Fajaruddeen (Kashi na 3)

    Yauma kamar kullin tana zaune aƙofar Faculty ɗinsu ta baya tana kallon ɗaliban dake shawagi tsallaken Faculty ɗin wato geography kamar ko yaushe gurin ya kalla tana zaune shikam zai so jin meke damunta da kullun take zaune ita kaɗai cike da tunani shikam zaiso jin matsalarta ko zai iya magance mata ita ya fuskanci damuwa ce ta ke damunta har take zuwa gurin ta zauna.

     Motarsa yaja acan É—an nesa da ita ya ajiye ya tako inda take kamar rannan sallama ya mata saidai yau É—inma ba ta amsa ba.

     Bai damu da rashin amsawar tata ba ya sa littafin hannunsa ya É—an taÉ“o ta tai saurin jiwowa a tsorace sannu ko yafaÉ—a yana mai nuna mata littafin hannunsa alamu da shi ya taÉ“ata na miki sallama baki ji ba ko zan iya zama ba ta ce komi ba iya É—an kallonsa da tai da alamu nazarinsa tai kamin ta É—an matsa alamar ya zauna batare da ta ce kasa komi ba zama yai gami da cewa na gode ba ta ce komi ba ta cigaba da kalle kallenta.

     Sunkai minti talatin kamin ta É—an duba agogon da ke hannunta miÆ™ewa yaga tayi ba ta ce masa komi ba ta bar gurin juyawa yai yabita da ido harta Æ™ule sa'annan shi ma ya tashi yabar gun.

     Tun daga wannan ranar kullin ya kanzo saida ba maganar da take haÉ—a su ahankula yake nazarinta so yake ya gama fahintar ta kamin yai tunanin yadda zai shawo kanta sai dai ita É—in tana da wuyar fahinta har yau abu guda yakai ga fahinta game da ita wato tana da damuwa babba.

     Allah mutumina kana abin da kake so a Faculty É—innan tamu yaÉ—an murmumusa towo me nayi kuma ai kaima kasani kagafa yadda kake jan yaran mutane aÆ™as yaÉ—an ja Æ™aramin tsaki fahintar dani nake jansu aÆ™as kamar yaya fa.

     Ai kaima kasani ah haba na sani kamar ya fa haba malam ai Æ™arya kasa sanin yadda ‘yan matan Faculty É—in nan suka gama matowa akanka.

     Ni kuma ya dafe Æ™irji gami da zaro ido su waye ke nan mahamud ya sha kunu kai abin da iskanci muma mukasan suna sanka bare kai da ake so sai kaita jan aji har ajin ya tsinke wai kai baka fahinta ba.

     Ina kuwa zan fahinta ina kaima malami ne me ya sa kai baku gano suna sanka ba ko kuwa za ka ce min sa idon naka basu gano haka ba ko kuwa na taÉ“a baka labarin wata cikinsu ta zo guna zance ko kuwa kai sun taÉ“a baka saÆ™o ka kawon eyy yadda ya wani haÉ—e rai ya tsare gida yana magana yabaiwa Mahmud dariya.

     Dariyar da ya sa ce tabaiwa Deen haushi yai tsaki kana da matsala Mahmud wallahi ya miÆ™e yabar office É—in.

     Farida ce zaune cikin motar ta tana duba course É—in D dan Captain ya faÉ—a mata É—azu wai ta zo zai mata test Æ™arfe uku hakan ya sa take ta duddubawa tasan duk mugunta ya taka shi ya sa yaÆ™i fawa Captain É—in sai ayau É—in wato inbata zo bama shi ke nan se ya ce ba ta zo ba in tai kamar za ta ji haushinsa sai kuna zuciyarta taka sa jin haushin nasa itakam gangar jikinta na faÉ—a mata zuciyarta cutar ta kawai take sedai ta kasa fahintar haka.

     Tana ganinsa ya fito daga office É—in malam mahmud ta miÆ™e ta bi bayansa.

     Yana shiga ta kwankwasa yafi minti uku kamin ya ce yes shigo da sallamar ta tashiga ya amsa murya Æ™asa Æ™asa za ta rufo Æ™ofar ya ce mene haka zaki wani rufen Æ™ofa tai saurin barinta a buÉ—e ita É—in ba mai tsoro bace maganar maza ba ta tsorata ta ko dan cikin masa ta tashi oho sai dai shi kwarjinsa yai yawa muryarsa razanar mata da zuciya take.

