Fajaruddeen (Kashi na 5)

    Shi kuwa Deen yana ku kaiwa Bank road ya parker motar sa Fatiha tai saurin kallonsa ya ce Fatiha wai mai ke damunki karfa kisa ma kanki damuwa kina ‘yar ƙaramarki ciwon zuciya ya kamaki wallahi kallonsa kawai take tana tunanin da ace ya san meke damunta da baice haka ba ko kaɗan ba ta jin damuwa za ta barta sai dai ko inta mutu dan ita ta gama yadda damuwa da ita aka haifeta.

    Ki faɗan meke damunki ko nima inada abin da zan iya miki wajen cire miki damuwar nan wallahi bana san ganinki cikinta wallahi ina jinki kamar Fatima ƙanwata pls ki faɗan na miki alƙawarin duk girman da muwarki zan yi iya yi na wajen share miki ita.

    Kamin ya ankara hawaye ya fara wanke mata fuska haba Fatiha mene haka kuma kukan ne ya kwace mata kawai ta hau rera abinta sai da tai mai isarta sa'annan ya miƙa mata hankici fari ƙal yana ƙamshi ta amsa ta ajiye shi a gefe tasa hijabinta ta goge basai na ɓata maka shi ba da hawaye na marar anfani Na gode.

    Anman dan Allah kayi haƙuri abar maganar abin da ke damuna dan inna faɗa maka baƙin ciki ne kawai zai ishe ni inna baka labari dan ko yaushe na tuna ina jin babu daɗi ko na faɗa ma ba abin da za ka iya ƙaddara ta ce mutun baya iya sauya ƙaddara.

    Bai ce mata komi ba ya ce ina ce unguwar ku a'a a tsohuwar jami'a zan sauka ok kawai gami da jan motar sa yai gaba.

    Kasan tuwar tayi yanma tun a makaranta ba ta samu zuwa gida ba sai mangariba hankalin ta duk ya tashi tsoronta ɗaya Allah ya sa Babansu bai kawo shawagi ba dan tasan a kowanne lokaci zai iya zuwa tun da ya jima bai zo ba.

    Za mu iya cewa Addu'ar ta ba ta amsu ba dan tana zuwa ƙofar gidansu ta ganshi yana alwala hankalinta ya tashe tai kamar ta wuce sai ji tai ance ke daga ina haka.

    Tai saurin zubewa agun tana faɗin lab Baba ashe ka dawo kin ci gidanku ina tabayar ki kina tambaya ta kaga shaƙiyyar yarinya daga ina kike cikin rawar murya take faɗin Baba daga makaranta nake.

    Yanzu dan tsabar rashin mutunci na hanaki zuwa makarantar nan shi ne bakiji ba ko wato ban isa da keba to naga kin kuma zuwa makarantar sai na saɓa miki wallahi ki barmu muji da masifar da ke cikin mu basai kin kwaso mana wata ba ta karatun boko wallahi baba afusace ya kawo mata duka kaga mara mutunci.

    Tada iƙama da akai ya sa ya ce ki je ciki zanso yanzu wallahi sai naci mutuncin ki keda uwar taki shegiyar yarin da baƙin hali.

    Miƙewa tai tana share hawaye tai cikin gidan nasu itakam dabadan yadda duk ‘yaran ummanta babu mai kama da Babansu ba sai ita da ta ce ita ɗin ba ɗiyar sa bace da ace ita ce ‘yar fari da ta ce ba aure suka haifeta daga baya aka ɗaura aure sai dai daga ita sai auta ta rasa mai ta tsone ma mahaifin nasu.

    Koda ta shiga ummanta na kwasar tuwo a tsakar gida dan nanne madafar tasu tana ganinta tana kuka ta ce Fatiha badai kin haɗu da babanku ba kai ta ɗaga alamar eh gaban umman ya faɗi me ya sa kika bari kuka haɗu tai shiru sai yawaye dake bin fuskarta sai ji sukai ance to muna fuka ko ta ɓuya sai na ganta shi ke nan jeki ki yi Sallah ta ce da Fatiha batare da ta ko kalli Malam ɗinba.

    Ransa ya ɓaci ya hau masifa yana zaginta Fatiha na ji ta toshe kunnenta duda haka tana jiyo zagin da Abban nata kema ummanta hawaye kawai ke bin kuncinta da tausayin umman nata.

    Allah ya temake ta kwana uku Baban nasu yai ko tsakar gida ba ta iya fitowa dan in ya ganta yanzu zai hau mata masifa kullin tana ɗaki tana ji in ƙaninta ko yayanta sun shigo suna hira da shi harda dariya itakam tana kunshe a ɗaki fatan ta ya tafi da wuri ko ta samu kar tayi missing exam ɗinta.

