Ta Ɓangaren Farida kuwa tun randa malam Fajar ya faɗa mata game da auransa Farin ciki ya barta sai dai sosai take basar da muradin zuciyarta take walwala dan ko Ma'u bataga wani sauyi na cewar tana cikin damuwa ba.
Duk wani abu da zai ɗebe mata kewa shi take yi sai dai fa da ta
zauna ita ɗaya tuni ɓacin rai ke rufeta duda
Farida ta rage damuwa sai dai kullun damuwar mahaifinta cikin ƙaruwa
take duda yanzu yaɗan
samu kwanciyar hankali na ganin tana walwala.
Ya rasa meke damunta duk binciken da zai yi
yai ya tambaye ta sedai ta buba ba komai hakan ke ƙara tsoratashi yake kuma
zargin kansa na zaton abin da yaike ya shafi ɗiyar
tasa har take fama da ƙuncin zuciya na haka kawai.
****
Ita kuwa
Fatiha ganin kwana uku da bikin Malam bai zo makaranta ba duk sai tausayin
kanta ya cika ta na amincewa da za ta jirashi na yadda cewar yana san ta kwata
kwata ko sati baiba da aure har ya mance da ita in har da gaske yake yana san
ta koda baizo makaranta ba ai ko kiranta ne awaya in ma tsoron matarsa take ai
yana fita salla da sai ya kirata yaji ya take.
Hawaye ne ya wanke mata fuska tai saurin goge
su gami da kallon wayarta ji take kamar ta kirashi sedai ba ta da tabbas ko
baya gida karta kira ta haɗashi
da matar sa duda tana jin koda tasan baya gida bazata iya tsaga ballenta ba har
ta kirashi.
***
Umman Fa'iza
ce tafe zuwa wani shago data hanga nesa dasu dan siyo musu abin da zasuci dan
mahaifin Fa'izar ya ce basai an faɗawa
kowa abin da Faizar taiba hakan ya sa da isha'i ya ce Bashir ya tafi gida kar
suji shiru sannan ya gargaɗeshi
da kar ya faɗa ma koda
ummansa ne dan baya san in Faizan ta tashi surutun tai yinƙuren
kashe kanta ya dameta har ya kuma ƙara mata wata damuwar.
Wajen tara mamin su Fa'izan ta ce da
mahaifinsu Fa'iza ɗin
Alhaji ko za ta tafi gida tun da jikin nata da sauƙi mun bar yara a gida ga
dare bana jinma gidan a buɗe
yake na san bazai wuce su shiga maƙota ba hankalinsu bazai kwanta ba.
Sai alokacin ya tuna da yaran shi ma
hankalinsa ya tashi gasu duk mata biyu ne kawai maza suma ƙanana
anman mai zai hana ni in zauna ke ki tafi kodan kiyo mana karin safe ya buƙata
a'a Alhaji kai ka je ɗin
sabida kasan za ta iya farkawa inta ganka hankalinta zai tashi dan zatai
tunanin ko za ta mata wani abu sabida zuciyar tata duda likitan ya ce temporary
ne.
Yai shiru kafin ya ce haka ne bari inje ɗin yawwa inyaso sai zainab
ta girka abincin na san ma yanzu indai gidan a buɗe
yake ta musu girkin dare ya shafa kan Fa'izar da take kwance bisa gadon masu
jinya kafin ya wuce gida.
***
Deeni umma ta kira fajar da take gyarawa
mahaifinsa kwanciya ya ce na'am umma daman game da aikin ka ne tumda yaji sauƙi ya
kamata ka koma kasan da Allah muka dogara sa'annan da albashinka karkayi lefi
na rashin zuwa ka samu matsala in yaso sai Adamu ko ummaru su dunga zama
lokacin aikin kai ka dinga zuwa da daddare daman da yau nai niyar zuwa in bada
bayani a'a kayi yadda nace ɗin
to umma insha Allahu.
