Fatiha ta jima tana mita aranta kamin tai tsaki ta miƙe tai inda suke zama.
Rai duk atunkushe ta gaidashi abinka da psychologist tuni ya fahinci akwai damuwa yaɗan murmusa aransa ya ce mata se abarsu ƙaramin abu su babba ne gurinsu.
Ƙanwata ya kirata ta kalle shi batare da
ta amsa ba ya ce am sorry kwana biyu banzo ba bankuma kira na ji ya kike ba
aranta ta ce ashe ya san be kyauta ba.
Banzo bane sabida mahaifina beji daɗi ba duk na rikice jiki na
rawa cikin nuna nadama take tambayar me ya sameshi tun yaushe.
Faɗuwa
yai yau kwanansa biyar kenan a asibiti muna sa ran ko yau ko gobe ma
asallameshi dik se ta ji babu daɗi
taita Allah ya sawwaƙe yana amsawa da amin.
Kinsan me ya sa ya faɗi ta girgiza kai yaɗan murmusa ya tambaya ne ba dan daman ta bada
amsa ba dan ya san ba ta da ita.
Any way abin da nazo mu tattauna kenan nan ya
ba ta labarin auren da fasawa gami da dalilin fasawa ta jinjina abin aranta
gami da afili shiru ya ratsa.
Can ya ce Fatiha zaki iya aurena ta dube shi
kawai pls kiban amsa zaki iya aurena ban ɓoye
miki komai ba game da abin da na sani akaina sedai kawai ina da tabbacin
iyayane sune suka haifen duda banda tabbacin niɗin
sun haifen lokacin da sukai aurene ko kuwa kasuyi.
Kiban amsar da take ranki karki damu wallahi
bazan zargeki ba dan kince bazaki auren ba dan na san kina da hujja me ƙarfi.
Indai har kana jin za ka iya aurena ni babu
wani aibu dazaisa in kasa auren ka ta faɗa
ya dubeta ni kuwa fatiha mezai sa ince bazan aureki ba a'a yah karkayi bincike
ka ce bazaka iya .
Bazan bin cike ba Fatiha ki faɗan da kanki wallahi kinji
na rantse miki zan yadda da kome kika faɗan
bazan taɓa tunanin kin
ɓoyen wani abu kamar
yadda na ban ɓoye miki
komai ba sedai ni bazan ce ki yadda da abin da nace miki ba ki fara bin cikawa.
Murmushi tai bana buƙatar bin cike domin ba ni
ma da wanda zai bin cika min wanda zan aura dan ba wanda ya damu da rayuwata
karka damu.
Na ji yimun bayani na miki alƙawarin
ba abin da zaisa in fasa aurenki tai shiru kamin ta fara.
Ni haifaffiyar
kaduna ce.....
Thanks for
reading 😍
Fatiha ta
cigaba.
Mahaifina sunansa Abdurrashid muktar haifaffen
kano ne komai nasa na kano ne.
Malam muktar shi ne mahaifinsa wanda ya
kasance yanada mata biyu umma salamatu da umma Barira ko waccensu tana da nata
yaran umma Barira ce uwar gida tanada yara biyar sai umma Salamatu wadda take
ita ce amarya tana da yara takwas ita ce kuma mahaifiyar mahaifina wanda shi ne
na huɗu a ɗakinsu.
Gidansu mahaifina shahararren gida ne a
unguwar su da maƙotansu koma ince a garin kano baki ɗaya daga nisan duniya in ka ce akawo ka gidan
Malam muktar sarkin mayu za a kawoka yar gidan kakana wato mahaifinsu babana.
Shi ne sarkin mayun garin nasu sana'arsa ita
ce bada magani babu lefi Allah ya hore masa dan maganin nasa yana ci sosai
kamar yankan wuƙa indai ya baka insha Allahu za ka warke saidai fa in mutuwa
ce to ba yadda za'ayi.
Kasantuwar yanayin gidansu mahaifin nawa ya sa
mutane basa san mu'amala dasu duda kuwa sunsan da fewar maitar gidan ba me
cutarwa bace dan kuwa bazaka taɓajin
ƙorafin
wani ɗan gidan ya kama
wani a waje ba.
Duk wanda ya isa aure ayaran iyalin akan yaɗa shi aure da ‘yar
uwarsa ko ahaɗata da ɗan uwanta domin kuwa mutane
basa yadda kan su basu auren yaransu ko kaɗan
hakan baya damunsu domin kuwa suma ba lefi suna da dangi masu yawa ta inda wani
be rasa abokin aure.
Da yawa cikin ‘ya’yan kakana basu da sha'awar sana'artasa
duda kuwa yana san ace yasamu Magaji cikinsu Baba musa ne ma wani zubin yakan
nuna kulawa ga yaga yadda mahaifin nasu ke abubuwa.
Cikin masu ƙin sana'ar mahaifin nasu harda mahaifina
wanda shi ya zaɓi sana'ar
fatauci dan karatun ma yaƙi duk yadda mahaifinsu yai yaƙi domin iya primary bn kawai yayi itama
daƙyar
ya ƙarasa
hakama na addini ba wani nisa yai ba dan ko hizifi guda ba'ace ya haɗa ba tun da ya samu na
sallah ya dena zuwa.
Cikin iko da ni'imar Allah sai kasuwancin nasa
yai albarka domin kuwa komai ya taɓa
sai yazama kuɗi hakan
ya sa mutane ke cewa ai shi ɗin
akwaishi da nasibi.
Ganin Allah ya sanyawa kasuwancin nasa albarka
ne yana samu sosai ya sa mahaifunsu ya buƙaci da yai aure nan ya ce yana san ya
nemi yar gidan ƙaninsa wato Batulu domin alokacin kusan ita ce sa'ar aurensa
duk yarane ‘yan.
Saidai fa kwata kwata Batulu ba ta cikin
tsarin matan da Abdurrashid yake ganin sun dace da burin zuciyarsa na mace
hakan ya sa ya ce shifa gaskiya baya santa duda kuwa ya san afaɗin garin kano babu mai ba
shi ɗiyarsa ya aura
anman haka ya nuna shifa tabbas baya santa.
Hakan ya sa mahaifinsa zuba masa ido kawai ya
ce aƙyaleshi
inyaje yaga ya rasa matar aure zaizo da kansa yana neman auren batulun yana
bada haƙuri.
Fatiha ta ɗan
numfasa kamin ta cigaba inbaka mance ba nace maka mahaifina Fatauci yake.
A harkar
fataucinsa babu garin da baya zuwa cikin Nigeria wani zubin har maƙotan
Nigeria fataucinsa ya kaishi garin makurɗi
fahintar da yai kasuwanci agarin da riba ya sa har shago ya kama inda in ya zo
yake zama masaukinsa.
Yakanyi watanni agarin kan ya waiwayi gida
hakan ya sa yasaba da mutane da yawa musanman ‘yan unguwar da yake zaune domin shiɗin akwaishi da saurin sabo
saboda mutun ne shi mai faran faran da jama'a ga zaulaya.
A garin makurɗin
ne Allah ya haɗashi da
wata yarinya mai suna sakina wadda gidansu ke lokon da ya kama haya daga
gaisuwa wani zubin kuma sukan ɗanyi
hira dan takan ganshi agidansu wajen yayanta har suka saba indai ya ganta saiya
zaulayeta.
Sannu ahankali shaƙuwa ta shiga tsakaninsu
dan haka kawai takan fito susha hira ita da shi koda yayan nata basa nan kafin
wani lokaci sun fahinci irin soyayyar da suke ma juna .