     Shigowa tai jiki a saluÉ“e gami da gaidashi ina jinki ya ce ba tare da ya mata amsar gaisuwar da tai ba eh daman Captain É—in level 2 Department of phsycology ne ya ce in zo kana nema na.

     ÆŠagowa yai yaÉ—an kalle ta gami da faÉ—in ni kuma to kimin mene cikin rawar murya ta ce nice wadda level coordinator ya ko takardar banda lafiya za'amin make up nazo ka ce se naje gunsa ok Farida ko ya faÉ—a idonsa kan takardar da yake karantawa tai saurin cewa eh tana murmushi.

     Tsaki yaja shi ne kuma daga dawowata zaki wani zo eh daman monitor É—in namu ya ce inzo before 3 ya É—an kalli agogo 3m to 3 se kuma kizo min office ke kaÉ—ai ki je in kin samo wanda zaku zauna sai kizo a miki 3 nayi time É—inki ya fara tafiya 30m kawai zan baki.

     Ta buÉ—e baki zatai magana ya shige É—akin dake haÉ—e da office É—in fiska a haÉ—e.

     Futowa tai rai aÉ“ace itakam yau ta shigesu Ma'u ba ta zo ba gashi time É—in baida yawa bare ta kirata awaya ta ce ta zo gashi ‘yan ajinsu babu wanda suke magana ba wanda tasan sunansa mace ko namiji afuska kawai tasan wasu....

    Don't forget to vote, comment and follow

    Tsayawa tai rai a tunkushe wani ɓarin na zuciyarta na faɗa mata rashin kyautawarsa inda ɗayan ɓarin ke ce mata ai dedai yayi in yana barin kowa sasakai bama tsari tana cikin tunane tunanen ne ta rasa madafa ta hangi wani ɗan ajinsu batasan sunansa ba sai dai tana ganinsa a ajin da sauri ta ƙarasa inda yake ta masa sallama.

     Ya É—ago ya kalle ta gami da yin murmushi kamin ya amsa tace.

     Sannu ko ta ce dan Allah tai mako za ka min mamaki ya kamashi tai mako kuma fahintar mamakin nasa tai ta ce kaga wallahi Malan Deen ne nai missing test É—insa so zaimin make up ya ce sai nazo da wanda za mu zauna tare bai san mu zauna mu biyu a office É—in inba damuwa ka temaka kazo mu zauna ok ba damuwa muje ko ok na gode ta faÉ—a.

     Yai gaba ta bi shi abaya Nasir na shiga Deen ya ce lafiya daiko tai saurin shigowa dan Namiji da sauri ya rigata shiga ta ce danman shi ne frnd É—in nawa dazai tsaya ni inyi test É—in.

     ÆŠan kallon Nasir É—in yai gami da taÉ“e baki kai ka zauna anan ya nuna masa kujerar da daga ita sai Æ™ofa ke kuma ki zauna anan ya nuna mata kujerar kusa da tebur É—insa tai saurin shigowa sosai dan zama mene haka kuma zaki barmin Æ™ofa a buÉ—e ya faÉ—a oh my goodness ta faÉ—a É—azu fa ya ce danme za ta rufe ta buÉ—e yanzu ya ce danme shikam mutumin nan ya cika matsala wani zubin.

     Da sauri ta koma dan rufewa wasu ‘yan mata suka shigo suna ta baza Æ™amshi anci ado kai ka ce wani gidan biki zasu gurin Dinner.

     Lafiya dai ko ya faÉ—a yana Æ™ara haÉ—e girar sama da Æ™asa daman sir za mu wuce ne mukaga Æ™ofar office É—inka a buÉ—e shi ne muka shigo dan gaidaka ok ya muku kyau zaku iya tafi suka tsaya sororo cikin fishi ya kuma maimaitawa nace zaku iya fita dasauri suka fice dan yadda yai maganar ya basu tsoro.

     DaÉ—i ya kamata har hatasan sanda tasa dariya ba Nasirma ya sa dariya ya É—an kallesu ya watsar zaki rufe ko kuwa cikin time É—inki kike tai saurin rufewa ta zo ta zauna.