****
Umman Fa'iza
ce zaune gefen gadon da Faizar ke kwance hankalinta duk atashe haka ma bashir
dan tun safe ya zo duda likita ya tabbatar musu da komai lafiya bacci kawai
take saidai su hankalinsu yaƙi kwanciya ganin har azahar ba ta farka
ba ido kawai suka zuba mata dan ko abinci duk sun kasa ci.
Da kuka ta farka tahau ƙoƙarin cire ƙarin
ruwan dake hannunta tana kuka ummanta da Bashir sukai gunta tana ganin mamin ta
kuma fashewa da kuka mami dan Allah karkuce min ban mutu ba dan Allah suka hau
rarrashinta baki mutu ba Fa'iza .
Rushewa da kuka ta kuma yi tana faɗin me ya sa kuka hanani
mutuwa me ya sa kuka ceci raina bacin kun rabani da mesona sudai sukaita
rarrashinta dagyar suka samu tai shiru.
Yinin ranar yinsa Fa'iza tai tana kuka inda
basa gajiya wajen rarrashinta ciki kuwa harda Abbanta dan yagane faɗansa ɓata komai yake.
Ganin taƙi cin komai ne ummanta ta fito dan siyo
mata maltina da madara ko zasu samu ta sha.
A gefen shagon ta tsinkayi muryar matashiyar
budurwa na faɗin lah
mami ina wuni kamar tasan muryar ta juya Fatima ƙanwar Fajar tagani suka gaisa Fati me
kike anan wallahi Abbanmu aka kwantar tun randa abin ya faru ya faɗi ayya a ina ne Fatima ta
nuno mata da hannu au bama nisa muje in duba shi.
Abakin ƙorar ɗakin
suka tadda ummansu Fatiman a zaune kan tabarma tana lazimi ba yabo ba fallasa
suka gaisa da umman faizan nan ta mata ya me jiki ta ce da sauƙi inda
shiru ya ratsa kamin mamin ta ce bari in shiga in dubashi sai in wuce.
A'a inji umman Fajar basai kin shiga ba
ganinki zai iya tada masa da ciwon munsamu yaji sauƙi hakanma ya isa Allah ya
bada lada.
Murmushi mamin
Fa'izan tai kamin ta ce haka ne daman Fa'iza ce baji daɗi ba Ayya Allah ba ta lafiya umman Fajar ta faɗa da alamun ƙosawa
ba tare da ta tambayi me ya samu Fa'izan ba guba tasha mamin ta faɗa ba tare da damuwa da ƙosawar
umman Fajar ɗinba.
Innalillahi
wa'inna ilahi raji'un umman fajar ta faɗa
hankali tashe nazone dam Allah in roƙi alfarma Fajar ya zo yama yarimyar nan
nasiha sabida tana jin zancensa gashi kuma Deenin baya nan Fatima bita kiga ɗakin in ya zo seki rakashi.
Sun miƙe zasu tafi Fajar ya ƙaraso
gun Fatima ta ce lah umma ga yayan nan ba haka taso ba ko kaɗan bataso yaje ba sai dai
ba yadda ta iya ta ce yawwa Deeni ka je wai Fa'iza ce tasha guba innalillahi
wa'inna ilahi raji'un ya faɗa
kamin ya ce Allah ya ba ta lafiya anman ai ina ganin basai naje ba.
Mami tai sauri
cewa a'a dan Allah kazo muje ɗin
ceton rai zakai zai magana ummansa ta ce kuje ɗin
karku zauna rai ɓace
yabi bayan mamin Fa'izan da ƙanwarsa da sukai gaba.
Thank you for
reading 😍
Kai tsaye Inda
aka kwantar da Fa'izan sukai ransa duk a ɓace
dan gaskiya yadda ya tsara babu ganin Fa'izan a yan kwanakin nan sedai ya zai
yi umarnin ummansa ne dole yaje.
Da mahaifinta suka fara cin karo ran Fajar ya
kuma ɓaci ya haɗe rai ji yake kamar yaje ya
rufe shi da duka sabida duk sabida shi ne mahsifinsa ya faɗi ganin Fatima na gaidashi
yasashi daurewa shi ma ya ce Barka da yanma ya me jiki shi ma mahaifin Fa'iza ɗin rai ɓace ya amsa.