Sakina haifaffiyar garin makurɗi ce mahaifinta ɗan kano ne aikine yakaishi
makurɗi har ya haifesu
daɗin zama ya sa ya
kasa dawowa gida kano sedai suzo da ziyara duk ‘yan uwansa suna garin kano shida yayansa
ne kawai anan makurɗin
wato Alhaji sule wanda shi kasuwanci ne ya kawoshi nan makurɗin.
Iyayan sakina su bakwai suka haifa shida mata
sai ɗaya namiji yayin
da kuma alhaji sule yake da yara uku duk maza hakan ya sa suke san ɗiya mace da yara domin su
haihuwar ba me yawa suka samu ba.
Ganin mahaifin sakina yana da yara masu yawa
ya sa matar Alhaji sule ta nemi da subata biyu ta riƙe sukako ji daɗi dan ba wani arziƙi suke
da shi ba Salima da Sakina suka basu wanda Sakina ce babba dan inda take Ss 1
zasu tafi 2 yayin da ita salimar ke a JSs 2.
Akoyaushe burin Hajiya Shatu shi ne sakina tai
candy su aurawa Babban yaron su ita ita kuma salima su aurawa ɗan autansu itadan harma sun
sanarwa da iyayansu sakinar sun kuma yi murna sosai.
Yadda suka riƙe su sakina riƙone na amana kamar
yaransu suka ɗaukesu
habu abin da su sakinan zasuce sun rasa sedai ma ace sunfi jin daɗi anan fiye da agidansu dan
gidansu suna da yw yayin da kuma mahaifinsu bai da ƙarfi sosai.
Saidai fa kan kowa ya ankara soyayyar
Abdurrashid tai ƙarfi azuciyar Sakina wanda har batajin za ta iya rayuwa ba da
shi ba sun shaƙu irin shaƙuwar da mai rubutu bazai iya rubutawa mai karatu ya fahinta
ba.
Sakina suna
Ss1 3rd term Abdurrashid ya nuna shifa yana san ya futi ai aure dan ya jima da
shiryawa ta nuna itafa tafisan tai candy abinka da shi ba wani mahincin illimin
ya sani ya dage harseda ya juyo da hankalinta ta amince abinka da shi namiji ne
kuma ya girme mata.
Yayin da
shikuwa tsoron girman yarinyar yai da yadda yaga tana kuma kyau ga farin jinin
samari hakan ya sa yakeso suyi auren kar aje amasa ƙafa dan yana santa sosai
in yai sake ya rasata ya san zai sha wuya.
Ganin dai ya
takura da batin auren ya sa ta cire kunya ta tunkari mariƙiyar
tata da batun hankalun Hajiya shatu yai mugun tashi dan tasan shirun su ya
tasarma rushewa na haɗa
auren zuminci dan yadda tasan sakina da kunya tun da ta zo mata da batun auren
take so tasan tabbas tana matuwar san yaron.
Duk yadda
ummanta mahaifiya da mahaifinta suka so fahintar da ita kan kartai butulci taƙi ta
nuna itafa Abdul kawai takeso ganin haka ya sa kowa yai fishi da ita kowa ya
fita sabgarta duk dan ta mance da batun Abdul ɗin
saidaifa kamar ƙara mata sansa suke dan lokacin da kowa ya fita sabgarta shi
ne yake kwantar mata da hankali yake kuma nuna mata irin san da yake mata yake
kwaɗaita mata irin daɗi da kulawar da za ta sha
agidansa akuma gurinsa hakan sai ya ƙara ninka shaƙuwarsu.
Ko makaranta
ma Sakina dena zuwa duk kuwa da yadda ada ta ɗaukaki
karatu ta ba shi mahinmanci duk ta faɗa
ganin kar yarinyar mutane ta cutu tumda iyayanta sun musu kara ya sa Alhaji
Sama'ila da kansa yasamu mahaifinta ya ce shi gurinsa babu komai suma karsuji
komai ai sakina ɗiyarsa
ce dan haka bazai mata auren dole ba akwai wasu yaran ƙanne da yayyenta se ayi
zumuncin.
Haka iyayanta
suka haƙura
duda basu soba Alhaji sama'ila ya wuce gaba wajen auren nata.
Koda
mahaifinta ya sa aka masa bin cike akan Abdurrashid ɗin nan suka gano ko shi waye da sana'ar
mahaifinsa nanfa hankalinsu ya tashi nan suka saka Sakina a gaba suka mata
bayani da fatan ta ce ta haƙura bama sai an mata dole ba.
Buɗar bakinta ta ce ina ita ai
a musulunci babu maita sai kanbun baka wanda kuma dan mahaifi nada kanbun baka
ba yana nufin cewa ɗan
sa yana da shi ba dan haka Abdul ɗinta
ba dole bane yana da shi ta ji ta gani tanasam sa za ta aureshi.
Duk zagi da
hantara da iyayenta ke mata haka ta rufe ido taƙi haka suka haƙura da faɗan dan sunga ba zai yi ba
suka koma lallashi da nasiha anman ta ƙi sairaronsu.
Ganin ta
bijire ta nace ya sa mahaifinta da mahaifiyarta suka ce sun janye hannu dags
kanta basu ba ita ta ce itafa ta ji ta gani dan tana ji aranta fishi ne kawai
sukai in lokaci yaja zasu haƙura aganinta.
Alhaji
Sama'ila ne da matarsa su sukai mata komai aka kaita ɗakinta wato ɗakin
mijinta anan makurɗin
inda za ta zauna ba shi da nisa sosai da gidan iyayanta.
Sakamakon
Alhaji Sama'ila sun saba da riƙe mace ya sa lokacin bikin cikin yaran da
sukazo daga kano suka roƙi Balaraba da ta bar musu ɗiyarta
Hadiza su haɗa da
Salima ƙanwar
sakina tun da mahaifin Hadizan ya rasu aiko Balara ta ji daɗi nan ta bar hadiza kan
sauran kayanta za a aiko Driver ya zo ya ɗaukar
mata.
Watansu Sakima
takwas da aure suka taso suka dawo kaduna dam kasuwamcin sa alokacin yafi ci a
kadunan.
Zaman aurensu
zamane me ban sha'awa domin indai ka gansu sai sun baka sha'awa abu guda ke
damunta shi ne rashin haihuwa musanman yadda dangin Abdul suka takura mata
danma ba gari guda suke da su ba.
Shekarar
sakina ta biyar da aure sedai Allah bai ba ta haihuwa ba abin duniya duk ya
isheta dam in ta zo kano gidan su Abdurrashid iyayansa da ‘yan
uwansa suyi ta mata gori banda hantara dan abunne ya haɗe gs haushin yaƙi ‘yar uwarsa ya aureta ga haushin kuma
rashin haihuwa.
Akoyaushe ta
je kano da kuka ko da takaici take dawowa haka ma in waninsu ya zo da ƙunci
suke barinta Fahintar hakan ya sa Abdul rage mata zuwa kanon kazalika in sukazo
baya zuwa ko ina dan in yananan basa iya mata hakan ya maya daɗi sosai yakuma ƙara
mata san mijin nata.
Sedai matakin
Abdul ya ƙara
tura tsanar sakina ga dangin nasa suka ƙara sama ransu tafa shanye musu ɗan uwa.
Seda suka
shekara shida suna shirin shiga ta bakwai sannan ta samu ciki murna gurin ta
ba'a magana haka ma Abdul dan zanma iya cewa yafa fi sakina murna.
Alokacin kuwa
Abdul ya zama babban Alhaji dan kuwa Arziƙinsa sai san barka dan tun suna shekara
ta huɗu da aure sukaje
saudiyya shida matarsa.
Watanta tara
ta haifi yaronta santalele me kama da mahaifinsa ya ci sunansa Abbakar aiko an
kashe kuɗe ranar suna
alokacin sakina ta kuma tabbatar wa Abdul ita yake so ba wani abu nata ba dan
alokacin se take ganin kamarfa sabon shafin soyayya ya buɗe agareta da yaronta.