    Yau tana da paper tanata Addu'a Allah ya sa ya tafi aikuwa tana fitowa taga ba mashin ɗinsa ta ji daɗi ta shirya tama ummanta sallama umman ta ce zaki tafi eh umma to ki kula ta zaro naira ɗari ta ba ta ga wannan ki ci abinci na san kinada kuɗin mota ko ta ce eh umma zaima ishen inci abinci tun da jarabawa muke har mu gama wanda su Yaya suka ban bazai ƙare ba.

    Kin tabbata eh umma to shi ke nan Allah ya bada abin da akaje kema ta ce Amin.

    Sai da ta je soro ta goge hawayenta tasan tun da umma ba ta ce ta tsaya taci abinci ba Baba ya kwashe abin da suke da shi ya tafi da shi shi bazai kawo ba sai dai ya zo ya tada musu da hankali ya kuma kwashe abincin su ya tafi da shi itakam da badan ba da ta ce haƙurin ummanta yai yawa.

    Shiko Deen kullin sai ya zo baya ganinta a gurin kanshi duk ya cushe ko dai dan ya tambaye ta meke damunta ta sauya guri.

    Bai gajiya ba yauma ya zo yai sa'a tana gurin ya mata sallama da fara'a ta amsa suka gaisa yake tambayar ta me ya sa ta dena zuwa tai shiru kamin can ta ce banji daɗi bane yanda tayi ya tabbatar masa da ƙarya take abinka da phsycologiest sai dai bai ce mata komi ba kawai ya ci gaba da abin da yake basu daɗe a gurin ba ko wannensu ya miƙe dan ita tana da exam shi kuwa yan da abinyi a Faculty ɗinsu.

    Tun daga wannan lokacin Fatiha ta ƙara sakewa da Fajar har hira suke sosai yake jin daɗin yadda take hira da shi har labarin yayyenta da ummanta take ba shi shi ma yakan ba ta labarin ƙanwarsa da mamansa ayadda ya fahince ta mutunce mai daɗin zama hankali ga kwanya daga labarin ta ya fahinci sosai ‘yan uwanta da ummanta ke san ta duda ya fahinci su ɗin talakawa ne sai dai ƙwaƙwalwar sa kan kulle ya rasa mene damuwar yarin yar nan.

    Koda ta koma gida ummanta ta gani zaune tayi tagumi tai saurin ƙarasawa tana tambayarta me ya faru umman tai saurin aga kanta sama aƙoƙarinta na kar Fatihan ta ga hawayenta.

    Jeki ki kai jakarki ɗaki ba komi kai kawai ta gyaɗa dan batasan takurawa umman nata tai ɗakinta.

    Seda ta fito ta kalli gun girkinsu babu alamar anyi girki hakan ya sa ta leƙa gun umman ba ta ciki motsinta ta ji a abayi ɗakinta ta koma ta ɗauko hijabinta gami da kuɗin makarantar ta.

    Robar da suke saida mai ta ɗauka babu komi ciki bacin ko rabi ba'a siya ba jiya wato Baba ya kwashe ya tafi da shi hawaye ne ya zo mata kawai tai waje.

    Kuɗin ta irga sauran Ɗari tara gashi yayanta tasan bazaizo ba sai nanda wata guda koma fi tun da ya san sun kusa gama exam yakuma kawo musu abincin da zai isheshu da man da zasu dunga ɗan juyawa kan ya zo sauran dik karatu sike sai buga buga suma duk ba'a kano suke ba daga Yaya Bashir sai ƙaninta sune kawai agidan.

    Kantin Bala ta wuce ta sayi waken suya rabi da kwata sai mai da magi ta ce ya ba ta bashin Barkono da kwai guda biyu tun da suka fara exam ta ajiye sayar da awarar da take saidai taga alamar inba yi taiba ba inda zasu sami abinci.

    Kasantuwar gidan nasu gidan yawa ya sa ko ɓarinsu ba ta shiga ba dan tasan icema basu da shi bare ashana dan tasan har su Abban ya kwashe tai ɓarin wan babansu anan ta gyara waken ta ce umma salima ta soya mata man kan takai markaɗe.

    Bata jima ba ta dawo kan ka ce me ta dafa awararta umma salima ta ba ta ice da murhu da kasu su Basira suka tayata tai waje dasu acan Bakin layinsu take suyar.