Umman Fa'iza ce ta ce da Bashir ya shigar da
su ɗakin ita kuma tai
gun mijin nata dan fahintar da shi me yakawo Fajar ɗin.
Suna shiga ɗakin
Fa'iza tai zunbur ta miƙe tana kuka yai saurin ƙarasawa inda take yana faɗi yi zamanki ai zan ƙaraso
yah dan Allah ka faɗan
zuwa kai ka ce baka saken ba dan Allah ka ce mun mafarki nake.
Ya girgiza kai Fa'iza ba mafarki gaskene anɗaura mana aure sedai baida
tsawon rai bawai hakan dan lefin ki bane sedan haka ƙaddarar mu take ta kuma
fashewa da kuka.
Ya kamo hannunta ki yi haƙuri
Fa'iza na sani ke mutunce me tunani gami da illimi hasalima hakan ya sa na ji
kin dace da zamowa matata Fa'iza ki daure karki ban kunya dan Allah karki sa
inyi zaton tarbiyya da illimin da na baku ya tafi a kawai na san kina cikin ɗalibaina da suka fi kowa
sanin wanda ya kashe kansa ɗan
wuta ne ko ta gyaɗa
kai
Ya kuma cewa to me ya sa zakisha guba tai
shiru haba Fa'iza ina illimin naki haba Faiza ko so kike inyi zaton baki yadda
da ƙaddara
ba tai saurin girgiza kai to me ya sa zaki sha guba kan wani can da in anje
lahira bazai iya miki komi ba tai saurin kallonsa eh kinsan dai ni a cikin
duniya ma ba kowan kowa bane bare alahira me ya sa zakisha guba sabida ni ko an
faɗa miki ni kaɗai ne namiji ta girgiza kai
alamar a'a.
Kamin ta ce bakai kaɗai bane namiji saidai ni kai kaɗai zuciya ta takeso yai
murmushin takaici kamin ya ce se kuma aka ce miki bazata kuma san wani ba meye
anfanin shekara goma sha da kikai kina zuwa islamiyya inhar baza ki ɗauki ƙaddara
ba ki kuma dage da anfani da illimin naki wajen neman sauƙi ta
hanyar yawaita salloli da karanta alƙur'ani da zikiri ki kaiwa Allah kukanki
ki roƙeshi
ya baki mafiyi na duniya da lahira.
Ita rayuwa Fa'iza ba ta taɓa zuwa yadda muka tsara ta
saidai za mu iya yin farin cikin ciki ayadda ta zo mana indai muka zamto masu
tawakkali asannu ma se muga ashema yadda ta zo manan tafi yadda muka tsara daɗi indai muna addu'a da haƙuri.
Kinsan wani ta girgiza kai ya ce babu ta yadda
daman zai zama farim ciki kawai ke cikin rayuwar mu dole akwai matsaltsalu da
duhuwa lokaci lokaci sedai in aka daure komai lokaci ne sannu komai zai wuce
musanman inmuka saka aranmu ita rayuwa gabakin ɗayanta
ta kunshi sabon shafi kinga ke nan da ka shiga wani sabon shafin shafin baya fa
ya zama tarihi ko da antuna baƙin cikin bazai zama kamar lokacin da kake
tsaliyar shafin ba inma kaima shafin nisa sedai ka dinga tuna lokacin baya ashe
kuskure nai da na damu kan wancan abin.
Nasiha sosai ya mata seda ya fuskanci zuciyar
tai sanyi sannan ya mata faɗan
karta kuma ƙoƙarin
kashe kanta dik runtsi ta ji daɗi
kamin ya miƙe
ni zan wuce ki daure ki dinga cin abinci badan ranki yana so ba sedan jikin ma
za a tambaye ki yadda kika tafi da shi ran gobe ki kuma dinga Addu'a Allah ya
yafe miki ya kuma baki miji na gari nima ki dimgamin Allah yaban mata ta gari
kinji karki cireni matsayina na malaminku sedai ki mance cewar mun taɓa soyayya ta masa godiya
ranta ya mata daɗi
yanzu dan tana jin aranta kamar za ta iya rayuwa yanzu.