Haihuwar
Abubakar se ta zama kamar an buɗe
mata haihuwar dan tana yaye shi ta Haifi umar sannan usman datai na huɗun ne ta roƙi ya
sa mata sunan mahaifinsa shi ne ya sa Ibrahim nanmafa taga jalala a family ɗinsu wai besa sunan
mahaifinsa ba se nata ita dai ta toshe kunnenta kawai.
Tun haihuwar
Ibrahim se yazama kamar an rufe mata haihuwar sedai alokacin ba ta wani damu
dan tana ganin su Abbakar agabanta kuma alokacin babu me kiranta juya dan ta
aje har huɗu.
Seda ta shekara takwas dan har ma sun cire rai
suna zaton ko ta gama ne sannan ta kuma samun ciki murna gurin ma'auratan kai
ka ce haihuwar fari ce.
Alhaji Abdul alokacin ma dai yafi Hajiya
sakina murna sanshi aduniya yana san yara musanman ma ace Sakinansa ce za ta
haifa masa.
Lokacin da sakina ta je asibiti aka ce mata
macece tai murna sedai fa Abdurrashid yafita murna danshi akwai da san ɗiya mace duk se ya ƙagu
Sakina ta haife masa me kama da ita.
Tun cikin na yaro yake waƙar
Fatiha zai samata.
Tun farkon cikin abubuwa marasa daɗi ke samun mahaifina
akasuwancinsa na asara.
Abinka da ‘yan gargajiya nanfa danginsa suka hau faɗin anya ba hannu aka saka
masa ba tun da da lokacin da auri sakina arziƙinsa haɓaka
yai bare suce ita ce me farar ƙafa.
Yanayin yadda yake asarar ya sa ya fara yadda
da hannun aka sa masa abinka da wanda be wani illimin addini me nisa ba .
Ran Litinin mahaifiyata ta fara naƙuda
hankali tashe mahaifina ya ɗauketa
sukai asibiti dan Allah ya temaka lokacin ya zo dan lokacin yakan yawan tafiya
hakan ne ma ya sa ya ɗauko
kakarsa dan kar haihuwar ta zo yazama ita kaɗaice
agidan.
Basu jima da zuwa ba nurse ta fito take faɗa masa ai ta sauka ta samu ɗiyarta mace murna gurin sa
ba'a magana ya miƙe yana faɗin
zan iya shiga in ganta ta ce eh dan asibitin kuɗi
ne ita kaɗai ce aɗakin.
Wayarsa ce tai ƙara ya dakata ds shiga ya ɗaya muryar yaronsa ya
tsinkaya yana faɗa
masa ai wuta ta tashi a kasuwa cikin shagunan da suka kama harda nasa bakuma
yajin akwai mamora kasa shiga ɗakin
yai ya koma ya zauna daɓas
hankali tashe yana faman innalillahi wa'inna ilahi raji'un yayin da kaka kuma
keta faman faɗin kai
ita dai wannan yarinya batazo da arziƙi ba yayinda shi bama jinta yake ba dan
shi kaɗai ya san me
yakeji aransa.
Ya jima azaune kamin ya miƙe zai
bar asibitin nurse ɗin
ta fito riƙe
da baby ta miƙa masa ya amsa yana shafa kanta ya shiga ɗakin da matarsa take wato
ummana ya mata sannu sannan ya faɗa
mata abin da ya faru hankalinta ya tashi ya ce shi zai je dan ganin ya ake ciki
seda yamin huɗuba da
Fatiha ya kwantar dani gefen ummana yana shafa kaina kamin ya fice.
Koda yaje alokacin hankalinsa ya kuma tasha
dan be yi zaton abin yakai haka ba dan babu wani abin mora komai ya ƙone
abinka da wanda ya nema da gumin sa yai kuka sosai dan ya san zafin dukiyar sa.
Yayin da Danginsa daga kano ke ta faman cece
kuce kanwai yarinyar nan ita ce silar komai duba da tun randa aka samu cikin
yake tafka asara kama da haihuwar ta.
A cewarsu wai na kwaso babbar maita daman akan
samu haka wani maitarsa tafi ta kowa zafi.
Ummana ce ta sayi ragon suna ganin ko maganar
bayau zatonta sabida matsalar da ya faru da shi ne dan batasan tayar masa da
hankali.
Watana uku a duniya mahaifina ya tattaro
iyalinsa daga kaduna zuwa kano dan kasuwan cin kadunan yaƙi ci.
Lokacin da muka dawo kano yana da gida anan
rijiyar zaki da ya sa ‘yan haya kan mu dawo ya tashesu nan mukai masauki.
Alokacin rayuwa tai mana zafi dan kuwa komai
yafaƙi
ci hakan ya sa ummana ta ce tun da gidan da muke ciki babbane kuma unguwar
tanada daraja mai zai hana ya saida gidan ya siya mana ƙarami anan gaida sauran
kuɗin sai yaja jari
sosai yaji daɗi kuwa
dan hakan yayi yaja jari.
Babu lefi kasuwamcin yana garawa sai dai duda
haka ba kamar da ba alokacin ida shekara guda harda watanni ina yawona ka ina
sai dai tun alokacin mahaifiyata ta fahinci mahaifina baya shiga sabgata dan ko
abu ya ce ummana ta masa in ta ce Fatiha takema abu yanzu zai balbaleta da faɗa wai tana sangarta ni yai
waje cikin fishi.
Ranar da aka sa za a yaye ni alokacin ne akai
wata gobara a sabon gari ciki kuwa harda shagon mahaifina hankalinsa ya tashi
sosai dan kuwa har faɗuwa
yai.
Duk wanda ya zo daga gidansu Abdul ɗin wato mahaifina jaje sai
kaji suna shaguɓe kan
wai sanadiyya ta komai ke faruwa da shi ahankali mahaifina ya gama yadda da
batun ‘yan
uwan nasa duba da hujjojinsu abinka da wanda bai wani illimi mai ƙarfi
ba.
Ya riga ya gama yadda da cewar indai har abin
farin ciki zai sameni to tabbas abin takaici zai sami me ɗaukan nauyina sabida wai
nice na gaji wata yayar kakarmu domin maitarta mai zafi ce itama haka abubuwa
ke samin mijinta indai zai faranta mata maganin abun kawai shi ne fita sabgata
da nunan tsana.
Duda kuwa duk yaron da aka haifa ana karya
masa maitarsa saidai acewar su irin tawa tafi ƙarfin karyuwa.
Alokacin inada
shekara uku aduniya aka haifa min ƙani wanda ya ci sunansa Aliyu tun lokacin
ko faɗa mukai da yaro
se yaita cuta ko dan iyayansu sun canfa ne oho hakan kuwa ya ƙara
tunzira mahaifina da ƙara tsanata aduniya babu wanda nake tsoro kamarsa dan kuwa
yana ganina zai hau muzurai yakuma hauni da faɗa
gashi lokacin kakana yarasu wato mahaifinsu su babana bare ace zai yi maganin
abun su kuma yaransa basu wani san komi kan sana'ar tasa ba.
Mahaifina bai shawara da mayaifiyata ba ya
saida gidan da muke ciki na gaida tun tana jin jita jita ba ta yadda ba har
seda ya zo da akori kura ya ce wai kaya za a kwashe za mu koma gidansu wato
gidan kakana dan daman duk mara ƙarfi kawai shatar guri yake ya zauna
shida iyalinsa dan gidan akwai girma.
Koda ummana tai magana ya hauta da faɗa wai ai duk lefinta ne da
ta haifo masa masifa haka kawai yana zaman zamansa ds arziƙinsa
ta haifo masa tsiya alokacin ummana tai kuka sosai na bijirewa iyayanta dan
tasan baƙin
cikin da tasasu ke bibiyarta.
