Fajaruddeen (Kashi na 4)

    Saida ya gama biya musu ya tabbatar sun iya ya sa suketa maimaitawa yau Babban aji.

     Yana barin ajinsa ya wani haÉ—e rai kai baka ce shi ne yanzu yake ta faman dariya ba dan ya tsani babban aji yaran ko kaÉ—an basu da kunya ada suma yakan É—an musu wasa saidai ko ganin fuska sukai oho sune harda kawo masa letter tun lokacin ya bar sakar musu fuska dan yaga raini na san shiga tsakani.

     Suna ganinsa suka shiga tai tayinsu sai É—an magana da suke Æ™asa Æ™asa wadda duk ba ta wuce kan shigar sa ta yau ba dan kayan da ya sa sun amshe shi duda dai shiÉ—in ko wani kaya ya sa kai ka ce danshi akayi.

     Yana musu Æ™ari suna Æ™us Æ™us zahra tafe kinsan mai sadiyya se kin faÉ—a wallahi malam Fajar ya haÉ—u ke sai yau kika gani inji Badairiyya a'a kawai dai yau naÆ™ara gani kudai kubari ai duk makaranta albarka ina jin malan Nasiru ne kawai zai iya takara da shi a fagen kyau shi kuma ya sa mugunta aransa Kulsum ta ce to ba gwanda mugun ba yana dariya shifa wannan shashashun ajinsa kawai yakewa dariya.

     Kai ashe kema kin sani ai inna ganshi a ajinsa se inji kamar anya shi ne kuwa bari kawai ji nake kamar in koma ajin nasa inji zainab taÉ“ koro ki zai yi.

     Yana ganinsu duda baya jin me suke cewa sai dai yana jin Æ™us Æ™us ransa ya É“aci dan ya tsani yana Æ™ari ana magana ya miÆ™awa usama littafinsa da ya ara ya ce abin da wulaÆ™anci ina da abinyi na taso dan muku karatu tsabar wulaÆ™anci sai ku dinga surutu inkun san karatun ne bakwa so ai sai ku zauna agida ko ce muku akai banda abinyi ne to indai nine na dena shigowa ajin nan sai ku nemi wanda zaku raina.

     Mansura ta ce Allah ya isa wallahi banzaye kawai dan ita tana san karatun dan sosai take gane abin da yakeyi suka kuwa yo kanta da masifa yan maza suka shigar mata dan suma sunji haushi.

     Sabida haushi ma yana zuwa ya tashi ajin nasa yai gaba Faiza tai saurin tsai da shi tana faÉ—in takaddun baka amsa ba ya ce ok ba ni za ta hau duba jaka ya ce basshi gobe ki kaima ummamu ta ajiyemin in bana nan ta ce to tai gunsu Aimana da suke jiranta.

     Majalisar su ta da yai yajima baije gun ba yana zuwa suka hau masa mitar yai kuÉ—i ya manta dasu Mahmoud ya ce banda abinku ai ba mantawa ake da asali ba abubuwa ke yawa kuma ai kun rage zaman yawwa mutumina gane min hanya dai inji Fajar.

     Se wajen goma ya musu sallama Mahmud ma ya ce bari in gudu suka taso dan tafiya gida aiko suna barin gurin aka kafa fagen zaginsu wai dan sunga sun samu aiki shi ne suke wani shasshan Æ™amshi nidai nace uh mutun.

    Tun bawa ma'u motar nan kishiyoyin ummanta keta gulma dan sosai suke mamakin wani dalili ya sa Alhaji ya haƙura yabar motar bai mai da ba itadai umman ma'u daman can bamai san shiga hayaniya bace kullin tana sashenta sai lokaci lokaci ma suke ganinta.

     Tun jiya Farida ke takurawa Dad É—inta kan ya shirya zasuje duba ma'unta ko kaÉ—an baya san É“acin ran É—iyar tasa suka shirya su huÉ—u harda yaya faruk da momun ta suka tafi.

     Ankoyi sa'a Abban ma'u na gida bakinsa yaÆ™i rufuwa daÉ—i ya cika shi wai yau shi ne Alhaji Nasir Dala ya zo har gidansa mutumin da seka shekara kana san ganinsa bazaka ga ko Æ™urarsa ba.