    Umma salima ta bita da kallon tausayi itakam da ace suna da arziƙi da ta kula da su Fatiha sedai suma neman nakaiwa bakin salati suke wataran ma se malam ya fita yake samo naci ɗin.

    Tana tausayin yarinya ace yarinya budurwa ‘yar jami'a tana faman suyar awarar sayarwa abakin loko wannan abu da yawa yake.

    Tasa kaskon farko yayanta Bashir ya zo wucewa a keke ya tsaya Fatiha ba yaya ya ce ki dena awarar nan ba sai kun gama exam tai murmushi kawai ɗan tsaya ka kaiwa umma wannan ka ce taci kan inzo in Ibrahim ya dawo ka ce yazo.

    Kinga ki je gida ki huta na san baki jima da dawowa ba na ji kina cewa gobe exam ɗin safe gareki kawo ni in suya dan ya fuskanci me take nifi da cewa ya kaima umma taci se a lokacin ya tuna Abba fa ya zo wato ya kwashe duk abincin gidan kamar yadda ya saba.

    Saida ta ɗaura na umman ta miƙe ya zauna in Ibrahim ɗin ya zo kice ya zo ya amsheni to yaya na gode tai gida ya bita da kallon tausayi.

    Tana shiga umma tahau tambayarta inata ta shiga umma naje sayo kayan awara ne to naga bamu da ice sai naje gidan Baba Habu nayi yanzu Yaya Bashir na can ya soyawa ya ce inzo inyi karatun exam ga wannan kici ta miƙa mata.

    Tausayin yaran nata ya kama ta ace namiji saurayi na suyar awara abakin titi aranta ta ce Allah ka duba mana afili ta ce a ina kika samu kuɗin ta ce kuɗin makaranta tane zan zare su in yaso se a juya ribar to shi ke nan Allah ya sa albarka ta ce amin tai ɗaki.

    Koda Ibrahim ya kawo mata kuɗin tabashi yakaiwa Bala kuɗinsa ya sayo wasu kayan yi ɗin ta ajiye ɗari biyun zuwanta makaranta na gobe ta ba shi ta ce yasaro rake ya dinga sedawa yana bawa umma ribar ya ce to yayanta Bashir ta ba shi ɗari ya ce shi bazai karɓa ba ta miƙawa Ibrahim gashi ka ƙara jarin raken.

    💞 Don't forget to vote, comment and follow💞

    Fatiha Yau sukai last Semester paper ɗinsu zasu tafi hutu duk sai take jin babu daɗi dan ta saba sosai da shi ji take dama baza'a hutun ba ta jima a zaune tana jiransa dan masa sallama ba ta ankara ba tai nisa a tunani anya fatiha kima kanki adalci kin shaƙu da wani daban bacin kinsan ke ɗin wace kinsan da yana sanin ke wace zai guje ki to wallahi ki farka ji tai an taɓa ta tai saurin kallon inda ta ji alamun mutum ɗin.

     Murmushi ta sakar masa au ashe yaya ne inata jiranka mu yau za muyi hutu ayya na ɗanyi wani abu ne zo mu wuce kawai nima gida zani batai musu ba ta bishi.

     Suna tafe suna ‘yar fira wanda duk ta exam ɗin da Fatiha sukai ce yau tana tafe tana lissafin abin da za ta ci yana biye mata aransa yana jin daɗin yadda afagen karatu take ture damuwar ta.

     Ta Ɓangaren farida kuwa ji take kamar ta jawo baya dan ko kaɗan batasan gobe ta zo dansu gobe zasu gama exam itakam inda tasan intazo makaranta cikin hutu za ta dinga ganin D babu abin da zai hanata zuwa dan kam tasan tabbas zuciyarta za ta iya bugawa na rashin ganin D tasan ganinsa da take yana rage mata damuwa.

     Itakam za ta so ko sau ɗaya ne D ya ce mata Farida ina sanki koda da wasa ne itakam za ta fi kowa jin daɗi.

     Wayar ta ce tai ƙara kamar yadda ta za ta fatahu ne tsaki taja gami da katse kiran sosai take jin haushinsa ta rasa me ya sa shi baya ganewa bacin ya san ko kaɗan ba ta sansa.

     Kiranne ya kuma shigowa ta ɗaga daga kunnenta tana jin ajiyar zuciyarsa ya hau magana tamai banza kuka ya sa mata Farida dan Allah kimin magana ko zuciya ta tasamu sukuni ɗan tausayinsa ta ji ta ce kaga malam abin da shagwaɓa in ka saba yi agida ni nan bazan ɗauka ba ni wallahi abin da ragon namiji ta kashe wayar ta.