Lokacin Aliyu nada shekara 3 inada 6 ummana ta
nemi akaini makaranta Abbana da kansa yakaini dan har lokacin be gama cire
hannunsa akaina ba nan yakaini primary ta gwamnati da ke unguwar tamu nai murna
sosai dan kuwa akwaini da san karatu.
Banda yaya mace se yayye maza tun haihuwata
nake yar gata agunsu komi suka samu na Fatiha ne ko Ali dake ɗan auta basa ji da shi
sabida suna san mace ni kaɗai
kuma suke dani hakan ya sa sabida yarinta banwani damu da rashin kulawa ta
mahaifina ba.
Sesai lokacin dana shiga primary ‘yan
ajinmu kowa kance babansa ko Abbansa yai masa kaza yai masa kaza sai na fara
damuwa nagane bawai fa iya kulawar yayye nake buƙata ba ta uba ma ita ce mafi a'a la.
Babana bai sati da kaini makaranta ba ya tafi
Nijer da kuɗin gidan
da ya seda dan sayo shinkafa dan yaji labarin alokacin cinikin shinkafar ke
garawa.
Cikin rashin sa'a duk wanda ya sayi shinkafar
se ya dawo masa da ita dan kuwa duk ciki tai hunhuna alokacin mahaufina ya
fidda hannunsa akaina dan ya riga ya gama yadda da soki burutsun danginsa.
Tun tasowata mahaifiyata ta koyar mun da komi
nagani insa mass albarka hakan zai sa komada dagaske ne inada kanbun bakan to
babu wani abu da zai sami wannan abin da ya birgeni hakan kuma nake.
Tun bayan asarar shinkafar da yaine ya ce
shifa ina yama dena neman kuɗin
inje inci kaina da kaina badai dukiyar sa ba tun da dai inrasa wa zanma zalunci
sai ubana.
Kwata kwata ya dena zuwa ko ina sedai ya ci
yashi yaje salla ya dawo ya shige ɗaki
yai kwanciyarsa.
Ummana ita take mana komi da temakon yaya Habu
in yaje makaranta ya dawo yakanyi buga bugarsa ya kawo ahaka muke rayuwa.
Kamin wani lokaci aka samu wanda sukai
convincing ɗin
mahaifina cikin danginsa kan cewar dole sai ya auri ‘yar danginsa arziƙin sa
zai dawo aiko dai ya yadda nan aka sa lokacin bikin nasa shida Batulu wadda
akai akai ya aura abaya yaƙi dan kuwa har lokacin batai aure ba.
Duk wainar da ake toyawa ummana batasan anai
ba sai ran kai amarya ta samu labari dan ba gida guda muke dasu batulunba bacin
ma haka mu bama shiga sabgar ‘yan gidan dan sun ware ummana.
Aikuwa ranar tai kuka sosai taita masifa
mahsifina ya mata banza zan iya cewa shi ne karo na farko dana ga faɗan ummana.
Washe gari ta kwashemu mukai makurɗi saidai fa ba ta wani samu
karɓuwar kirki ba bare
ta musu bayanin me Abdul yake mata dan babu fuska duda dai bakamar daba da suke
korarta satinmu guda acan ta tattaro mu muka dawo kano dan tabar Yah Habu da
yah Ummaru akano sabida su suna exam.
Ina primary 6 matar babana ta haifi ɗiyarta mace inda Abba na ya
sa mata Sakina aikuwa taita masifa baza'a sama ɗiyatta
sunan kishiyarta ba nan yaita rantsuwa ba sunan matarsa ya sa ba kawai dan yana
san sunan ne ta ce to ta ji anman wallahi baza'a ɓoyeba
dole kowa ya ce mata sakina ya ce Yaji yagani.
Duk soyayyar da mahaifina kema ɗiya mace se ya ɗiba ya ɗora kan ɗiyarsa sakina dan ya jima
yana san mace.
Mahaifiyata ba ta ankara ba sai labari ta ji
wai zai koma kaduna anman da iya amaryarsa zai tafi tai kuka iya kuka har ta
godewa Allah dan kuwa tasan ba ta isa ta hanashi ba inko ba haka ba yanzu aji
kansu.
Tun daga wannan lokacin da yabar kano se
lokaci lokaci yakanzo hayan watanni ya ɗan
kawo abin da ba'a rasa ba yaɗanyi
kwanaki ya tafi wanda in ya zo ɗin
mu hankalin mu atashe shi nasa atashe dan in ya zo yadinga masifa kenan ta
bagaira bare dalili seda yakai ya kawo kar cikin mu babu me san zuwan nasa.
Kusan ina Jss
ne ya dawo kano inda ya zo gida wurjan jan bayan wajen wata takwas da ya kwashe
bezoba yaita mun masifa wai duk sanadinane wallahi in ban sake masa mara ba yai
kasuwancin sa zai koreni daga gidan ya cireni cikin yaransa.
A wannan zuwan ne ya ce ya cireni amakaranta
yakuma hanani fitowa koda tsakar gida ne indai yana nan sedai inna ji fitarsa
masallaci in maza in abun da zan in koma ɗakina.
Alokacin bamu san me yasame shi bakuma musan
asarar me yaiba har ya dawo kanon.
Alokacin babu lefi yayyena sun tasa su ke
ciyar damu yayana usman shi ne yaban jari ya ce ba talla ba indunga zuwa bakun
lokon mu ina suyar ko waina kuma awara na zaɓi
awara duk wanda yake gida acikinsu to za ka sameshi gurin awarata suna tayani
zama hakan ya sa babu me kawon wargi in ba ita kazo siya ba kawai kazo surutu
ne yanzu zasu nuna maka hanya.
Kwanansu biyar mahaifina agida ya kwashi
amaryarsa da iyalinta suka bar gidan bamu san inda suka koma duda de har yanzu
suna kanon sedai lokaci lokaci yakanzo anman ya dena kawo mana komai sedai ya
kwashe abin da yayye na suka kawo yai gaba dasu.
Idan ummana tai magana yahauta da masifa yana
faɗin shida da yake
kawowa me ya sa ba ta magana se yanzu da yaranta ke kawowa to daɗinta bafa ita kaɗaita haifesu ba kuma ayanzu
ai haƙƙin
ci da shi yana kansu.
Ana haka yayana ya kammala makaranta yah Abu
da yah ummaru inda yah Habu yasamu aiki da FG suka tura su jigawa shi kuna ya
ummaru yake kasuwanci babu lefi yana samu.
Lokacin danai candy yah usmanma ya kammala
karatunsa yana koyarwa a secondry babu lefi yanzu ta fi mana da yayyena suka
biyamun kuɗin jamb
cikin ikon Allah naci aka ban abin da na nema agric naita murna.
Alokacin damuwata biyu ce ta farko ita ce ta
mahaifina yadda kullum kamar ƙara masa tsanata ake wanda lokacin da ya
samu labarin ai naci gaba da karatu harnai candy na cigaba da jami'a yaita
bala'i wai zai koren daga gidansa.
Sai abu nabiyu shi ne afamily ɗinmu kaf wanda suke sa'oin
aurena mata an musu aure mazan da suka rage kuma ba wanda yake sha'awar aurena
dan tsoron kar masifa ta dinta afka masa.
Yah Bashir ya dage shi zai auren iyayansa
sukace zasu tsine masa ina ji ina gani ya auri Badariyya duk da kuwa har yanzu
yana sona sedai ba inda muka iya.
Tun ina primary ba ni da wata ƙawar
kirki dan uwa ta samu labarin ɗiyarta
na abota da Fatihan gidan sarkin mayu tuni za ta raba mu.
