Ticker

Fajaruddeen (Kashi na 15)

Lokacin da Fatiha ta faɗa masa mahaifinta ya ce ya turo aifa yai murna iya murna ji yake kamar anbashi sarautar mulkin mutan Nigeria koma na nahiyar Afrika baki ɗaya ashe ada shi ba so yai ba shirme ne kawai yanzu ya san mene so me ake nufi da ƙauna yadda kawai cewa akai ya turo anman farin cikinsa yazama maras misaltuwa.

 Lokacin da ya jema mahaifin sa da batun shi ma yaji daɗi yadda fajar yaga farin ciki fuskar mahaifin nasa ya masa daɗi gami da yadda mahaifin nasu ya wuce masa gaba duda kuwa ba shi yaje ba amininsa ya sa saidai yaji daɗi dan ada baya sa baki a abun da ya shafesu.

 Lefen da ya haɗawa Fa'iza da suka dawo masa da shi shi ne aka fito da shi ya haɗo abubuwan da ba'a rasa ba maza ne suka kai duda kasantuwar lefen ba wani mai yawa bane sai dai za a iya cewa a dangin su Fatiha ba'a taɓa kamarsa ba sakamakon auren zumunci suke ba kuma arziƙi ne dasu ba.

 Kan ka ce mene wannan maganar lefen ta baza gari duk dsngin nasu maganar lefen suke inda da yawa maganarsu ita ce anya ba lashe kurwar yaron mutane taiba har yaji zai aureta ya haɗo da uban lefe haka.

 Sudai shiru sukai suka toshe kunnuwansu inda ummanta tafi kowa farin cikin ganin ɗiyar tata tasamu miji kuma wanda take so yake santa.

 Wata shida aka saka wanda shi ma yayyenta ne suka zaɓi hakan dan su samu su kintsa sosai yadda zasu fidda ƙanwar tasu inta fajar ne shikam asa ko wata guda ma yana jin yai nisa Yaita ma Fatiha mita ita dai dariya ma ya dinga bata.

 Cikin lokutan da suka rage soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi ƙara ƙaruwa tsakanin masoyan biyu gurin Zamansu na agric yazama matattar fajar dan yanzu ko zaman office baya yi yana fitowa daga aji zai yo gurin ko ba ta nan haka zai zauna yana jiranta yana kallon hotunan da ya mata awaya.

 Inko suka ɗan samu saɓani taƙi zuwa gurin sedai ta koma gida ta ganshi a ƙofar gidansu sosai suke san junansu kana ganinsu kaga masoya duda da wuya kaji suna hirar soyayya ko dan sun riga sun saba da hirar rayuwa ne oho.

 Tun Fatiha na jin kunyar kar ‘yan ajinsu suzo suganta da shi a gurin tun da sunsan malami ne dandai ya ɗaukesu GSP harta sake dan randa ta karanbanin ce masa dan Allah ya dena zuwa gun tun da dai yana zuwa gida kaca kaca sukai yaita mita wai ya gane shi baikai wanda zataso wasu su ganta da shi bane shi ya sa take faɗin haka taita ba shi haƙuri daƙyar tasamu ya yaƙura.

 Duk wanda ya san Fajar ya san da Fatiha ta jima da zama a ransa ɗalibansa ma sun sanda akwai wata me suna Fatiha arayuwar sa dan kuwa ko misali zai basu lokacin karatu za ka tsinci sunan Fatiha shi ne kan gaba.

Wannan sabuwar ɗabi'ar tasa ita tafi ɗagawa Farida hankali yadda taga ya dulmiya cikin kogin san wata duk damuwarta dai ta ƙaru duda kuwa ayanzu sun saba da shi sosai takan kirashi ma awaya su gaisa har wasa da dariya suke duk sanadin project ɗinta.

 Ada tana jin daɗin kiransa dam har hira suke ta chat ma haka sai dai banda ayanzu domin kuwa maga ɗaya biyu zai fara mata hirar wata Fatiha itakam ta tsani sunan sosai takejin kishin me sunan duda batasan ta ba.

 Ji take ina ma ita ce ta samu fajar tasan ko bakomai zatasha kulawa dan yadda ya damu da mesuna Fatihan nan ko ba ta waje tasan kam tanashan kulawa irinsu malam Fajar ne basu iya soba in kuma suka fara shi basu san wani abu denashi ba.

 Tausayin kanta ya cika ta itakam wannan masifa har ina haka.

 Fatiha kanta har tausayin fajar take yadda yakesan ta musanman in ta tuno ta mutuwa sai tausayinsa ya cikata ko ya zai yi in ta mutu tasan tana san sa sai dai yadda take ganin ƙaunarta ƙara ra atattare da shi ya sa take ƙarasa godewa Allah da yabata me ƙaunarta.

 Farida ce zaune a office in Fajar ita da Ma'u yana duba project ɗin da ta kawo masa sa'a ma taiyi taga office ɗin abuɗe ta shiga ta hau roƙensa kan ya duba dan ta kwan biyu da kawo wa kullin baya nan baya zama suna hira sama sama.

