Ticker

Fajaruddeen (Kashi na 12)

Kwata kwata kasa faɗin saƙon kawun Fa'iza yai dan shi baiga dalilin da za a ce yaro ya saki yarinya ba sai dai ya ce wa Fajarudden ɗin kar ya tafi ya jira sirikin nasa yana hanya bai kawo komai ba ya jira zatonsa ko mahaifin Fa'iza ɗin na san suyi hotuna ne.

 Ko da mahaifin Fa'iza ɗin ya ƙaraso baibi ko takan yayan nasa ba ya hau tambayar ina waliyyan ango anyi sa'a basu tafi ba ya hau masifa a asakar masa ɗiya ya kuma ƙi faɗin dalili sai da manyan mutane suka sa baki sannan ya ce.

 Sabida yaro baida asali bakuma su faɗa mana ba sun munafurcemu ran yayan mahaifiyar Fajar ya ɓaci ya ce kamar yaya yaro da ubansa ace bai da asali mahaifin Fa'iza ya ce in yana da ina dangin ubansa ina kuma uban ai bana jin mutum da ɗansa ace bazai zo aurensa ba koda kuwa akwai waliyyi da ya naɗa sannan ace arasa mutun guda daga danginsa in kuma akwai ina suke sai dai na matarsa abin ai da mamaki da na kasa yadda sai dai danai nazari na yadda dole asakar mun ɗiya.

 Yah ni abin da me ya sa kukai saurin ɗaura auren nan ba ko ɗam afrikan time ɗinnan ai ya ci kuyi.

 Wallahi ɗiyata bazata zauna da wanda ba'asan asalinsa ba balle ya gudu ya barta kowa ya san yaron nan iyayansa zuwa sukai da shi sa'annan kowa ya san wanda yake riƙe da shi baya wani nuna kulawarsa akansa shedar ba ɗansa bane shi kansa wanda ake iƙirarin shi ne mahaifin nasa baida asali ke nan shege ke riƙe da shege ina ba zai yiwuba wallahi.

 Wani dattijo ya ce anman dai kasan baka kyayta ba ai da tun sanda ya fara neman aure za ka bin cika mahaifin faiza ya ce kuskuren da nai ke nan kyawawan halinsa suka ringaye ni na kasa bin cikawa sedai da aka kawon hujjoji masu karfi na ji araina bai dace da zurriyar mu ba dan da kaina bazan ma zurriya ta tabo ba.

 Dattijon ya kuma cewa kaji ba ka ce yanada kyan hali hakan be wadatar ba ina aurene wannan ba kasuwanci ba dole asakar min ɗiya.

 Fajar ya ce duda na san akwai abin da iyayenake boyewa sedai ina da tabbacin su suka haifen sa'annan a musulunce babu inda aka ce ba'a auren mara uba dan ba shi yai lefin dan Haka wallahi bazan saki matata ba aure an ɗaura saidai mutuwa ta rabamu.

 Adam ƙanin Fajar cikin kuka ya kira mahaifinsu ya sanar masa aikuwa rai a ɓace ya ce ya cema Fajar ɗin lallai lallai ya sakar musu ɗiya aikuwa ya ce ina ai shi fa babu saki a tsarinsa dan haka babu saki tsakaninsa da Fa'iza aiko mahaifin Fa'izan ya shago masa wuya yana masifa ya sakar masa ɗiya shi kuwa ya ce ina baifa san zance ba.

 Jin abin da Adam ya faɗa masa yasashi daurewa ya tawo jami'an dan bai da nisa da inda yake abin da baiyi zato ba wato zuwa gurin ɗaurin auren Fajar kai tsaye inda Fajar ke tsaye mahaifin Fa'iza riƙe da wuyansa yai hannu ya sanya ya cire hannun Mahaifin Fa'iza gami da gyarawa rajar rigarsa.

 Kallon Fajar ɗin yai ya ce Deeni fikin nutsuwa Fajar ya dubeshi in har ka yadda nine mahaifinka inaso ka saki yarin yar mutumin nan Fajar ya ce anman Abba karka ce komi inaso inma baka yadda ni na haifekaba inaso ka dubi darajar riƙe ka danai ka saketa dan Allah karka sake mintuna da auren ta akanka dan Allah ka saketa yai saurin riƙe hannun mahaifinsa Abba baka buƙatar roƙona.

 Wayarsa ya ɗauka ya turawa Fa'iza saƙo kamar haka.