Hakama ina secondry rimi rimi za mu fara ƙawance
da yarinya ta zo gidanmu se ta fara tsorona tun da dai gidanmu gidan mayu ne
hakan ya sa kaf rayuwar karatuna nake ni kaɗai
banda wata ƙawa
ko aboki.
Tun rashin saurayi na damuna har ya dena
sabida ada babu fitar da zan banyi saurayi ba sedai fa yana zuwa gidanmu zai
dena zuwa wani zubinma ‘yan gidan ke korarsa.
Hakan ya sa kawai na rungumi ƙaddarata
nake komai nawa ni kaɗai
har ko yaushe kake gani na anan ni ɗaya
dan abin da in saba da mutane su gujeni inzo ina damuwa.
Yayye na duk sunyi aure ina level 1 going to 2
babban yayi aure yah Habu dansu yah Usman sun rigashi aure.
Duk da sunyi aure basu fasa ɗaukan nayun karatunmu nida
su yah Ibrahim ba sun jima da hanani yin awara sedai dan bana san cika
tambayarsu dansuma ba wani ƙarfi garesu ba ya sa naƙi denawa.
Ayanzu nice kamar ‘yar auta dan ko Ali da
yake ƙarami
da ya samu abu to yanzu zai kawon gabaki ɗayansu
tausayina suke danma ummana ta hana da tuni ina Jigawa gurin yah Habu ta ce ina
bazai yiwu daga aurensa akaimasa yarinya budurwa ba.
Fatiha tai shiru kamin ta ce wannan shiene ataƙaice
wace ce Fatiha.
Cigaban labari.
Shiru kawai Fajar yai yana kallon ta
hankalinta ya tashi kodai shi ma tsoron nata yake ne ta ce daman na sani indai
kaji ni wace tuni za ka sauya ra'ayi ta faɗa
tana share hawayen da ya zubo mata.
Yai murmushi ba hak bane Fatiha kawai tausayin
kine ya cikani ya hanani magana ai shi so baruwansa da waye mutum kuma shi so
na gaskiya shi ne kaso mutum ka rungumi komi nasa ka maidashi naka sanki a jina
yake bazan denashi ba kamar yadda ummanki ba ta yadda da maitaba haka nima
kawai ki fara amsa sunan Amaryar Deeni tai murmushi dagaske.
Ba wasa nake ba ki faɗan yaushene Abban naku ke zuwa zanzo in
sameshi eh to ba shi da taka mai mai lokacin zuwa sai dai in ya zo zan kiraka
awaya in faɗa maka.
In za ka zo karka zo da mota karkayi wata
shiga me kyau in yafe mene sana'arka ka ce koyarwa ya ce sabida me tai murmushi
sabida in ka je da mota bazai baka aurena ba inkaje da shiga me kyauma haka
zaiji tsoron kar kaima ƙaddarar data faɗamasa
ta faɗa maka dsn haka
zaice zai baka Sakina ƙanwata.
Inko yaga baka da komi ko kusa ka kaɗan bazaima sakina sha'awar
auren ka ba dankuwa yana santa da yawa.
Ok kin ba ni satar amsa suka sa dariya gami da
sauya wata hirar zukatansu cike da annashuwa musanman Fatiha dan Fajar duda ya
san mahaifinsu zai amince sedai ta wani ɓarin
yana tsoron mahaifiyarsa kar taƙi amin cewa.
Koda Fajar ya
koma gida baima mahaifiyar sa maganar Fatiha ba sai da ya bari mahaifinsu ya
dawo sannan ya faɗa
masa komai game da game da fatihan ya ce ba komai indai ya tabbatar yana san ta
shi ke nan ba komai.
Sai dare suna cin abinci sannan mahaifin nasa
ke faɗawa ummam nasu.
Salima ya kira sunanta ta amsa gami da mai da
hankalin ta gunsa daman maganar Deeni ne kan aurensa na samo masa yarinyar da
nakesan ya aura ta ji daɗi
aranta aƙalla
dai ya sa hannu akan Deeni sanin halin sa ya sa ko tambayar sa wace yarinyar ko
a ina ya samo masa ita batai ba.
Kwana uku da yin maganar su Fatiha ta kira shi
take faɗa masa cewar
Abbansu yadawo yako ji daɗi
aransa ya ce zaizo kan ya tafi.
Da yan macin ranar da sukai waya da Fatihan ne
ya shirya tsaf cikin shigar farin yadinsa da yasha guga wanda inkai ba mai
mu'amala bane da ya dudduka bazaka taɓa
banbance shin mai tsada bane ko mai arha duda kasancewar simple shiga yai
saidai yai kyau sosai kwarjinin sa da zatinsa ya kuma bayyana.
Fajar Dogo ne bacan ba shi ba fari bane bakuma
baƙi
ba kalarsa wasu kekira da ruwan tarwaɗa
sumar kansa akwance take luf akansa wanda ko bai ta je ba ko bai aske ba za ka
ganta akwance yayin da sajen fuskarsa ke ƙara masa kyau da kwarjini duda yana
yawaita aske shi sai dai kan wani lokacin ya kuma kwanciya a fuskarsa.
Hancinsa da idanunsa duk na mahaifinsa ne
wanda idanunsa suke dara dara hancinsa har baka ataƙaice dai Fajar mai kyau
ne kyansa ke jan mata da yawa wajen kamuwa da soyayyarsa.
Sau da dama shike haska kaya inya saka ba kaya
ke haska shi ba hakan ya san ko wacce irin shiga ya ɗauki hankalin mai kallonsa.
Kai tsaye bakin titi yai dan tarar ɗan sahun da zai kaishi
unguwar su Fatihan.
Ji yai ana Malam ya juya jin kamar ya san
muryar murmushi yasaki ganin Faiza ashe dai zan ɗauki
murya itama murmushin tai kamin su gaisa ya ce daga ina haka naje gidansu
Fadila ne suka ɗan taɓa hira nan take ba shi haƙuri
kan abin da mahaifinta yai ya nuna mata ai komai ya wuce ya kuma nuna jin daɗinsa na yadda yaga ta saki
ranta tana rayuwa ta masa godiya kan admission ɗin
da ya samo mata ya ce ba komai sukai sallama yai gaba.
Ta jima tana kallon sa har ya ƙule
sannan ta share hawayen da tuni fa yanzu tana gidansa yana kiranta mamata tana
kiransa mijina Allah ka ciremin san wannan bawan naka ta faɗa sannan tai gida.
Har unguwar su Fatihan mai adaidaita sahun ya
kaishi abakin lokonsu maiɗan
sahun ya ajiye shi inda ya sauƙa ya miƙa masa kuɗin
nan ya hangi Fatihansa tana suyar ta sai yanzu fa ya tuna bai ce mata yau zai
zo ba ya ɗan jima yana
kallon ta yadda ya ganta fes duda ba kwalliya tai ba sai yaji ta burgeshi aƙalla
ita ɗin mai tsafta ce.
Gurin ya ƙarasa tana ganinsa ta diririce shi kuma
yahau dariya haba tawan mene haka kuma daga gani na sai ki wani daburce yah
Ibrahim yatoso lafiya dai Malam yai ɗan
murmushi Ibrahim ko eh nine fatiha tai mamaki yadda ya iya gane yayan nata da
sunansa bai bari ya kuma magana ba dan yaga ɗan
zafi ne yai saurin cewa pls gurin Abbanku za ka min jagora Fatiha tai saurin
cewa yawwa yah kuje ɗin.
A hanya yake faɗa
masa abin da ya kawo shi Ibrahim yaji daɗi
ya godewa Allah da baisa ya kwafsa ba wajen yima Fajar ɗin rashin mutunci.