Ada Bashir yana jin haushin Malamin su Fa'iza
dan tun tana yarinya in ya zo yakan kaita makarantar ko kaɗan jininsa bai haɗu da malamin ba yadda yake
masa kallo shi ne mutun ne me ji dakai har mamaki yake yadda lokacin Fa'izan na
ƙarama
magana kaɗan ai malam
Deeni yayi abu kaza ya ce kaza se yau ya fahinci me ya sa yaran kesan malamin
nasu wato shi zuciyar sa me kyau ce sosai yaji daɗin
nasihar da yama Fa'izan musanman da ya dawo daga rakasu yaga tana cin abinci
wato ta ji nasihar malamin nata.
Kwanan Fa'iza huɗu
a asibiti aka sallameta duk ta saki ranta duda har lokacin zuciyarta bats mata
daɗi sedai ta yadda da
cewar malam inta basar lokaci ne za ta nemi damuwa ta rasa.
Kullin Bashir yana gidansu duk wani abu da zai
rage mata damuwa shi yake mata mahaifinta ma yaji daɗin sauyawar datai yakuma ji daɗin bayanin da bashir ya
masa na Nasihar da fajar ɗin
ya mata tabbas shi kam dabadan rashin asali ba babu abin da zai hanashi bawa
Deeni ɗiyar tasa.
****
Tsaf
Fajarudden ya kintsa dan yau lecture ɗin
safe yake da ita bakuma ya san ya makara hakan ya sa bakwai ma yabar gida dan
yana da nisa da new campus.
Yana fitowa wajen goma ya duba time table ɗin su Fatiha dan yana da
ita tun randa aka dawo ya karbo dan ya san lokacin da ba ta da aji ilai kuwa ba
ta da aji hakan ya sa ko office baije ba yai gun motarsa nan yajata sai agric.
Ta baya ya shiga sedai bai hangeta ba hakan ya
sa ya ƙarasa
gurin mamaki sosai yai na rashin ganinta zama yai gami da ciro wayarsa yahau
kiranta seda ya kirata sau uku kamin ana huɗun
ta ɗaga.
Murya adaƙile tai masa sallama kamin ya amsa ya ce
kina inane nazo gurin mu bakyanan ta turo baki kamar yana gurin naje wani guri
ne ok kimaza kizo pls ina jiranki za muyi magana tana da mahimmanci bai jira
amsarta ba ya kashe wayar ranta ya kuma ɓaci
mutumin nanfa ya rainan hankali yayi aurensa ya mance dani sannan yanzu koma
yaji ina inane sedai kawai yaban umarni wai in wani zo.....
Nasa dariya nace taɓ Fatiha kina da aiki wato kishi ke damunki kan
mutumin da koma soyayya baku fara ba.
Farida ce
zaune riƙe
da hannun mahaifinta tana faɗin
pls Dad kabarni inje ya ɗan
kalle ta haba Jariri na kin mance kuna da makaranta ne ki bari Semester ta zo
tsakiya se ki je a break ɗin
da kuke tafi pls Dad I really want to go nayi missing ɗin makurɗi
dasu Hajiya pls.
Naga kun kusa tafiya pls Dad kwana uku kawai
kaga bama lectures ran friday da asabar ran alhamis kuma malami ɗaya ne kawai damu shi kuma
yayi aure yana hutu seda gabanta ya faɗi
lokacin da ta anbaci yayi aure ganin yadda fuskarta ta sauya ta shiga damuwa
lokaci guda ya sa Dad ɗin
nata saurin cewa shi ke nan Jaririn Dady ki shirya se wani cikin yayyenki ya
kaiki ta faɗa jikinsa
tana murna Dad's my Dad I love u yai murmushi love u more suka sa dariya baki
daɗi ya kamashi ganin
yadda take annashuwa yaji inama ace ta dawwama ahaka.