 Fatiha tai Sallama sanye take da leshinta milk da hijabinta ruwan zuma tai kyau sosai yana jin muryarta ya ɗago yana murmushi ta jima batazo Department ɗin yau mamaki tai niyar bashi.

 Yadda yake faman washe baki ya sa faridar Fahintar wannan ce Fatihan da alama ta zuba mata ido ta ganeta ita ce yarinyar da ta gansu kwanaki sai dai yau da ta kalle ta sosai se take mata kallon sani sedai ta rasa ina tasan ta.

 Fajar ya katse mata tunani da Faɗin Farida ga ƙanwata Fatiha ku gaisa farida ta daure suka gaisa yadda ya mai da hankalinsa kan Fatihar yabar duba project ɗin ya sa Farida miƙewa Sir za muje mu dawo ok kawai ya ce sukai waje.

💞 Don't forget to vote, comment and follow 💞

 Ayanzu fajar baya jin kunyar kowa kan Fatihar sa dan ko faculty ɗinsu ta je shi yake riƙo mata takaddun ta zuwa gun motarsa da yawa cikin ɗalibansa sun san yana san yarinyar yadda yake wani walwala in ya ganta.

 Yanzu ma zaune suke a kujerun da suke bakin political science department suna hira wucewa kawai zasuyi Fatiha ta dubi gurin ta ce gurin nan zai daɗin zama ya ce ko mu zauna ne a'a ta ce tunawa datai shifa malam ne beci aganshi da wata zaune ba gurin yai yazauna ta ce pls kazo mu ƙarasa ta nuno masa sociology department kaga fa har munzo kinga sedai in nine kike kyamar aganki tare dani.

 Kusa da shi ta je tazauna suka hau fira yana nuna mata posting ɗin mutane a twitter dan ita ba ta wani abu da ya shafi social media sosai suke jin daɗin yanayin kana ganinsu kaga masoya.

 Duk asabar da lahadin duniya inka lalubi fajar za ka sameshi a unguwar su Fatiha dan ma tana ƙi da tashi ne kullun shi zai ɗaukota yakawota makaranta ya kuma mai da ita ada ko old campus ɗinma ta dena binsa sai da taga yai fushi sannan sukai yar jejeniya kan iya old campus.

 ***

Ta ɓan garen Faruk kuwa abin duniya ya masa yawa tun lokacin da ya samu labarin saka ranar yarinyar da ya riga ya gama tsara rayuwarsa da ita yarinyar da dukkan burinsa akanta yake.

 Lokacin da ya zo gidansu Fajar ya zo yadda yaga ta sake tana ta walwala da wanda aka ce masa shi ne za ta aura ya tabbatar masa da tabbas yayi rashin burin zuciyarsa sedai duk da haka ya kasa zuwa ya kalle ta duda ba ta sani ba kusan kullin sai ya zo inda take sana'a wani zubin ma sai ta tashe yake barin gurin cike da tausayin kansa dan ya san shikam tuni ta mance da shi yadda yaga ita rayuwar ta kawai take.

 Ya san ta mance da babun sa tun da sau ɗaya suka taɓa haɗuwa ta da sunan so daga nan ta dena fitowa dan ta ji me kawoshi shi kuma ya ba ta hutu ko tayi tunani ashe besani ba hakan shi ne babban kuskuren da yai ya san ta jima dasashi a kwandon shara ya san tuni tai zaton daman ba son gaske bane duda ya san da wanda take so ɗin baya mata rabin son da shi yake mata nace uhummm faruk ke nan kanka kawai kasani.

 Komai aka sa lokaci asannu zai zo yau take ɗaurin auren Fajar yadda yake ta wani rawar kai da kai kawo har kunya yake baima ummansa itakam gwanda aɗaura auren na akawo ma Deeni matar nan ko ta samu ta huta da zumuɗi dan ita a gurin ta duk zumuɗi ne da ango kanyi in za a kawo masa amarya.

 Yayin da shi kuwa gurin fajar duk cikin farin cikin Fatihar sa ta kusa zama tasan agaske ta kusa dawowa kusa da shi suyi rayuwa ta har abada shi baima san yana wani abin ba sai an masa tsiya yakanyi murmushi kawai dan yanzu ya riga ya gama yadda da so kan mai da mutun zuwa wani daban da shi kansa baisani ba dan shi da kansa yana mamakin anya shiɗinne kuwa true love make life colorful.

 Ƙarfe uku dai dai aka ɗaura auren Fatiha Abdurrashid da Fajarudden Isma'il anan masallacin juma'a na BUK old campus.

 Fatiha na zaune ya kirata yana tsokanar ta kaga uwar gida gurin Deeni ta turo baki kamar yana ganinta wane irin uwar gida yai dariya mai da wuƙar ina nufin amarya kuma uwar gidansa ke ɗaya ce ki yi mulkinki daga ke ba ƙari tai murmushin jin daɗi har kasa na ji kunya wallahi.