Assalamualaikum

Abubuwa sun faru a dedai wannan lokaci ba wannan saƙon naso turo miki ba adai dai wannan lokacin naso ace turo miki nan ina tayaki farin cikin gami da murnar zamtowa matar Fajarudden kamar yadda mukai ta mafarki saidai abubuwan da suka faru yanzu suka sauya wannan saƙo zuwa ga waninsa ba haka naso ba sai dai haka ƙaddara ta zaɓar mana

 Fa'iza ki yi haƙuri aurenmu baida tsawon rai na yanke shi a yanzu kamar yadda aka ƙullashi baki da iddata ina miki fatan Alheri Allah ya baki miji nagari.

Tsohon mijinki mai sanki

FAJARUDDEEN

Ya dubi Abban Fa'iza karka damu na tura mata saki babu auren ɗiyarka akaina duka igiyoyin na yanke ya riƙe hannun mahaifinsa sukai waje inda sauran ‘yan uwansa suka mara masu baya.

 Suka bar sauran jama'a na cece kuce inda wasu ke faɗin tabbas mutumin da ya zo shi ne mahaifin Fajar ɗin dan kamarsu ta isa in banda shekaru ma zakayi tsanmanin yan biyu ne sedai da yawa sunfi ga eh mahaifinsa ne anman wataƙil ba aure ya haifeshi ko kuma shi ne mahaifin baida asali kowa dai da abin da yake faɗe.

 Fa'iza ce zaune ita da ƙawayenta sun kewaye ta suna faman tsokanar ta suna jiran shigiwar saƙon angon nata dan mata albishir ɗin an ɗaura.

 Jin shigiwar saƙo wayar ya sa sukai gun wayar inda Fatima ƙanwar Fajar tai sauri ta ɗauka dan ita tun da aka fara bikin tana ga gayyar amarya dan ba ta da aminiyar da ta wuce amar yar yayan ta.

 Azuci take karantawa ganin saƙon da ɗan tsawo sukai kanta dalla malama ki karanta mata ta ji aikinsan bake ya turowa ba kasa karantawa tai inda ta ji jikinta duk yai sanyi ta miƙawa ummi wayar gami sa zarar hijabinta ta bar gidan.

 Suka bita da kallo kamin su mai da hankalinsu kan wayar ummi ta hau karantawa jin abin da take karantawa ya sanya Fa'iza tai zaton kunnuwanta ba dedai suka jiyo mata ba tai saurin fizge wayar ta hau karantawa sai ganinta sukai luuuuu tai ƙasa inda wasunsu suka kurma ihuuu wasu kuma sukai kanta....

Shi kuwa mahaifin Fajar suna barin gurin ya kwace hannunsa daga na Fajar yai waje Fajar ya bi bayansa yana faɗin ka tsaya mu tafi tare yai masa banza yai gaba.

 Koda Fajar yabar makarantar kasa tafiya yai sabida tsaɓar ɓacin rai gefen titi ya parker motar inda ƙaninsa ya ce yah ko za ka fito in jamu batare da musu ba ya fito inda Adam ya amshi jan motar.

 Shi kuwa mahaifin Fajar yana fita ya tsaida adai daita sahu yai gida.

 Kamar yadda gidan biki yake haka ya tadda gidan nasa mata nata sha'aninsu anata girge girken tarar yan daurin aure ya shigo duk sunyi mamakin ganinsa ko duk sunyi mamakin ganinsa ko kaɗan bai kama da wanda aka ɗaura auren yaronsa ba.

 Salima salima yahau kira tai saurin fitowa tabi bayansa ganin yai ɗakin su Adam tana shiga ta ce lafiya dai malam ka dawo yanzu kaida mukai bazaka dawo ba sai dare ya raba yai shiru yana juya abin da yakesan faɗa mata kafin ya ce Adamu ya kirani ɗazun yake faɗan iyayan yarinyar nan da Deeni zai aura sun takura sai ya saketa.

 Ta waro ido wane irin saki nima abin da nagani ke nan hakan ya sa naje gun ɗaurin auren saidai abin da nagani na yanda mahaifin nata kewa Denin da tijarar da yake ya tunzurani ya sa dole nasa Deenin ya saketa Malam saki fa ka ce eh haka ubanta ya nema.

 Anman komaine ba ta cancanci saki ba ranar ɗaurim aurenta hakane Salima ai na sani arayuwata kullin nine mai lefi ba haka bane malam ba haka nake nufi ba koma me kike nufi na ji ya miƙe zai fice sai dai juwar data ɗebeshi yasashi faɗuwa ƙasa yup tai kansa tana kuka inda yai dedai da shigiwar su Fajar suka kwasheshi hankali tashe sukai asibiti.