Daman kasanni ne inji Ibrahim nop but taban
labarinku ta ce daka kai sai ita duda ka ba ta 8yrs but jikinka baya nunawa
Ibrahim yai dariya ai sun rainani ita da Ali Fajar yai dariya haka ƙanne
suke ai shi ma yai murmushi inda yai dedai da zuwansu ƙorar gidan Ibrahim ya
shiga bari in maka iso to Fajar ya ce.
Babu yabo babu fallasa yadda mayaifin nata ya
amsheshi kamar yadda ta faɗa
aiki da sa'arsa ya tara tambaya kamin ya ɗora
da ince kasan me za ka aura dan bana san se abu yai nisa ka ce na munafunceka
Fajar ya ce ya san komai ya yadda ya amince yakuma ji yagani mahaifin nata ya
ce to ka je zan sanar mata da matsaya ta inna gama nazari to ya ce sukai
sallama.
Yana fitowa daga ɗakin zauren ya ci karo da Fatiha ya ce sana'ar
fa tai murmushi yah Ib. Ya ce zai jire nan suka sami waje suka hau hira wanda
sai bayan lisha sukai sallama da juna cikin shauƙin ƙauna ya tafi tai gida.
Cikin kwana biyun nan duk hankalinsa atashe
yake ya kasa kwanciya sabida zullumin kar Abban Fatiha ya ce bazai ba shi ita
ba dan sai ayanzu ya kuma fahintar irin son da zuciyarsa kema Fatihan wato
zazzafan sone wanda bayajin ya taɓa
ma wata irinsa wanda kuma ya san babu wata mace da zai iyama irin wannan son
shi kansa har mamakin irin yadda yake jin ta aransa yake.
Kwana biyun nan sabida fargaba har faɗawa yai duda yana jin kamar
mahaifin nata bazai ce bazai ba shi ita ba sedai yana tsoron kar ya ce sedai ya
ba shi Sakina ƙanwarta.
💞
Don't forget to vote, comment and follow 💞
Fajaruddeen (Kashi na 6)
Tun daga
wannan ranar lokaci lokaci takan kirashi inda yake katse kiran ya kirata haka
shi ma yakan kirata kamin wani lokaci har sunyi sabo me ƙarfi wanda har basa iya
yini ɗaya bai kira ɗaya sun gaisaba ba.
Azahirin gaskiya Fajarudden mutun ne me murɗaɗɗen hali wanda in be baka fuska ba zakai zaton
ko kaɗan bai san maine
kirki balle kai zaton yana da shi anman in kai dace ya nuna maka other side ɗinsa zakai zaton samun
mutum mai kirkinsa zai matuƙar wuya.
Koda aka kafe result ma shi ya kirata yake
tambayarta Reg number ɗinta
kan in ya shiga zai faɗa
mata me ta samu tai murna sosai dan ba ta Whatsapp bare a turo ta duba gashi ba
ta da number in kowa bare ta tambaya.
Sosai yai mamakin abin da ta samu danshi
zatonsa damuwa bazata bari ta iya karatu ba da ƙarfin gwiwa ya faɗa mata ta samu 4.6 tai murna sosai gami da
masa godiya sun ɗan taɓa fira kamin su ajiye
wayar.
Gun ummanta ta nufa nan take faɗa mata an kafe sakamako ta
faɗa mata me tasamu
umman tai murna sosai itama.
***
Faiza ce zaune
abin duniya duk ya isheta gashi sanyi ake an bada hutun makarantar mangariba
bare taga malam hankalinta ya ɗan
kwanta ita ba abin ta kirashi ko ta je gidansu ba tun da bama tasan me za ta ce
ta je ko ta kirashi danshi ba.
Aɗa
ɓangaren yaya Bashir
yaƙi
kiranta bacin da ya san sunyi zai kirata yanke shawarar zuwa gidan su Bashir ɗin kawai tai dan ba ta da
aminin da ya fishi so take ta taɗa
masa abin da ke damunta dan gani take rashin faɗawa
kowa ya sa abin ke cin ranta.
Tsaf ta fito tai ɗakin ummanta, umma zani gidansu yah Bashir
umman tai ɗan shiru
alamun tunani take kamin can ta ce me zakije yi tai shiru shi ke nan ki je karki
zauna kar kuma ki kawon ƙorafi inkin dawo game da zuwan naki ta ce to umma gami da
ficewa.
Kai tsaye titi tai ta tari ɗan sahu basu da wani nisa
sosai hakan ya sa befi minti goma sha biyar ba suka iso danma ɗan sahun bai cika gudu ba.
Har ƙofar gida yakaita ta ba shi kuɗin sa sai da ta zura ƙafarta
gidan ta ji faɗuwar
gaba kamar ta juya ta dai daure ta shiga.
Da Balara mai wanke wanke ta fara gani suka
gaisa tai ciki tayi sallama yakai biyar ba'amsa haushi duk ya cika ta kamar ta
juya tadai daure ta kuma yin sallama can aka ce cikin faɗa waike kurma cene tun ɗazu ana amsa dan wulaƙanci shi ne zaki ishemu
da ihu ta shiga tana me sunsin da kai.
Kamar yadda ta za ta umman su Bashir ɗin na kujerar bakin ƙofa
amsa sallamar ne kawai ba zatai ba anman tahau ta da faɗa tana faɗin
wai ta amsa aƙas ta zauna tana gaida ita ƙasa ƙasa ta amsa.
Lafiya dai naganki da rana fatsar fatsar haka
cikin rawar murya take faɗin
gun yaya Bashir nazo baya nan umman tai saurin ba ta amsa to bari in jirashi
a'a ba yanzu zai dawo ba kizo ki tafi inyadawo ya zo to ta ce gami da yin waje
idonta na kawo ruwa ace kai bawa kaida gidan yayan Babanka sai dai kallo.
A ƙofar gida suka ci karo da Bashir yadda ya
ganta yasha jinin jikinsa a'a ƙanwar kinsan daga gida nake mami ta ce
kin tawo nan taɗan
saki yaƙe
harma zan koma ah haba ai kuma kinyi kaɗan
se kin koma munyi hira tai saurin zama a rumfar farfajiyar gidan dan tasan dai
bazai barta ta tafi ba tun da ya dawo.
Sun ɗan
taɓa fira kamin ya
tambaye ta me ya kawo ta tai ɗan
fari da ido kamin ta ce kaji yaya shi ke nan bazan zo mu gaisa ba sai wani abin
ya kawoni shi ma yai fari yana kwai kwayonta yana faɗin kaji ƙanwar shi ke nan ni bazan tambayi sis ɗina ba gabaki ɗaya suka sa dariya.
Faɗa
masa abin da ke damunta tai kan kaceme bugun zuciyarsa ya ƙaru
yayin da muguwar faɗuwar
gaba ya ziyarce shi ɗan
taɓo shi tai yaya baka
ce komai ba yai saurin sakin yaƙe ina tunanin mafita ne tai murmushi bari
in tafi kawai kayi tunani me yawa yanda za ka ban shawarar da za ta anfaneni
kaji yaya na yai murmushin ƙarfin hali yawwa kamar kinsan meke raina kuwa tai murmushi
gami da yin hanyar waje.
Juyowa tai yah ba rakiya yai saurin miƙewa
yayo inda take tsaye bari kawai ƙanwar inata tunanin mafita tai saurin
cewa ahto yi zaman ka kawai yai murmushi ah haba ai dole in raka ƙanwata
danma ina san yin tunani me kyau da ai kaiki zan yi tai murmushi kaji yaya
karfa ka ce na kawo maka aiki shi ma yai murmushi badai kiji na faɗa ba.