    Gwanda ma shi sabida yana da kuÉ—i ba lefi ya samu darajar ganin sakatarensa shi ma dakyar sai gashi a gidansa a É“agas.

     Ma'u ta ji sauÆ™i tai mamakin ganin su farida ta ce yanzu aminiyar seda kika taso su Dad bacin nace miki gobe ma zanzo sch ta turo baki gami da hararar ta to saka su nan gaba innace muje guri suce no Æ™arya nake akai dariya baki É—aya.

     Ganin yadda mai gidan nasu yake ta girmama baÆ™in ma'u yaita basu mamaki dan sun san farida tana zuwa gidan saidai su basu damu da sanin ko ita É—in wace ba dan sanin makaranta guda suke da ita ma'u É—in.

    Sai isha suka bar gidan Abban ma'u sai ziba godiya yake kai baka ce shi ne ba.

     Yau basu jima azaune ba Deen ya dubi agogo Fatiha ni zan wuce inada abinyi to shi ke nan sai Allah ya sake haÉ—a mu amin ya ce yabar gun baisan ya makara dan karya bawa É—alibai Æ™ofar makara.

     Bai jima da barin gurin ba ta miÆ™e tai aji dan itama malamin su ya kusa zuwa batasan afara lecture tana waje dan malumman su na agric basu cika rufe class ba dan hana É—alibin da ya makara shiga.

     Farida ce zaune tana duba littattafin ta lokaci lokaci tana duban hanya kar ya zo ya shiga ya hanata shiga duda taga alamar baya nan dan ba ta ga motarsa a Department É—in tasu ba ko kaÉ—an ba ta cika san hayaniyar

     ðŸ’žDon't forget to vote, comment and follow 👫💞

    Ɗagowar da zatai idan ta kan motarsa da ke ƙoƙarin shigowa Department ɗin tasu ba shiri ta fito daga motar tai aji.

    Ajin ya cika sosai wani takai ci ya kamata sai yanzu ta tuna ba ta tsari guri ba yanzu dole in koma baya ke nan ta faÉ—a aranta to ya zakiyi yau dai kam bake ba ganin D É—inki sosai.

     Ji tai ance Farida ga guri muryar namiji ce jitai kamar tai halin nata ta share shi kamar karta kalli mai maganar tai baya É—an juyawa tai dan ganin mai maganar Nasir ta gani yai tsuru yana kallon ta ayayin da duk ‘yan ajin suka zuba musu ido jira kawai suke ta dizga Nasir É—in tai baya su sa dariya.

     Ga mamakin kowa zama tai harda Æ™arin na gode Nasir ko me sunan baba zance yai dariyar jin daÉ—i dan ya san da ta dizgashi tai baya yau ba Department É—in ba duk Faculty É—in an samu abinyi ya ce ah duk wanda kika zaÉ“a ok shi ke nan nazaÉ“i Dad Name sake É—in.

     Masu san gulma sai aka hau mamaki ashe ma har sunan sa ta sani .

     Anya kuwa zaizo inji musa ko kawai mu ware ne inji Nasir taÉ—an kalli agogonta gami da faÉ—in naganshi yana Faculty É—innan still time É—insa bai cika ba ok to mujira kawai Muktar yai saurin faÉ—e wai dan dai shi ma dole ace shiÉ—in abokin farida ne .

     Lokaci lokaci tana saka baki a hirar tasu hakan yaima Nasir daÉ—i ashe dai tanada mutunci tasan wanda ya mata alkairi ko kaÉ—an bai za ta zata iya riÆ™e sunansa da kaman ninta sa ba.

     Ko da aka tashi malan na fita ta fice Nasir yai saurin bin yanta saida ta kusa shiga mota ya tsaida ita ta tsaya ya ce Na gode taÉ—an kaÉ—a kai alamar godiyar me ya ce da kika zauna abin da sanda nace ki zauna É—in ba bankuma yi tunanin ko zaki zauna ko a'a ba tai É—an murmushi nice da godiya dan ko kaÉ—an abin da zaman baya yai murmushi to seda safe tai motarta.

     Tana jan motar abokansa suka Æ™araso anman wallahi Nasir kai munafiki ne ace kuna mutunci da Farida shi ne bamu taÉ“a sani ba yai dariya kunji ba baku taÉ“a sani bs inda da gaske ne muna mutuncin da ita ai da saikunfi kowa sani.