Ran laraba
tana dawowa ta shirya tsaf yayyanta suka kai mata kayan da zatai tsaraba zuwa
mota kasantuwar duk suna da abinyi ya sa Dady ya ce Driver ya kaita ita da
Faruk haushi duk ya cika ta dan baida aiki sai tsokanarta ko kaɗan basa shiri tana ɗaga musu hannu suna ɗaga mata driver yaja mota
sai makurɗi.
Suna isa ko isasshen parking driver baiba ta
fito tai ciki da gudu Hajiya babba na zaune Habiba na mata tausa ta faɗa kanta tana murna Hajiya
ta tureta keni abin da sakarci karki karyani ta turo baki kai Hajiya Alhaji ya
fito daga ɗaki yana faɗin zonan yar leleta kyaleta
in ba ta sanki ni ina sanki ta miƙe tai gunsa tana faɗin ai nima na fi sanka ya
sa dariya nima na sani.
Faruk ne ya shigo yana masifa kan shi ba bawan
ta bane take ta ɗebo
kayanta kuma driver bazai kawo mata ba tasa kuka tana faɗin Alhajina ka ganshi ko kyaleshi ni muje in ɗauko miki mantawa yai kina
da bawan ki na daban tasa murna suka fice Faruk yabita da harara.
Seda suka shigo da kayan sannan suka gaisa
sosai kakan nin nata se nan nan suke dasu musanman ma ita daɗi duk ya cika ta.
Fatahu na jin labarin Farida na Makurɗi ya shirya shi ma sai
makurɗi yadda kowa ke
nan nan da ita inka ɗauke
faruk da yake gwaleta shi ma cikin salon tsokana ya sa ta mance da wani malam
bare takaicin aurensa ji take kamar ma karta dawo garin kano tai zamanta makurɗin.
***
Ta ɓangaren Fa'iza kuwa ta
warware ta koma rayuwar ta baya farin ciki take sosai duda wani zubin takan
tuna da malam ranta kan mata ɗaci
sedai in ta kuna da nasihoyinsa sai ta ji sanyi.
Abu guda yafi damunta ayanzu shi ne in ta fito
farfajiyar su taga kayan gadon da aka siya na aurenta wanda gidansu fajar suka
dawo da shi duk se hankalinta ya tashi hakan ya sa koma zaure batasan zuwa bare
farfajiyar gidan.
Fahintar hakan ya sa maminta sanar da
mahaifinsu aikam ba shiri ya sa aka kwashe kayan sosai hakan yamata daɗi ta kuma murmurewa.
Dakansa mahaifinsu Fa'izan ya samo me aiki ya
kuma fashewa Fa'izan bayan gidan inda yake da siminta ya siyo mata irin shukoki
kalala harda ja mata fanfo bayan gidan dasu mesa na ban ruwa yayi hakan dan ya
san arayuwar Fa'iza ba abin da ke ɗebe
mata kewa sama da ta zauna taita shuke shuke.
Hakan kuwa da yayi yai mata daɗi dan kusan koyaushe kazo
gidan tana bayan gida tana faman shuka da kula da ƙananun shukokinta Bashir
ma kusan lokacin sa kaf ya kwashe ya maidashi na Fa'iza da shukokinta dan da
wuya kazo gidan bazaka tadda shi tare da ita suka kula da shukokinba hakan ya ƙara
kusanta shaƙuwarsu
duda daman can Fa'iza ba ta da wanda ta saba sama da shi shi ne yayanta aminta
kuma abokinta.
Yadda yake kula da Fa'izan yama ummanta daɗi duda can ƙasan
ranta batasan shaƙuwar dake tsakaninsu sedai ayanzu farin ciki da kwanciyar ɗiyar tata shi yafi komai ko
sa samu ta dawo hankalinta sosai ta dena tunanin mutuwa.
Rubutawa
Faɗima Fayau
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.