 Hira suka ɗan taɓa irin ta masoya kamin suyi sallama ta rungume wayar tana jin daɗi wai yau ita ce tai aure kuma Deen ɗinta ta aura saƙon da ya shigo wayar ya sa ta duba wayar.

Assalamu alaikum

Sunana Faruk bana jin zaki gane ni ina miki fatan alkairi arayuwar auren ki Allah ya sa albar yabada zurriya ta gari na gode.

Tsintar kanta da cewa amin tai ta fice daga ɗakin jin ana kiranta.

 Shiko Faruk yana tura saƙon ya goge number ɗin da yai mata ma'ajiya da matata gami da share hawayensa yai inda ya ajiye motarsa ya jata yabar harabar makarantar.

 Kai tsaye gida ya wuce ya ɗauki kayansa driver ya jashi zuwa Aminu kano airport dan daman ya shirya kan zai halarci ɗaurin auren dan ya tabbatar da cewar da gaske ya rasa Fatiha dan baya san zuciyarsa ta dinga kawo masa tantama.

 Huɗu dedai jirginsu ya tashi inda ya nufi Jordan dan can ya nufa ba kuma ranar dawowa dan ji yake duniyar ta masa zafi musanman ƙasar tasa Nigeria.

 Da yan macin ranar juma'ar ne da aka ɗaura auren Fajar ya zo gidansu taƙi fitowa aikuwa yaƙi tafiya har magariba ganin haka ya sa ummanta tasa dole ta fito aiko ta haɗe rai sedai yadda yaketa zolayarta yasata dariya ta ce wai mutum shi ma dai anman ai lahadi kaman yaune ya langwabar da kai ni wallahi dama abar bikin mayi abunmi haɗe da na suna ta zaro ido kaga nayi gida tai ciki tana dariya ya hau kwala mata kira shi ma yana dariya ganin taƙi dawowa ne yasashi jan motarsa yai gida ransa fes.

Ranar asabar aka sa ita ce kamu anan gidan maƙotansu za'ayi inda ‘yan uwan Fajarudden zasu zo dan kama amarya.

 Amarya tai kyau sosai kamar wata zinariya kai bazaka ganta ba kai zaton ‘yar gidan talaka ce ba zato zakai wata ‘yar hamshaƙin mutun ce duda ba wata shigar alfarma taiba.

 Fatiha Fara ce ba sal ba mai tsayi ce cikin mata tana da jiki ko ba za a kirata siririya ba haka baza'a kirata lukuta ba tana da yalwal sumar kai wanda ta sakko bar wuya yayinda gaban goshinta ma gashinta baƙi siɗin ne a kwance dake ƙara mata kyau kazalika tana da dara daran idanu wanda suke farare tasa gashin idanunta ma zara zara ne girarta kamar zana mata akai ba ta cika dogon hanci ba sai dai ya dace da yanayin ta ita ɗin me sanyi ce hakan yake ƙarawa fajar san ta dan yansan mace me sanyi arayuwar sa komai tai birgeshi yake.

 Kowa yaganta sai ya yaba da yanda tai kyau jan les ne a jikinta mai adon baƙi da zaiba simple make up aka mata tai kyau sosai kowa yaganta ya san tabbas ita ce amarya ita da kanta tasan tai kyau har mamaki take na kyan da tai take .

 Cikin ‘yan uwan Fajar ɗin da suka zone Hajiya Basira Matar aminin mahaifin Fajar ta fito da sauri tana faɗin Ubaida ubaida!!! Wadda ake kira ɗin ta juyo ganin me kiran tai saurin ƙarasowa tana murmushi suka gaisa Hajiya Basira ta ce kardai ki bikin ɗiyar tawa kika zo eh anman ta gurin ango ayya nifa ince suka kuma gaisawa gami da tambayar juna bayan saduwa.

 Kinga ikon Allah aure me haɗa zumunci bayan lokaci mai tsayi min sake haɗuwa wallahi fa ai kimma san mahaifiyar Amaryar inji wadda aka kira da ubaida dan Allah fa inji Hajiya Basira nifa ince danaga yarinyar na rasa ina na san me kama da ita .

 Yarinyar fa wajen Sakina ce sakina dai wacce sakinar Saliman ki fa karfa kice tun abin da ya faru ba'a zuminci ke wace Sakinar kar kice mun yayar Salima eh ita fa innalillahi wa'inna ilahi raji'un to ai yaron Deeni ne ɗan wajen Salim Haj. Ubaida ta zaro ido na wajenta eh subhanallah anso ayi kwaɓa aibabu aure tsakaninsu.

 Ya akai aka ɗaura maza basu fahimta eh to kinsan mahaifin yarom beje ba itama na yarimyar baijeba to da madatsala shi ya sa nace suyi bincike suƙa ƙi inji Haj. Ubaidah kinga ban ga ta zama ba daman gurin Sakinar zani zan amso abu sai insanar mata inui Haj. Ubaida ɗin nima kinga bari mu koma asan abinyi tun kan duniya ta ɗauka an ɗaura auren Yaya da ƙanwarsa...

Rubutawa

Faɗima Fayau

Fajaruddeen

Post a Comment

0 Comments