Seda ta hau ɗan
sahu ya juyo dan komawa gida sai dai yadda yakeji aransa baya jin zai iya
komawa gida bai fashe da kuka ba gidansu Salim kawai ya shige ya san bayanan ya
shige ɗakinsa kamar
yadda ya za ta kuwa salim ɗin
baya nan ya kullo ƙofar ɗakin
gami da rafka uban tagumi shikam wannan wace irin ƙaddara ce tahau shi
yarinyar da yakema matuwar so ya gama shirya rayuwarsa da ita ace ita ce ke
tambayarsa shawarar ya za'ai wani namiji ba shi ba ya sota shikam yau baƙar
rana ce agare shi.
Be san sanda hawaye ya hau kai kawo akuncinsa
ba tabbas ya san ya rasa Fa'iza yadda yaga san wani ƙarara a idanunta takaicin
sa ɗaya wai ace ma shi
zai bada shawarar yadda Rival ɗinsa
zai sota wannan wace irin masifa ce ya faɗa.
💞Don't
forget to vote, comment, share and follow 💞😍
Kafe result da
akai za mu iya cewa yafi komai yiwa Farida daɗi
duda ta ga me ta ci a group hakan besata cewa za ta je ganin result ba abin da
ba ta taɓa yi ba.
Sedai abin da ta je danshi ko sahunsa ba ta
gani ba bare tai nasarar ɗora
idanunta kan kyakkyawar fuskarsa ko zuciyarta za ta ji sanyi ganin abin da take
muradi haka ta dawo gida rai duk a aɓace.
Yadda ta tashi yau kan ta tafi makaranta ganin
result yaiwa iyayanta da ‘yan uwanta daɗi
sai dai yadda ta dawo a cun kushe ya tada musu da hankali wato dai ana ‘yar
gidan jiya mahaifinta yafi kowa damuwa domin yana matuƙar san ɗiyar tasa ko kaɗan baya san ganinta cikin
damuwa shi kam da zai san meke damunta ko dukiyar sa za ta ƙare
sai yai mata maganinsa.
Tunani tai ko dan sau ɗaya ta je shi ya sa ba ta ganshi ba hakan
yasata sauya shawara.
Gurin Dad ɗinta
ta je ta ce ya ba ta kuɗin
registration za ta je tayi ba musu ya ba ta dan baya san abin da zai ɓata mata rai ganin yau tana
cikin walwala fiye da sauran kwanakin da yake ganin ta duda tun da ta fara
makarantar ko sau ɗaya
ba ta taɓa zuwa yin
wani registration ba baima jin tasan yadda da inda akeyi.
Kai tsaye gidansu Ma'u ta wuce sosai Asma'u
tai murnar ganinta Farida ta tsuke fuska ai kyayi murnar ganina mana mara M ace
tun da akai hutu sau ɗaya
zaki kawon ziyara ma'u ta ce ai dai gara ni ke aikinzo Farida ta harareta yanzu
ai ba ni bace ko wallahi zaki sa in koma Ma'u tasa dariya sorry hajiya wasa
nake.
Seda suka ɗan
taɓa fira kamin Farida
ta ce pls rakani sch zakiyi ma'u ta ɗan
waro ido an koma ne mtsss farida taja tsaki abin da wulaƙanci aikema kinsan ba'a
komaba dai ko to inba'a koma ba me zakiyi farida ta kumayin tsaki kefa kinada
matsala yaushe kika koma ‘yar jarida koma barrister zance ne mai da wuƙar
bari in shirya faɗawa
umma to.
Farida ta miƙe bari in faɗa mata kawai malama kisa hijabi mu tafi to
jeki ki faɗo mata bari
in ɗauko hijan ɗin farida na ficewa ma'u ta
shige toilet.
Koda farida ta dawo masifa tahau yi ita ala
dole ma'u za ta makarar da ita itadai ma'u haƙuri kawai take bata.
******
Fatiha ce
zaune tana gyara waken awarar ta suna ɗan
taɓa fira sama sama da
ummanta wanda duk yawanci kan kuɗin
karatun su ne wanda yayansu zai kawo sai dai har yau baizo ba.
Fatiha ta dubi ummanta ta ce ina ganin umma kuɗin gurin ki na mai da kuɗin da nake ajiyewa na awara
za mu haɗa inyaso ko
rancene ki yi a haɗa
in yi registration ɗin
nan shi ma yaya Bashir sai yayi nasa in yaso in yah Umar ɗin ya zo se mu biya bashin
da kuɗin gurin sa.
Eh to kin kawo shawara anman me zai hana mu
jira zuwan nasa ai umma matsalar kar su rufe karɓa
in suka rufe ka kori kanka shi ya sa eh to da haka kuma zammasa waya ya haɗa kuɗin a natse in ya yaɗa ya kawo yawwa umma bari in duba inga nagun
naki zasuyi nawa baza su wuce dubu ashirin da ɗaya
ba inji umman.
Fatiha ta miƙe bari in ɗebo
in irga tana shiga ɗakin
ta ji sallamar babansu tai saurin ƙulle kuɗin
a bakin zaninta gami da tuttule mansau cikin ƙatuwar langa ta tura can ƙarƙashin
gadon umman tabar ɗan
kaɗan taliyar su ma ta
tura ƙarshin
gadon tabar guda huɗu
shinkafa daman sauran kaɗan
tabarta nai tahau ninkin kaya.
Tana jerawa a adaka ya shigo ɗakin ganinta yasashi sakin
tsaki gami da faɗin ke
ban hanaki shigowa ɗakin
nan ba in ina gida tai saurin zubewa aƙas tana faɗin
lah baba sannu da zuwa ya watsa mata harara dan gidanku baki ji me nake faɗa ba tai saurin cewa
wallahi baba abin da ka zo ba.
Munafukar banza munafukar wofi ki dinga wani
sun sun da kai se ka ce wata ta gari fice ki ban guri mara mutunci da tai gadon
tsiya hawayenta ta goge tai saurin shigewa ɗakinta
tana shiga kuka ya kwace mata itakam ta rasa me taiwa babanta ya tsaneta da
badan abubuwa da dama da suka tabbatar da kasantuwar ta ɗiyarsa itakam da ta ce ba mahaifinta bane.
Tana jin fitar sa zuwa Masallaci tai saurin
fitowa ta deɓo kayan
da ta tura ƙarƙashin
gado ta kawo nata ƙarƙashin gadon dan tasan in ya dawo ko ina sai ya dube a ɗakin in yaga an ɓoye a ƙarƙashin
gado kowa na gidan ya shiga uku ba ita ba.
Itakam ummanta bawai rashin zuwansa ko rashin
ci dasu da yake ƙinyi ke ba ta takai ci da shi ba face yadda yakewa tilon ɗiyar su mace kan hujjar sa
mara kai bare makama.
****
Ita kam Fa'iza
ganin tsahon kwana uku ba yaya Bashir bare shawarsa ya sa ta kiransa bugu ɗaya ya ɗaga cikin shagwaɓa take faɗin yah kafasan kai nake ta
jira yai murmushi har tana jiyo sautin sa ya ce hoo Ƙanwar gaskiya malam ɗin nan ya tafi dake da yawa
tai dariya bari kawai yaya kofa Bacci banayi wani takaici ya ziyarci zuciyar
Bashir yaɗan daure
kinga yanzu rubuto miki nake bai ƙarasa ba ta ce to bari in kashe ina
jiranka.
Kamin ya ce wani abu ta kashe yabi wayar da
kallo azahiri dan besan shawarar da zai ba ta bane ya sa ya ce rubuto mata yake
shikam bema san me zai ce mata ba gidan rubuta saƙo ya shiga ya rubuta mata ya daɗe yana kallon abin da ya
rubuta kamin yai gun dun balar turawa.