     Eh shi ya sa tasan sunanka yai murmushi kun mance a ajinmu take ne kun mance yawancin presentation ina cikin presenters kun mance ana faÉ—in suna anan ta san sunana ko kun taÉ“a ganin munyi magana da ita ne yauma tausaya mata nai naga kullin agaba take yau sai baya gabaki É—aya sun yaddadashi.

     Kai amman kam tausayinka ya kyauta ko ba komai in kuna gaisawa muma za mu saba da sannu inji musa suka saka dariya.

     Masallaci ta parker motar sai dai ba ruwa ta tarar hakan ya sa tai central mosque wato C monque anan Æ™ofar shiga ta ajiye motar tasai pure water gami da shiga masallacin.

     shi ma Deen yana fitowa bai wani bi ta masallacin Faculty ba yai C monque nan tsallake ya ajiye motarsa bayan inda white bus ke É—aukan É—alibai ya tsallaka dan shiga masallaci.

     Kamar ance ta É—aga idonta tana Æ™oÆ™arin tada motarta ta gangeshi suna magana da wani aranta ta ce ko me ya zo yi oho can ta ce bazai wuce salla ba ido kawai ta tsura masa ta ma kasa tada motar tana kallo suka Æ™ara gaisawa da mutumin ya tsallaka.

     Ga mamakinta baya ta ga ya dawo zuwa inda É—alibai ke zama dan jiran mota.

     Tayi zaton ko motarsa ta sami matsala ya zo hawa motar É—alibai tana cikin tunani aranta taga yaje gaban wata dake can gefe kusa da yara masu saida goro ta ta rafka tagumi harda tsugunnawa kishi ne ya kamata to ita É—in wace da har zai mata haka mene gamin sa da ita bacin tasan ita kaÉ—ai ce tasa nai dariya nace eyye wato ke É—aya ma.

     Shiko anasa É“angaren har ya wuce idanunsa suka kai kan Fatiha data rafka uban tagumi da alama ta jima a gurin bama tasan motoci sunzo ba sunata cika.

     Ya jima a tsugunne agabanta ransa na raya masa abubuwa da dama kan abin da ke damunsa sai dai kwata kwata yaka sa gano ko mene.

     Ganin irin É—alibansa da suka sanshi suna gai da shi ya sa ya ce ma É—aya cikin masu goron É—an taÉ“a min ita aÉ—an razane ta kalle shi ganin shi ne yasata É—an murmushi lah yah Fajar kaine jin yaya bakin ta ya sa É—alibai masu san gulma sikai zaton ko Æ™anwar sa ce.

     Ina zuwa ya ce da ita motarsa ya É—auko ya ce da ita shigo ko tsintar kanta tai da kasa ce masa a'a kawai ta shiga duda kuwa ba al'adar ta bace shiga motar wasu.

     Farida na kallon su gabaki É—aya jikinta yai sanyi ta rasa wane irin jarabar so takewa mutumin nan hawaye kawai ke bin fuskarta.

     Ta rasa me ya sa zucuyarta ke sansa in dan kyansa ne za ta iya cewa Fatahu yafishi kyau in kuÉ—i ne daman tuni tasan fatahu ya kere shi in illimine tun kan ta shigo buk Fatahu yai PHD É—insa in Æ™uruciya ce ma tasan Fatahu bai girmi D ba anman ta rasa me ya sa ko sau guda ita ba ta taÉ“a sansa ba sai wanda baima san tanai ba.

     Ada tanada É—an hope É—in ko zai so ta sai dai yau se take jin kamar bazai so ta ba ji take kamar tafi kowa rashin sa'a aduniya.

     Kuka ta saka zuciya ta why me ya sa zakimin haka me ya sa bakiyi shawara dani ba.

     Ta jima tana kukanta kamin ta fito ta wanke fuskarta ta É—an shafa mai gami da shafa hoda da kwalli dan ko kaÉ—an batasan tadawa iyayan ta hankali dan tasan in ta je gida da alamun tayi kuka duk gidansu hankalin su bazai kwanta ba barima Abbanta zai shiga damuwa sosai.

     Motar ta taja tabar makarantar.

    💞 Don't forget to vote, comment and follow 💞

    Rubutawa

    FaÉ—ima Fayau

    Fajaruddeen

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.