     Question ya ba ta rubuce cikin paper É—in da za ta amsa ya ce inkin magana ko kika ci gaba da wannan dariyar zan yaga kinyi missing time É—inki ya daÉ—e da shiga sauranki 15m nan ta ci gaba da abin da take.

     Time na cika ya amshe ta miÆ™e za ta fice ya ce no ki tsaya ki tafi da abarki nan ya fara dubawa sosai yai mamakin yadda ta amsa baiyi zatom za ta iya haka ba tai Æ™oÆ™ari ahankula ya É—ago ya kalle ta ya taÉ“e baki not bad ya faÉ—a ya maka gami da shigar mata da marks É—inta computer ya ba ta ta fito ranta fes.

    Ko da suka fito Nasir tama godiya kamin ta ce in bazaka damu ba sunanka mana yai murmushi Nasir taɗan murmusa oh ashe ma Dad ne ashe shi ya sa kamin mutunci any way zan riƙe ni am Farida na gode fa Maisunan Dad ya ce no bakomi farida tai gaba ranta fes shi ma haka yau shikam sunyi magana da farida ashe tana da kirki ba kamar yadda suke ganinta a class mara mutunci ba.

     Tana tafe amota tana sakin murmushi yau ta ji sunanta bakin D kai satinnan tana caÉ“awa ta sami hotonsa yau kuma ya kira sunanta ai tana zuwa danja saida tai sadaka dan ita kaÉ—ai tasan farin cikin da ta ji tana san sauran bayain Allah suma suji daÉ—i yau É—innan.

     Ko agida kowa ya san yau Jaririn mom da Dad ana cikin farin ciki yadda Faruk yaita tsokanar ta shi dole saita É“ata rai anman abanza.

     Kwance take rungune da paper É—in da ya marker lokaci lokaci takan shishina ta dan shaÆ™ar kamshun dake jikinta ayayinda kunnuwanta ke tariyo mata da sautin sa alokacin da ya ce Farida ko tasan yanada sanyin murya muryarsa me daÉ—i ko lecture yake sedai lokacin da yake faÉ—in sunan se takejin kamar Muryar ta Æ™ara daÉ—i itaman tasan duk duniya babu wanda yafi D É—inta iya faÉ—in sunanta.

     Taso ina ma ace Ma'unta ta zo ta taya ta murna ta ji D yakira sunan wayyo me ya sa ma'u baki zo ba waya ta É—auka ta kirata ummansu ce ta É—aga seda suka gaisa ta ce tai bacci ko abata kinsan ba ta jin daÉ—i lah wallahi umma ban sani ba ba ta faÉ—an Allah ya Æ™ara sauÆ™i ta kashe wayar duk farin cikinta sai ya ragu Allah sarki Ma'una ko meke damunta gobe zan je dubata ba ta san sanda tai bacci ba rungune da paper É—in.

     Washe gari ta shirya ta faÉ—awa ummanta za ta duba ma'u umman ta ce ta mata sannu sosai ta ji tausayin Æ™awar tata dan yarta É—an faÉ—a taita mata sannu nan ta faÉ—a mata ai jiya D ya kira sunanta ma'u ta kalle ta cike da tausayi ta daure ta taya ta murna

    Da yayan Ma'uɗin ya shigo ne ta ba shi paper ɗin data ninke tasa aleda ta ce Yah Aminu pls faɗan sunan turaren nan ya amsa ya shinshina ya jima kamin ya faɗa mata tai godiya ta san intace yayunta su faɗa mata se sun isheta miƙezan wuce kar in makara se na kuma dawowa.

     Kai tsaye sahad ta wuce ta siyo turaren tabbas shi ne tai makaranta ita kaÉ—ai tasan me take shiryawa aranta..

    💞Don't forget to follow, Vote and comment💞

    A mota tabar turarenta tai aji dan tasan malami ya kusa shiga kasan tuwar Dr tijjani baya jimawa hakan ya sa ba ta wani jima a sch É—inba tai gida ranta cike da farin ciki.

     Duda tana jin yunwa kasa zuwa tai gurin abincin tai É—akinta na sama bayan ta cewa mum ta dawo turarenta ta É—auko se alakacin ma ta rasa ya zatayi ganin duk a rufe suke ma'u ta kira dan tambatarta nan ta faÉ—a mata sukai sallama.