     Data ta kunna tai profile ɗin D na Tweeter tweet ɗinshi take karantawa lokaci lokaci tana sakin murmushi sosai magan ganun nasa ke burgeshi aranta tana faɗin word of wisdom.

     Shi kuwa ta ɓangaren Fatahu tagumi yai ya rasa mai zaiwa farida ta gane ko kaɗan shi ɗin bafa rago bane san ta kawai ke mai da shi haka iska ya Furzar gami da faɗin Farida ki temaka ki fahince ni.

     Faiza ce zaune tana kallon hotonsu da sukai da malam Fajaru lokacin walimarsu ta izu talatin tun tana ƙaryata zuciyar ta kan ba san Malam take ba harta aminta tabbas sansa take so kuma mai zafi ita kam me ya sa zuciyarta za ta mata haka duk masu san ta ace sai wanda yake musu kallon ‘ya’ya za ta so.

     Anya naima kaina adalci abayyane ta ce a'a gami da goge hawayenta ta mai da hoton ma'ajiyarsa ta fito dan yin alwala agogo ta kalla 20:50 Am aranta ta ce so masifa ne shi tasan yanacan yana baccin sa ita tana nan tana fama da tunane tunane ko yaushe dare yai oho.

     Nafilfilu ta fara tana kaiwa Allah kukanta ita addu'a takema Allah ya yaye mata wannan azababbiyar soyayya dan tasan itakam har abada bazata iya faɗawa malam Fajar tana sansa ba.

     Kasantuwar abubuwa sun masa yawa ya sa kwata kwata ya aje zuwa makarantar mangariba dan daman yana haka se abubuwa sun masa sauƙi ya koma yakan sa a kula masa da ajinsa.

     Abin duniya duk ya ishi Faiza na rashin ganinsa batasan sansa yai nisa a ranta ba sai a kwana biyun nan da take rashin ganinsa ji take yau kamar in antashi tai tsuntsuwa tai gidansu Malam yadda zuciyarta ke azalzalar ta daurewa tai kawai dan kar ‘yan ajinsu su harbo girginta dan tasansu zainab za ta iya dena mata magana sabida yayarta na masifar san Malam.

     Washe gari ta shirya tsaf cikin atamfarta black blue mai ratsin ja tai kyau sosai mayafinta ma ja daman ita mai kyau ce bare tai kwalliya.

     Umma ni zani gidansu Fatima in tambayi malam batun admission ɗina kwana biyu baizo ba to karki daɗe Allah ya sa adace amin umma.

     Yana gida suna hira da ummansa ta shiga yana ganinta ya sake fuska umma tafe a'a yau Faiza ce agidan namu tai dariya kawai suka gaisa.

    Sun ɗan taɓa hira take faɗa masa abin da ya kawota ya ce Faiza sarkin san karatu ba'a fara fidda admission ɗinba tukun tai godiya ni zan tafi umma ta ce mutuniyar taki batanan taimur mushi gami da ficewa umma ta bita da kallo cike da yima ɗanta sha'awarta a matsayin mata.

     Umma nima bari inje inada ɗan wasu abubuwan to Fajar Allah ya temaka karka mance maganin Babanku ya ƙare shinkafa ma sauran kaɗan to umma insha Allah zan tawo da maganin inyaso shinkafar in an albashi na siyo shi ke nan Allah yayi albarka ya ce amin yai waje.

     Tana fita tajin gina da bangon soron gidan zuciyar ta na bugawa da sauri ta dafe ƙirji tana mai da numfashi kai ka ce wacce tai gudu idanunta a rufe ta ji muryarshi na Faɗin Faiza lafiya daiko tai saurin buɗe ido daf da ita yake har tana jin ƙamshin turarensa tai saurin cewa ƙirji na ke ciwo yaɗan kalle ta ayya sannu zo muje in sauke ki a'a ka bar shi zan iya zuwa gida ya maka mata harara zaki wuce ko kuwa tai saurin yin gaba ya bita a baya.

     Basu da nisa sosai ya sauketa a ƙofar gida ta ce Malam na gode ya ce ki je asibiti kinji ko ta ce to malam ta fice yaja motarsa tabi motar da kallon tai cikin gida.