Tana karantawa ta buga tsalle ji take kamar
Malam fajaru ya zama mijin ta ma ya gama sakon ta turawa yayan nata
"shi ya
sa nake sanka yaya na nakaina na gode sosai Allah barmu tare"
Yana zaune
ransa cike da tunani kala kala saƙonta ya shigo kawai tsintar kansa yaida
jin daɗin saƙon
nata kasa dena karantawa yai ayayin da farin ciki ya cika masa zuciya ya
rungume wayar yana sakin murmushi.
Kome ya tuna oho yai cilli da wayar yana
furzar da iska.
Nace towo kai kuma ko lafiya dago idanunsa da
yai naga sun koma jawur na san inna kawo wargi zan iya shan naushi ya sa na
fice nayo gida.
💞
Don't forget to vote, comment, share and follow 💞😍
A'a umma wanke
wanke kike haka ina Fatima inji Fajarudden umma tai ɗan murmushi ba ta jin daɗi ne ina za ka haka ya
kalli kansa ba ko ina da na ɗan
fito zan leƙa
ne se ka dawo ai na fasa fitar ma ya faɗa
yana cire doguwar rigar jikinsa.
Kawo in wanke ya faɗa yana ƙoƙarin durƙusawa a'a kaga basshi ka je inda za ka
kawai nifa ba inda daman zani pls ki kawo ai na ma gama sedai ka ɗauko waken can ka tsincen
to ya ce yai inda waken yake.
Yana tsintar waken sina fira da ummansa ya ce
wai kuwa umma ina Abba ya fice tun safe kai shi ma dai Abba baya gajiya da fita
duda jikinsa be cika masa daɗi
ya za'ayi tun da yafi san fitar inji umma maganinsa ma ya kusa ƙarewa
kuwa gwanda ka siyo tun kan ya san ya ƙare ya ce karka siyo kasan dai halin sa.
Yau zan siyo insha Allahu yawwa gwanda dai yaɗan dubi umman ya ce umma
yadda yai maganar yasata fahintar me yake san faɗa
mata sai dai ba ta da tabbas takan ya sa ta tsaida abin da take ta mai da
hankalinta kansa na'am ta faɗa.
Ya ce umma daman wannan dai maganar ce tai
saurin ɓata fuska
cikin fushi take faɗin
wai kai wane irin mutum ne nace karka kuma mun wannan maganar indai baso kake
nida mahaifinka mu mutu mubar ma duniyar ba nace karka kuma anman dan ka raina
ni shi ne dole sekayi ko to wallahi ka kiyaye ne karka sake inji koda dawasa
kaiwa mahaifinka ita inko kasake ko abayan idona ne ban yafe ba.
Fuuu ta miƙe ta shige ɗaki
hankalin fajar yai mugun tashi ba abin da ya tsana sama da tadawa iyayansa
hankali ruwan da ya ɗorawa
umman ya haɗa mata ɗakinta ya shiga kuka kawai
take nan hankalinsa ya kuma tashi yai saurin ƙarasawa ya riƙo hannunta yana ba ta haƙuri.
Ganin taƙi dena kukan ne shi ma ya sa kuka ganin
haka yasata yin shiru to mene kuma na kuka ta faɗa
shidai cikin kuka yake neman afuwar ta tai murmushin ƙarfin hali shike nan ya
wuce yai murmushi yawwa umma na kin yafe min tai dariya ai daman bance kayi
lefi ba ina kuka ne dan ganin mun tauye ku matsayin ku na yaranmu mun ɓoye muku abin da yake haƙƙinku
ku sani sedai ɓoyewar
shi ne mafi alkairi kayi haƙuri kamin alƙawarin dena wannan maganar.
Ya kuma riƙe hannunta indai hakan zai saku farin
ciki insha Allahu bazan kuma ba tai murmushi yawwa jeka yanzu zan fito Allah ya
muku albarka ya ce amin umman mu ya fuce tana binsa da kallo tasan me ke
damunsa tausayin ƙanwar su fatima yake sedai suma duda kasan tuwar su maza abin
tausayi ne ta share hawayen cike da tausayin yaranta da mijin ta ta fito tai
bayi.
Seda ya gama girki ya yankawa umman tasa salak
sannan ya leƙa
ɗakin fatima tana
kwance da alamu ciwon ya lafa ya ce salak ɗinnan
na kawo ki ajiye na Baba ne na san insu Usman suka zo cinyewa zasuyi karki basu
kinsan kan salak se yaƙi ci abinci ta ce to yaya seka dawo ya ce Allah ya ƙara
sauƙi
ya fice.
Fajarudden kenan indai yana gida baida abinyi
ba abin da baya yi tun tasowar sa ummansu ta sabar musu da taya ta aikin gidan
kasantuwar duk maza Allah ya albar ka ce ta dasu autar ta ce kawai mace sun
riga sun saba indai ummansu na girka abu to duk wuyar sa kuwa suma sun iya dafa
shi.
Umman su ko kaɗan
ba ta da matsalar ɗiya
mace dan yaranta sun iya komai basu da kyashi musanman fajar da baida san jiki
ko fita zai inyaga tana aiki indai ba abu me mahimmancin gaske ba se ya taya ta
komai tare suke baida aminin da ya wuce ummansa.
Abu guda ne matsalar sa da ummansa yadda ya
kasa daure dena tambayarta sirrin da suka binne suke ganin ya binnu sedai tana
jin kamar daga yau bazai kuma ba dan tasan baya saɓa alƙawari.
****
Ita kam Farida
ko da suka je makarantar me makom taja kan motar zuwa inda zatai registration
Faculty ɗin su ta nufa
inda ta saba tsayawa dai ta tsaya sun kusan awaya uku babu alamun malan ma'u ce
ta gaji da zaman shiru ta ce pls Farida muje mana mutumin nan fa ba zuwa zai ba
kema kin sani.
Ta ina kuma na san bazai zo ba sai dai in ya
faɗa miki ne ki faɗan ma'u ta zaro ido ni
asuwa a ina zan ganshi ya faɗan
kawai dai kinsan ko lokacin ba'ai hutu ba inbaida lecture baya zuwa bare kuma
cikin hutu kinsan baida dalilin zuwa.
Dan Allah muje
kar ace mun yi zuwan kawai abin da muka zo danshi bamu samu munyi ba dan dai
kin nace ne anman ai registration ba dole se munzo sch ba shirun da ta ji
faridar tayi ne ya sa ta saurin kallonta ga mamakinta kuka faridan take.
Ya ilahi ni ma'u Farida dan Allah ki sama
kanki haƙuri
kan mutumin nan indai har mijin kine da kansa zai kawo kansa ki rage takurawa
zuciyar ki in ba mijin ki bane ba yadda zakiyi cikin kuka me tsuma zuciya
Farida ke faɗin na
sani ma'u nima abin da meke damuna ba da na kasa cire soyayyar sa cikin raina
wallahi ina san sa ma'u banjin zan iya auren wanin sa zan iya zama da shi kome
zaimin.
Dafe kanta ma'u tai ranta fal cike da tausayin
ƙawar
tata tasan tabbas tana matuwar san Malam tarasa wane irin so take masa haka
tausayinta duk ya cikata.
Fita tai daga motar ta zagayo koma can naja
muje ba tare da musu ba Faridan ta koma kujerar me zaman banza Ma'u ta koma
gurinta kafin taja ta ce ki yi haƙuri yau befi sati biyu ba a koma tun da
kika iya haƙurin
rashin ganinsa na watanni na san zaki iya daurewa na sati biyu.
Ki dunga Allah ya sassauta miki sansa karki
tsaya iya kan ya soki kawai kinji farida ta ɗaga
kai kamar wata yarinya alamar to suka ja motar suka bar Faculty ɗin....
💞Don't
forget to vote, comment, share and flow 💞😍
Rubutawa
Faɗima Fayau
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.