-da-jikka zanƙalelen dabba
ne,
Can ga fukafukan baƙi ne ba zane
In kun lura dukkansu
misali ne,
Farkon kowanensu ɗauri aka sawa.
109. Lura Babarbare,
barunje da mayanka,
Makarantar da
malami ke dukan ka,
Rundawa ka ba da fata ga maɗinka,
In aka duba inda ɗaurinsu ya sauka,
Ɗaurin nasu duk
tsakansu yake zo wa.
110. Wasa ag gare mu Misau[1] wai girjim.[2]
Akwai ɗauri a ƙarshenta wato dai -jim,
Na ga baƙi-ƙirin da jajir
aje tinjim,
Zan kula, -rin da -jir da ƙarshen -tinjim,
Sai ƙarshen gaɓa a nan muka ɗaurewa.
111. In mun lura yadda ɗauri ka tahowa,
Farko
ko tsakansa koko ga tuƙewa,
Furuci
ko rubuce duk zanka kulawa,
Wato
dai zubi da tsarin ɗaurewa,
Kalmomi a gun su ne aka ganewa.
112. Sharaɗi nai a sa baƙi wasali daidai,
Su kasance a jere, komi ya yi daidai,
To kuma sai su zo da ɗaurin sauti dai,
Za a saka gaban wasali ɗin dai,
Kana a sa baƙin da ɗaurin ka riƙewa.
113. Baƙi, wasali jere ai gaɓa ta cika sosai,
Kuma buɗaɗɗiya ake ce mata, to sai-
Zancen a rufe ta gum! Baƙi zai zo sosai,
Ko wasali ya zo ya ɗaure baƙi sosai,
Acca, Annaboro,
ankwa, arbawa.
114. Keken Ammani ya zube can ƙasa kancau!
Ankara, Anka, Andarai, Indo,
Ancau,
‘In’ da ‘an’ cikin Indo da Ancau,
Da misalin da yat taho
jinkar ‘kancau’!
A misalan ga duk baƙi aka ɗaurewa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.