     Kai tsaye gurin abokin sa ya wuce dan azahirin gaskiya baida kuɗi bama zasu isa ya sayi maganin Baban ba gashi wata be wani nisa ba dan wannan watan yai hidimar ƙannensa da yawa duk albashin anan yatafi

     Gurin Bashir yaje nan yake tambayarsa ko zai samu kamin ƙarshen wata ba musu ya ba shi yaji daɗi sosai zai tafi Bashir ya ce inada shawara mai zai hana ko shagone ka buɗe wa ƙananan ka maza inya so tun da kakan dawo da wuri saika dinga zama kaima ribar za ta rage maka wasu abubuwan hidimar ka tafi ƙarfin albashinka murmushi yasaki dan yaji daɗin shawarar na gode bashir hakan zan yi insha Allah zuwa alhashi zan tunanin da me za mu fara tun da banda kuɗin katon jari Bashir yaji daɗin amsar shawararsa sukai sallama Fajar ya wuce inda zai sayo maganin.

     Ita ko Faiza a farfajiyar gidan tai zamanta bakin bishiyar mangwaronsu ta tura ƙaninta ya faɗawa umma ta dawo lokaci lokaci tana sakin murmushi gami da lumshe ido ayayin da hancinta ke dawo mata da ƙamshinsa da ta ji daɗi na ziyar tarta wai yau ita ce amotar malar tasaki murmushin jin daɗi.

     Jitai kamar ana kallonta ta ɗan buɗe idonta a hankali inda ta Ɗorasu kan Umar wanda yana zuba mata faman murmushi itama murmushin ta saki lah yah umar yaushe kazo Ɗazunnan na dawo ta waro ido ɗazu yaya shi ne baka zauna ka huta ba bari kawai duk kewar ku ce ta ishen ina san in zo ingaisa da umma.

     Ta turo baki gami da juya wa yai saurin matsawa kusa da ita mene kuma ba umma kawai ka damu da ita ah haba ɗanfa sakayawa nai ni danke nazo tasaki murmushi harfa na ji daɗi wallahi bari inje mugaisa da umman inzo musha hira da ƙanwata taɓ aini bazan hira da kaiba ta faɗa tana haɗe rai yai saurin riƙo hannunta cikin rikicewa yake faɗin haba ƙanwar sabida me mena miki kuma yadda yayi yasata fashewa da dariya to wasa nake.

     Ya miƙe yai ciki shi ma yana dariya tabishi da kallo yah faruk ke nan causin ɗinta ne ɗa gurin yayan mamanta duk cikin causins ɗinta maza shi kaɗai take iya sakewa suyi wasa da dariya may be ko dan tun tana yarinya ya sabar mata da kula da ita gami da ji da ita.

    ****

     Fatiha ce zaune tana bin number ɗin da ya ba ta da kallo yau watansu guda da hutu har kusa komawa ba ta kira ba bacin shida kansa ya ba ta number ɗin da ta ce ta mance da wayarta ranar hutu.

     Fitowa tai tsakar gida ummanta na tura wutar ta ɗora abinci ta ce lah umma wutar mutuwa tai ban sani ba da kin kirani umman tai murmushi a'a naga wutar naci awaje ne wani gun zaki ne bafa ki gama abincin ba.

     Ta sosa kai daman dan Allah umma Ɗari zaki ba ni zan kira wani ɗan makarantar mu tun kwanaki yaban number ɗin ban samu nakira ba umma tai murmushi ki ɗauka cikin kuɗin mancan karki daɗe ta bita da kallo cike da tausayi da fatan abin da take tunani ya tabbata.

     Koda ta dawo ta jima tana kallon number ɗin dan kamin ta danna kira wayar ta jima taja ringing har ta katse ba'aɗauka ba sau uku tana kira ba'a ɗauka ba sai da ta ji babu daɗi ta miƙe za ta fito kira ya shigo wayar.

     Kamar karta ɗauka yadda ta ji gabanta ba faɗuwa daurewa tai ta ɗauka sallama ta fara batare da ta ta ji mai zai ce ba shi ma yai mata suka amsa atare jin hakan ya basu dariya baki ɗaya kamin ya ce ban gane me magana ba.

     Daurewa tai ta ce Yah Fajarudden Fatiha ce ƙanwarka ta BUk atare ta faɗa masa ya saki murmushi dan ada bai gane wace Fatihar ba dan shi azahirin gaskiya yama mance da wata Fatiha sai da ta ce ƙanwar ka ta buk ya gane.

     Allah sarki fatiha ya hutu ya faɗa ta ce Alhamdulillah fatan an rage damuwa eh ta ce gami da murmusawa sun ɗan taɓa hira kaɗan kamin suyi sallama saving ɗin number yai gami da ajiye wayar ya ciga da abin da yake.

     Ita kuma rungume wayar tai tana murmushi wani farin ciki na ratsa ta.

     Nace ko na mene kuma oho.

    💞Thank You for reading😘💞

    Rubutawa

    Faɗima Fayau

    Fajaruddeen

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.