Dokokin Da Mace Mai Takaba za ta Kiyaye

    TAMBAYA (47)

    Slm malan mijina yarasu mene ne dokokin takaba

    AMSA

    Waalaikumus, Warahmatullahi, Wabarakatuhum

    Alhamdulillah

    An karbo hadisi cewar bazawara za ta nesanci abubuwa guda 5 kuma za ta aikata abubuwa guda 5

    1) Ta tsaya a gidan da take a lokacin da mijinta ya rasu, har zuwa karshen iddarta, wanda ake kammalawa tsawon watanni 4 da kwanaki 10, sai dai idan tanada juna biyu iddarta tana karewa ne idan ta haife, kamar yanda Allah SWT ya fada:

    ( وَاللَّائِي يَئِسْنَ مِنَ الْمَحِيضِ مِن نِّسَائِكُمْ إِنِ ارْتَبْتُمْ فَعِدَّتُهُنَّ ثَلَاثَةُ أَشْهُرٍ وَاللَّائِي لَمْ يَحِضْنَ ۚ وَأُولَاتُ الْأَحْمَالِ أَجَلُهُنَّ أَن يَضَعْنَ حَمْلَهُنَّ ۚ وَمَن يَتَّقِ اللَّهَ يَجْعَل لَّهُ مِنْ أَمْرِهِ يُسْرًا )

    الطلاق (4) At-Talaaƙ

    Kuma waɗanda suka yanke ɗammãni daga haila daga mãtanku, idan kun yi shakka, to, iddarsu watã uku ce da waɗanda ba su yi haila ba. Kuma ma'abũta cikinna ajalinsu, (shi ne) cewa su haifi cikinnansu. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, (Allah) zai sanya masa wani sauƙi daga al'amarinsa

    Kada mace ta bar gidan face da wata ƙwaƙƙwarar hujja kamar: zuwa asibiti idan batada lafiya ko kuma siyan kayan abinci a kasuwa idan ta rasa wanda za ta aika. Idan kuma gidan ya rushe ne to sai ta koma wani gidan ko kuma idan batada wata (muharrama) wadda za ta tayata zaman kadaici to ya halatta tabar gidan saboda halin tsaro

    2) Kada ta saka kaya masu ado, kamar jajaye ko yellow da sauran kayan da ka iya jan hankali ga maza. Sai dai za ta saka kayane marasa kyau ko dai bakake ko koraye da sauransu. Abin lura anan shi ne kada ta saka kayan da za ta janyo hankalin wani saboda wannan umarnine na Annabi SAW

    3) Ta kiyayi saka sarƙar gold, silver, lu'u-lu'u ko mirjani da makamantansu ko dai na sarƙar wuya ne ko awarwaro ko zobe da sauransu har sai ta kammala iddarta

    4) Ta kiyayi saka turare, ta kiyayi fesawa kanta bakhoor (incense) ko kuma kowanne kalar turare har sai ta tsarkaka daga bayan al'adarta wanda a sannan ne za ta dan saka turaren bakhoor

    5) Kada ta saka kwalli ko kuma duk abinda ka iya zama kwalliya ga fuskarta wanda zai ja hankalin mutane gareta. To amman abinda ya shafi kwalliyar yau da gobe ta hanyar amfani da ruwa da sabulu wannan ba matsala. Amman kwallin da zai saka idanu su yi kyau ga mace wannan bai halatta ba

    Wadannan sune abubuwa 5 da mace mai idda za ta kula dasu sosai. Amman gameda kare karen da wasu mutane suka kirkiro cewar mai idda bazatayi magana da kowa ba a wayar salula ko kuma kada ta yi wanka sama da sau daya a sati, ko kuma kada ta dinga tafiya ba takalmi a tsakar gida, ko kuma kada ta fito cikin hasken farin wata da dai sauran camfe camfe dukkan wadannan babu su a addini

    Zata iya tafiya a tsakar gidanta ba takalmi ko da takalmi, za ta abinda take so a tsakar gidanta, ta yi girkinta ko tayiwa bakinta, ta fito cikin farin wata, za ta iya wankanta ko sau nawa ne a sati, kuma ta yi magana da kowa ta hanyar da ta dace, za ta iya gaisawa da kowacce mace da kuma muharramanta, za ta iya cire khimaar (dan kwalinta) ga iya muharramanta

    Amman kada ta yi lalle (henna) ko turare ko saka saffron, ko a kayanta ko a coffee saboda saffron shima kamar turare yake. Kada wanda ya nemi aurenta sai dai a yi mata alamu (kamar wani ya kai mata kyauta haka) amman a nemi aure kai tsaye bai halatta ba

    Allah shi ne abin neman taimako

    (Fatwar Shaikh Ibn Baaz, daga Fatawa Islamiyya, vol. 3, p. 315-316)

    Domin neman karin bayani duba al-Imdaad bi Ahkaam al-Ihdaad na Fayhaan al-Mutayri; Ahkaam al-Ihdaad na Khalid al-Muslih

    Wallahu ta'ala a'alam

    Source: Shaykh Muhammad Saalih al-Munajjid tambayata 10,670

    Amsawa:

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

    https://chat.whatsapp.com/G5NSbo2TyHMD6bcoEfds5E

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.