     Roba ta samu ta haÉ—e turen da wanda ta siyo daÉ—i ya cikata inda Æ™amshin yabada wani sanyin Æ™amshi nai daÉ—i ji take kamar ita da shi ne suka haÉ—e suka zama mata da miji farin ciki ya cika ranta.

     Zaune take lokaci lokaci tana kallon gefen kujerar da tak zaune aranta tanata tunanin ko lafiya mutumin da ke zuwa ya zauna kusa da ita yau kwana uku baizo ba tasabs sosai da jinsa a gurin duda kuwa ba ta taÉ“a ido ta kalle shi ba bama za ta iya ganeshi ba in sun haÉ—u ahanya saidai ance mutun rahama ko yaya yake duk se takejin babu daÉ—i fatanta de Allah ya sa Æ™alau.

     Ya jima a bayanta yana Nazarinta yaÉ—an saki murmushi kamin ya tako ya Æ™araso dan ya fuskanci tana jimamin rashin mai zama kusa da ita ashe dai tana sane da zamansa a gurin dan basu taÉ“a magana ba ko sallamar sa ma dabadan yakanga bakinta na motsawa in yayi da ya ce ba ta amsawa.

     Sallama yai mata kamar koyaushe jakarta ta É—auke gami da matsawa bai damu da jin amsar ta ba yaja ya zauna taÉ—an kalleshe asaninsa tun randa ya fara zuwa gurin taÉ—an kalle shi tai nazarinsa bai Æ™ara ganin ta É—ago ido ta dube shi ba ta ce bakazo ba kwana biyu ta faÉ—a a hankula abubuwa suka min yawa ya ba ta amsa.

     Ba wanda ya kuma magana cikinsu can ta miÆ™e bayan kallon agogonta gami da saÉ“a jakarta da alamu gun takesan bari É—an É—agowa yai daga kallon wayar sa da yake ya ce bakya ganin dacewar cemin kin tafi.

     Ta É—an kalle shi ai ba gida naiba zan je salla ne in dawo inda gidai nai zsnce na tafi ok shi ke nan sunanki fa taÉ—an kalle shi kamin ta ce FATIHA ok kawai ya ce gami da miÆ™ewa ni bara inwuce ba ta ce komi ba tai hanyar masallaci.

     Shi kam yarasa meke damun yarinyar nan be san ta ba haka kawai yake jin tausayinta tsoronsa kar damuwa ta cutar da ita.

     Fatiha ce ta fito cikin shirin ta tsaf natafiya makaranta ta dubi ummanta daketa faman fifita wutar da tun É—azu take takesan ta kama sai dai da alamu icen É—anye ne umma ni zan tafi a'a Fatiha bazaki tsaya kici É—umamen bane eh umma na makara toshi ke nan Allah ya tsare akula insha Allah umma amana addu'a Allah ya bada sa'a amin umma ta faÉ—a tana shirin barin sashen nasu.

     A babban zaure ta ci karo da yayanta lah yah yaushe ka dawo jiya dadaddare ayya ban saniba fatan andawo lafiya Alhamdulillah ya faÉ—a badai har anfito ba eh wallahi ayya to tsaya in shiga in gaida umma se in rage miki hanya toyaya anman karka jima.

     Ababur É—insa ya É—auke ta suka tafi wanda tun da suka fara tafiya bawanda ya ce da wani ci kanka adaidai ATC ya tsaya ta sauka ya zaro duku huÉ—u ya miÆ™a mata ki ririta na san wancan sun Æ™are ko a'a yaya ka rage da saura a'a ki riÆ™e na san zan É—anjima banzoba in na koma to yaya na gode Allah ya saka da alkairi amin ya ce tai gaba inda zai kaita inda za ta hau motar zuwa sabuwar jami'a.

     Ya jima ya kallon Æ™anwar tasa ransa fal tausayinta kamin yaja mashin É—insa yai gaba cike da fatan inama yana da arziÆ™i ya farantawa Æ™anwar tasa sosai tun da ya taso yake tausayin rayuwarsa sai dai randa ummansa ta haifi Fatiha sai yaga shi cikin farin ciki mayake dan tun ranar aka fara kunsawa babyn abin rashin kyautawa har kawo yau.