Suka bar sauran ‘yan biki da tunanin kome ya faru.

 Su Fajar basu jima da fita ba kawun Fajar ya shigo wato yayan mahaifiyar su cikin fushi yake kwalawa mahaifin su Fajar ɗin kira danshi ya gaji dole mahmud ya mance da komai ya sauya shawara ai ba lefin yaransa bane sai dai nan yasamu mummunan labarin faɗuwar sirikin nasa.

 Matarsa ta tambayeshi me ya faru nan ya faɗa musu komi hankalimsu ya tashi shi kuma ya fice zuwa asibitin duda kuwa bai san wanne bane sai ahanya yake tambayar Adam a waya ya faɗa masa.

 Kawun na fita suka hau cece kuce inda da yawa suke cewa banda abin Mahmud ai ba yaransa sukai masa lefi ba bacin haka tsahon shekarun da aka shuɗe ya ci ace ya mance da komai ya rungumi kaddarar sa.

 Fatima kuwa ƙanwar Fajar data fito daga gidan su Fa'iza hankali tashe tai gida dan jin ko gaskene saƙon da ta karanta sai dai tana zuwa ƙofar gida taga yayyunta riƙe da mahaifinsu ta mara musu baya sukai asibiti cikin kuka.

 Koda kawu yaje asibiti duk sai hankalinsa ya tashi jikinsa yai sanyi ganin jikin mahmud ɗin kai bazakai zaton zakaje bakin ƙofa ka dawo ka tadda shi da rai ba duk sai ya mance da abin da ya faru ɗazun ya mai da hankali wajen ganin samuwar lafiyar sirikin nasa.

 Gidansu Amarya Fa'iza kuwa ihun ‘yan matan yaja hankalin iyaye akai ciku hankali tashe ake tambayarsu me ya faru kursum ce ta daure ta ce saki mijin nata ya turo mata har uku juwa ce ta ɗebi mahaifiyarta luuuuu ta tafi za ta faɗi akai saurin tareta.

 Ƙanwar maman Fa'izan ce ta ɗebo ruwa dan shafawa Fa'izan saidai shafawar duniya taƙi motsi ala dole aka kwasheta sai asibiti saida ta yini sir sannan ta san inda kanta yake yayim da duk hankalin iyayanta ya yashi zaton ko zasu rasa ɗiyar tasu.

 Da kuka ta farka tana faɗin dan Allah kuce masa wallahi ina sansa karya sakeni mahaifinta yai saurin zuwa ya kamo hannunta ki yi haƙuri Fa'iza sakin shi ne mafi alkairi tai saurin kwace hannunta cikin kuka tana girgiza kanta wallahi Abba bashi ne mafi alkairi ba Abba in babu malam wallahi bazan iya rayuwa ba mutuwa zan yi cikin fishi mahaifin nata ya daka mata tsawa ke Fa'iza tai saurin shiga tai taiyinta dolema ki haƙura da shi dan wallahi aure kedashi sedai bayan raina kina ji na ko ta gyada kai alamar eh ya tashi ya fice.

 Yana fita ta ɓarke da kuka dakyar aka samu tai shiru abinci kuwa kasa ci tai washe gari aka sallamesu sukai gida inda tuni yan biki suka watse.

 Agida ne mahaifinta ya kirata yake faɗa mata shi ya sa akai sakin da dalilinsa hankalinta ya tashi ta ce wallahi Abba Fajar ba shege bane kawai mahaifinsu ne ba me san shiga sabgar abubuwan su ba anman wallahi ba shege bane dan Allah Abba kayi haƙuri ni wallahi ko shi kaɗai ya girma ajuji wallahi ina san sa haka wallahi mutuwa zan yi in ba shi .

 Ke banfa san rashin ta ido ki mutu ɗin kinji ko anman wallahi indai wannan yaron ne keda aurensa sedai inna mutu inkinga mutuwar ta fiye ki mutu wani kikai wa kanki kikaiwa yai ficewarsa yabarta tana faman kuka.

 Kwanan Abban su Fajar uku a asibiti baisan inda kansa yake ba duk sun fidda rai inda hankalun matarsa wato mahaifiyar su Fajar yafi na kowa tashi dan tuna lokacin Fajar na ƙarami da ya taɓa irin wannan faɗuwar likita yai ta ja musu kunne kan zasu iya rashi lokacin ma da ƙarfim sa bare yanzu da shekaru suka ja.

 Cikin ikon Allah likitoci suka shawo kan abin inda suka samu daƙyar da taimakon Allah nimfashinsa ya dai daita.

