Duk Wadda Ya Tunkara Da Soyayya ta ce Ba Ta Sonsa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum Malam. Inada Ɗan'uwa Wanda yaka sance mai naci akan soyayya. Amma kuma duk wacce ya tunkara saita ce ba ta sonsa tanada Wanda takeso alhalin kuma tsakani da Allah shi yake sonta. Shi ne Malam nace koh akwai wata Yar bayani akan hakan koh wata addu'a da za a bamu. Na gode malam..

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus salam.. Abun da zai yi shi ne:

    1. Ya kasance mai addini da kuma dabi'u nagari; ya kyautata tsakaninsa da mahaliccinsa da kyau.

    2. Ya kasance yana da abun yi wato yana da sana'a ko aiki wanda aqallah zai iya daukar nauyin kansa da kuma ita wadda zai kawon. Kada ya zamo ɗan zaman kashe wando.

    3. Ya kasance mai tsafta daidai gwargwado. Bafa gaye nake nufi ba, a'a mai tsafta.

    4. Ya tabbatar ya tashi yin auren. Iyaye da magabatan yarinya suna dubawa su gani shin wanda keson 'yarsu shin tabbas ya tashi aure kuwa; suna duba sa'ana, aiki, muhalli etc. Wannan matsalar tana ɗaya daga cikin matsalolin da mu matasa muke fuskanta wajen neman aure kuma mune ke jefa kanmu a ciki da kanmu, za ka ga mutum yaje ya nemi 'yar mutane alhali ya san bai shiryawa auren ba, yai ta wahalhalu da ita shekaru da dama, sai kaga lokaci guda wanda ya fi shi shiryawa ko wanda ya fi shi kuɗi ya zo ya kwace masa ita sai kaga ta aje shi gefe ta kama wancan. Ko kuma kaga har yarinya ta cika sosai ta isa aure matuka har iyayen yarinyar su fara gajiya da ganinta hakan su gaya masa ya shirya alhali gashi bai shirya ba, sai kaga an watse lamari sai kuma ya fara ganin laifinsu (iyayen yarinyar). To dama tun farko an kaucewa shari'ah ai dole a samu matsala.

    5. Sai kuma ya cire ruwan ido, ya daina zuwa wajen wadanda ya san sun fi qarfinsa, ya dinga zuwa wajen daidai level ɗinsa. Eh! Kowa ya san akwai daidai da shi wajen aure. Gaskiya 'yan uwa samari wasu lokuta muke jawa kanmu raini da wulaqanci saboda wata kai da kanka kasan tafi qarfinka amma kuma sai ka ce kai ita kake so. za ka ga irin wannan auren koda iyayen yarinyar sun tilastawa yarinyar sun ba saurayin, to koda anyi auren idan yarinyar ba ta cire abin da ke ranta ba sai kaga mijin ba zai ji wani daɗin auren ba kwata-kwata wato in har ma auren ya dore bai wargaje ba ke nan.

    To in shaa Allahu idan mutum ya cika waɗannan sharuɗɗan da ke a sama kuma ya je wajen daidai da shi to lallai yarinyar za ta aminta da shi da yardar Allah. Gaskiya ba mai son ba mutum maras addini da maras abin yi 'yarsa ko qanwarsa. Sauran sharuɗɗan kuma na yarinyar ne saboda kaima na san baka son qazama, kucaka, ko wadda kake ganin ba level ɗinka ba ce.

    WATA 'YAR FADAKARWA:

    Gaskiya matasa mu tashi zuwa neman ilmi na addini dana boko gaba ɗayansu, sa'annan kuma mu tashi zuwa neman kuɗi ta hanyar sana'o'i da sauran ayuka. Ɗan'uwa ka sani a zamaninnan ba wai kai kaje ka fara gayawa yarinya kana sonta ba, ko ita da kanta ta ganka ta ji tana sonka aka fara tafiya sai daga baya ta gano cewa baka cika waɗancan sharuɗɗan ba musamman ilimi da kuma harkar yi to za ta jefar da kai. Saboda haka mu tashi zuwa neman ilimi da sana'a. Ka sani idan baka da abinyi to ka rufawa kanka asiri kada ka tunkari maganar aure da 'yar mutane sai kasan ka fara sana'a. Allah ya ba matasanmu sana'o'i da ayuka masu albarka. Ya kuma sanyawa bidarmu albarka.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.