     Sosai yau yai mamakin rashin ganinta a gurin bacin kullin a irin wannan lokacin yakan ganta to ko ta daina zama ya faÉ—a dana fi kowa jin daÉ—in hakan ya san damuwarta ta tafi ke nan dan baisan zaman da take tai tsit agun.

     Tun randa ya fara zuwa earth and environmental dan musu GSP idonsa ya faÉ—a kanta ada yai zaton shaÆ™atawa take saidai asannu yana nazarinta ya fahinci damuwa kawai ke kawota gurin.

     Yana shirin barin gurin yaji Sallamar ta ya amsa ba tare da ya kalle ta ba ba ta damu da hakan ba ta ce zan iya zama yaÉ—an matsa ga mamakin sa murtarta ya tsinkaya tana faÉ—in barka da safiyya.

     Barka dai Fatiha yau bakizo da wuri ba taÉ—an juyar da kai gami da faÉ—in na makara ne ok yayu kyau ya faÉ—a littattafin ta taÉ—auko ta hau dubawa yai mamaki baiyi zaton damuwar ta na barinta karatu ba.

     MiÆ™ewa tai ni bara inje za muyi test ok anman bakya ganin dacewar ki tambayeni sunana tai murmushi akaro na farko daya taÉ“a ganin tai murmushi ta ce ai baka ce in tambaya ba shi ma yai murmushi gami da faÉ—in shi ke nan yau na roÆ™a.

     Murmushi ta kumayi shi ke nan baka faÉ—an sunan ka ba shi ma murmusawa yau ya ce FAJARUDDEEN zaki iya kirana Fajaru ko Deen oh masha Allah ta ce zan riÆ™e insha Allah tabar gun ya bita da ido kawai kamin shi ma ya miÆ™e yabar gun.

    💞 Don't forget to vote, comment and follow 💞

    Deen ne zaune yana cin abinci Mamansa na kallonsa da alama jira take yagama cin abincn suyi magana Fatima ce ta fito riƙe da hijabi tana ƙoƙarin sawa take lah yaya baka tafi ba eh kawai ya ce ya cigaba da cin abincinsa ta ce umma ni na tafi to Fatima Allah ya bada sa'a Amin umma.

     Har takai bakin Æ™ofar É—akin ya ce Fatima inkin je kice ma Muhammad ya riÆ™en ajin zanzo anjima to yaya.

    Bayan ya sha ruwa ya matsar da kwanon ya ce yawwa umma naga kamar kina san muyi magana eh na ji kafe za ka makaranta ka je inka dawo ma tattauna kar yaran suyi ta jiranka a'a umma ba komi na san Muhammad zai kula dasu kamin inje to yayi kyau ta faÉ—a.

     Fajaru daman ba komi nake san mu tattaunawa ba face batun aurenka agaskiya na gaji da ganinka babu aure sa'oinka duk sunyi auren nan sun barka ada na ji karatu kake yanzu fa me kake eyyi.

     YaÉ—an sosa Æ™eya anman mama....karka cemin komi yanzufa ka duba makarantar nan taku ta mangariba tun kuna ÆŠalibai har kun zama ku ke tafi da ita jibi fa duk wanda kuke malinta da aurensu da yaransu anman mama kin mance duk sun girme min dan dai kawai munyi aji É—aya ne yimin shiru da nawa suka girmekan eyyi jibi fa Badamasi yaransa uku fa yanzu shi ma ai tare kukai wasa.

     Kai umma dan Allah dudu fa shekaru na bawa ashirin da takwas fa ni ban ga girman da naiba eyyi ah lallai ashirin da takwas in aÆ™auye ne ai ya aurar da É—iya to ai umma nan ba Æ™auye bane birni ne ki ci gaba damin addu'a insha Allah zan yi aure kamar yadda kike so karma kayi kaita jamun magana gurin mahaifinka shi ke nan ki yi haÆ™uri umma zan yi ni na tafi kar yaran suyi ta jirana.