 Hankalim iyalin nasa bai kwanta ba sai da sukaga yana iya buɗe ido duda baya musu magana saidai alamu sun nuna yana cikin hayyacinsa maganar ce dai baisan yayi.

 Shi kuwa ido kawai yake binsu da shi tausayinsu duk ya cikasho yana ɗaya daga dalilin da ya sa baya nuna musu kulawa sabida baya san in ya mutu suyi rashin wani ginshiƙi arayuwarsu sa'annan baya san su tambayeshi ina danginsa sai dai yana ganin rashin nuna kulawar bazai rage komai na soyayyar da Allah kan dasawa yaro na soyayyar iyaye ba agaresu.

 Umman Fa'iza ce zaune ta rafka tagumi abin duniya duk ya isheta tun wayewar garin yau ba ta sanya Fa'iza a idon ta ba batajin ko Sallar asuba tayi bare azahar ga mangariba na kawo kai gashi mahaifinta ya ce afita sabgarta intaga ana nuna damuwa da damuwarta saita fi ƙin warewa da wuri.

 Sai dai ance soyayyar uwa daban ce ga yaranta ganin shiru ya sa umman Fa'izan zuba abinci tai ɗakin faizar dan kai mata dan ita kam bazata bari yunwa ta illata mata ɗiya ba dame zataji da yunwa ko kuwa da rashin mijin da ta gama tsara rayuwarta ko da shariyar iyaye.

 Tana shiga ɗakin ta saki farantin abincin tai ciki da gudu mai za ta gani Fa'iza ce kwance shame shame da alama ma ta mutu gefenta kwalbar fiya fiya ce da takardar maganin ɓera da alamu su ta haɗe guri guda ta shanye ummanta ta hau girgizata cikin kuka sai dai ina ba ta ko motsi.....

Thank you for reading😍

💞 Don't forget to vote and Comment 💞😍

Fatan zaku mun afuwa na rashin posting akai akai na san sosai kuna haƙuri da ƙailula ta na gode da karantawa 😍

Fajar ne zaune kamar ko yaushe agefen gadon mahaifinsa kamar yadda suka saba tun fara jinyar sa shirune abokin hirarsu basa ce masa komai kamar yadda ko ido in ba lokacin sallah ba baya buɗewa.

 Deeni! Deeni!! Fajar ya tsinkayi muryar mahaifin nasu na kiran sunansa yai saurin matsawa kusa da shi yana faɗin Na'am Abba mahaifin nasu ya miƙo hannunsa miƙon hannunka Fajar yai saurin kamo hannun mahaifin nasa.

 Kuma mai-maitawa yayi Deeni fajar ya ce na'am Abba na san kai mai haƙuri ne tun da ka taso kake haƙiri da yanayin da ka taso ka cince mu ciki inaso ka ƙara kan wanda kake da shi na san bakaji daɗin yadda iyayan yarin yarnan suka hanaka aurenta ba sedai inaso kasani bakanka ne farko ba kamar yadda ba kanka ne ƙarshe ba.

 Ya kuma riƙo hannun mahaifin nasa da kyau wallahi Abba ni guna komai ya wuce dan Allah kaima ka daure ka mance dan Allah ka cire damuwa aranka ko kasamu sauƙi.

 Deeni da gaske kana san in samu sauƙi yai saurin gyaɗa kai eh Abba to shi ke nan kamin wannan alfarmar matsayina na mahaifinka inma baka yadda kamar da muke ta isar maka hujja na nine mahaifinka ba inaso kamin alfarma matsayin wanda ya riƙeka.

 Abba wallahi koda bama kama bazan taɓa yadda bakaine mahaifina ba baka buƙatar neman alfarma ta sedai kawai kaban umarni inyi inaso kasa amaidawa mutanen nan kayan jerensu sannan inaso dan Allah ka daure in zakai aure ka je ka nemo me taɓo arayuwarta ta yadda bame maka gori adanginta dan Allah in sonane ka je ka nemo aure gidan marayu ko wadda kasan ba ta da uba.

 Yai saurin kallon mahaifin nasa ya gyaɗa masa kai na san kajini indai ba haka kayi ba ina tabbatar maka da tabbas kuwa mutane bazasu dena kashe maka aure ba ni kuma bazan iya dena shiga damuwa ba kamar yadda bazan iya bayyana maka tambayoyin da kake ma mahaifiyarka ba.

 Fajar ya ce shi ke nan Abba insha Allahu zan yi duk abin da kake so mahaifin nasa ya ce na gode Deeni Allah ya maka albarka ya mai da idanunsa ya rufe fajar ya ce amin Abba.