     Fatima ce tafe tana ta zuba dan batasan makara sabida yau malam Nasiru keda duty duka zai mata ba ruwansa jitai an Æ™wala mata kira tai saurin jiyawa ganin Faiza ya sa ta faÉ—aÉ—a murmushin fuskar ta tana faÉ—in anti Faiza kema kin kusa makara bari kawai Fatima inata sauri kar malan ya rigani zuwa Fatima tai dariya baima fito ba nabar shi yana cin abinci.

     Faiza ta É—an saki murmushi ah kice yau zai zo eh zaizo ya ce min ince malam Muhammad ya jire ku kan ya zo daÉ—i ya ziyarci faizs ta É—anyi fari gami da murmusawa ba tare data ce komi ba itakan ta rasa meke damunta aduk ran Litinin take jin daÉ—in zuwa makaranta muje to kar mugun can ya dake inji Faiza uhun ku da baima bama ke nan inji Fatima sukai dariya baki É—aya gami da yin gaba.

     Zaune suke suna muraja'a ya shigo daÉ—i ya cika shi aduniya ba abin da ke masa daÉ—i kamar gari ya waye magariba tai yazama yana da lokacin zuwa makarantar dan ganin É—alibansa na gurfatu Aliyu bin Abi É—alib yana san yaran tun suna Æ™ana na yake koyar da su har kawo yau da duka girma aka fara aurar da wasun su.

     Suna ganinsa sukayi shiru dan gaidashi ya amsa cike da annashuwa kai baka ce shi ne wannan Deen É—in da baya dariya ba.

     Aisha ce ta ce malam yau ka makara yai murmushi Aisha sarkin mita ai saiki aika a É—auko bulala ki daken ta dabe fuska wa ai nayi kaÉ—an ah haba dai kinfa yi yawa tun da gashi ana min Æ™orafi.

     Ya dubu RuÆ™ayya ya ce ah su Rakiya ba magana ta turo baki dan batasan sunan tun tana yarinya in yaso tsokana sai ya ce Rakiya ta ce kai malan dan Allah idanta yai rau rau yai dariya ai na kusa dena faÉ—e ÆŠaha ya ce ai malan ko kadena faÉ—e mudai ba za mu dena ba ÆŠaha abokin faÉ—an RuÆ™ayya ne malan yai dariya nima ai ba yanzu ba ta watsawa ÆŠaha harara ‘yan mazan suka sa dariya.

     Fa'iza da tun da ya shigo ta É—an kalle shi gabanta ya faÉ—i ba ta kuma kallonsa ba ta rasa me ya sa kan ta ganshi saita tason ta ganshi tana É—ora idonta kansa gabanta zaita faÉ—uwa takanas take kwalliya ta rafi layinsu sai dai ko motar sa ta gani sai ta tajin gabanta na faÉ—uwa.

     Ya santa tun tana Æ™arama ba ta cika magana ba sai dai ba kamar yanzu ba bai tunanin komi ba zatonsa ko nata ‘yan matancin ya zo a haka.

     Aliyu ya duba ya ce Ali wai yaushe za mu sai banki ne Basira tai saurin rufe fuska dan tasan kan zancen bai ko kalle ta ba ya ce zan bawa Ali ya sayo in yaso sai duk me shi ya dinga sawa nima innazo zan dinga sa nawa suka ce to.

     Al'adar ajinne duk sanda aka sa ranar auren É—alibar ajin sukan sai banki dan tara kuÉ—in mata gudun mawa tun bai fara aiki ba har yakai ya fara in sun tara yakan shawar ce su me zasu siya ya cika asayo abawa amarya..

     Yanzu bikin Basira ya tashi shi ya sa yakesan su fara tarin tun da sai bayan azumi.

     Aimana ta dube shi ta ce malam wai kai yaushe za ka yi aure ne mu sai aita mana gori namu baban yaÆ™i aure yai dariya sai na gama aurar da ku inkuma kun gaji se ku min auren ai zainab tai saurin cewa munbana Faiza.

     Faiza tai saurin É—agowa daka kan littattafin da take dubawa ya ce kinci gidanku zainab maza ku É—auko littafin ku na muku Æ™ari ina da wancan ajin.

     Saida ya gama biya musu ya tabbatar sun iya ya sa suketa maimaitawa yau Babban aji.

     ðŸ’ž Don't forget to vote, comment and follow 💞

    Rubutawa

    FaÉ—ima Fayau

    Fajaruddeen 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.