 ****

Ita kuwa umman Fa'iza ganin ganin ɗiyar tata taƙi motsawa ya sa tai waje tana kuka a farfajiyar gidan taci karo da Bashir yana ƙoƙarin shigowa da hanzari hankali tashe yake faɗin mami lafiya cikin kuka take faɗin Fa'iza tana nuna cikin gida mai ya sameta yake tambaya hankali tashe ganin mamin taƙi faɗa masa yai cikin gida aguje.

 Kai tsaye ɗakin su Fa'izan ya nufa yadda ya ganta ya tada masa da hankali bai tsaya wata wata ba ya sa hannunsa a ƙirjinta zuciyarta ba ta bugawa hankalinsa ya tashi yai saurin kamo hannunta dan duba pulse kaɗan kaɗan yake jin bugun da alama da ranta yai saurin kamo gefen rigarsa ya goge mata sauran maganin dake bakinta.

 Seda ya ba ta temakon gaggawa yai ɗauketa mami ta mara masa baya sukai asibiti ko gidan ba ta rufe ba.

 Asibitin malam suka kaita har aka shigar da ita ɗalin duba marasa lafiya masu buƙata ta gaggawa ummanta ba ta dena kuka ba danma kawai Bashir ya nace ba ta mutu ba anman itakam tasan ta mutu.

 Likitan ya jima a ciki kafin ya fito yana cire safar hannu ta asibiti ya dubi Bashir biyoni office yabishi shida mamin Fa'iza ɗin.

 Munyi sa'ar ceto ranta sakamakon ba wani me yawa sosai tasha ba sannan kun ba ta temakon gaggawa agida tasamu temporary heart failure ne hakan ya sa nunfashinta yake ɗan samun matsala sabida maganin ɓera data sha Alhamdulillah yanzu komai yazama normal muna saka ran zuwa gobe ta farka mami ta hau godiya.

 Shikuwa Abban su Fa'iza koda ya dawo ya tadda gida a buɗe ya shiga ba kowa yahau masifa wato dan wulaƙanci salon azo amasu sata shi ne zasu fice subar mai gida na kowa.

 Wayar umman Fa'izan yahau kira sedai ga mamakinsa wayar na gida hankalunsa ya kuma tashi.

 Koda suka fito daga office ɗin Bashir ya ce bari ya kira Abban su Fa'izan ya faɗa masa mami ta ce to.

 Koda ya kirashi suka gaisa ya ce Abba daman mami ta ce in faɗa maka Fa'iza ba ta da lafiya muna asibiti yai tsaki banace karta shiga sabgar yarinyar nan ba wato ban isa aji maganata ba ko to maza kaɗauko su sudawo ta mutu.

 Bashir yai saurin cewa dan ganin Abban zai kashe Abba guba Fa'izan tasha bama tasan inda kanta yake ba innalillahi Abba yahau kira murya na rawa yake tambayar ko suna wane asibiti ne nan Bashir ya faɗa masa ko wayar bai kashe ba bare ya rufe gidan yai waje.

 Kotakan motarsa baibi yai bakin titi dan baijin zai iya jan mota ayadda yake jin ransa hankalinsa yai ƙololuwar tashi wato mutuwar da take cewa zatayi yana cewa ta mutum ita da gaske take shikam indai za ta farfaɗo zai faɗa mata shi dan ta cire wannan yaron aranta ne yake faɗin haka yana kumayin haka ne dan farin cikinta.

 Ko a asibiti yadda yaganta kwance kamar gawa ya kuma tada masa da hankali.

***

Shi kuwa Fajar koda Adamu ƙaninsa ya zo ya shirya yai gida seda yai wanka sannan ya faɗawa ummansa cewar Abba ya ce amaidawa su Fa'iza kayan jerensu umman ta ce nima nai tunanin haka da naso a aika musu suzo anman tun da ya nuna a mai da musu ka samo mota ya ce to umma ya fice.

 Komai nasu aka sanya a mota kalifa ƙanin fajar ya musu jagora.

A farfajiyar gidan aka ajiye kayan seda aka gama shigar dasu sannan kalifa yahau sallama dan faɗa musu an ajiye kayan shirun da yaji yasashi fitowa da ƙanwar Fa'iza ɗin ya ci karo ta taso daga islamiyya ya ce yawwa kadija sakamakon duk ya sansu in kin shiga kice ka ummanku ga saƙo nan inji ummanmu ta ce to yah kalifa tai ciki shikuma yai gida.

 Thanks for reading 😍

Rubutawa

Faɗima Fayau

Fajaruddeen

Post a Comment

0 Comments