Fajaruddeen (Kashi na 7)

    Koda mahaifin Fatiha ya dawo daga masallaci ɗakin matarsa ya shige wato mahaifiyarsu Fatihan kamar yadda ya saba yahau bincike nan ya tattara duk abin da yake buƙata tun daga kan taliya sauran man da ke cikin jarkar ya juye a leda ya ɗaure cikin huhu kamin ya fito yana cika yama batsewa cikin ɗaga murya yake kwalawa ummansu Fatihan kira.

     Da sauri ta fito daga madafa lafiya dai malam cikin fishi yake faɗin tsabar wulaƙanci shi ne kuka tsiri boye kaya ta daure ta ce wane irin ɓoye wa shi ke nan muke da shi abin da ƙarya ya faɗa na san Bashir Buhu guda yake ajiye miki gami da galan ɗin mai.

     Cikin fusata ta ce to be ajiye ba da me kake so yaji yanzu yai aure matarsa harda ciki ga kuɗin makarantar ƙananan sa yaja tsaki wannan ai duk haƙƙinsa ne inji wa ya ce haƙƙinsa ne kai yake kanka cikin fusata ya ce to gorantamin bana iya ci da ku nidai ba goranta ma nayi ba gaskiya ce.

     Tsaki yaja ya shiga ya ɗauko kayan da ya haɗa zai fice tasha gabansa me kake nufi bafa mu da komi kai baka kawo ba shi ne za ka kwashe mana namu tureta yai yana faɗin daɗin abun hake kika kawo ba kema ɗana ne yakawo kuma ki faɗa masa in ya zo lalle ya kawon dubu goma zan biyawa Salima kuɗin makaranta.

     Me wallahi bazai kawo ba indai ni na haifeshi to bazai kawo ba yadda yai ta gwannati haka itama tayi in kuma kaga bazatai ba seka ɗauki himmar biya mata anman ba shi ba, ya juyo zai haita da masifa tai shigewar ta bayi yai kwafa gami da ficewa rai a ɓace.

     Fatiha na jinsu tausayin kanta da ‘yan uwanta dana ummanta ya kamata ta share hawaye gami da fitowa ta ɗau wakenta dan kai markaɗe.

     Koda ta kammala komi na awarar Ibrahim ne ya ɗibar mata kaya suka fice zuwa inda take suyar.

     Tafe suke suna shida abokinsa cikin wata tsaleliyar mota kallo ɗaya za ka musu kasan tabbas kuɗi da hutu yagama zauna musu kai motar kawai inka kalla se kaso ganin na ciki.

     Anman wallahi Faruk kai ɗan Iska ne tsabar wulaƙanci nazo garinku ka rasa inda za ka kawoni yawon shaƙatawa sai nai jibi dan Allah yadda motar nan ke faɗawa kwazazzabai Faruk ya sa dariya kaga malam karka kuma iskantani kaifa ka ce in kaika inda baka taɓa zuwa ba agarin kano, Msttt kamis yaja tsaki ni maidani gida na haƙuri.

    What gida fa ka ce wallahi ba inda zan koma se naje inda nai niyya inkaga za ka koma in ajiyeka ka hau mashin ni mashin haba Allah ya kiyaye inji kamin to seka shirya zuwa inda nai niyya tun da dai mota tawa ce daɗin abin nima inada tawa.

     Kujerar da yake zaune ya ɗan tura baya ya kwanta yahau gami da saka ear phone a kunne ya lumshe ido dan ya san halin faruk in ya biye masa zai iya sa masa damuwa.

     Birkin da Faruk ɗin yaja ne yai mugun tsoratar da kamis yai saurin ɗayowa hankali tashe dan zatonsa ko sun taka ko kuma sun kusa taka wani ne sedai ganin gaban motar da suke ciki wayam ba kowa ya baima kamis haushi Haba faruk wannan wane irin ɗaukar alhaki ne kaji yadda gabana ya faɗi.

     Faruk bai ba shi amsa ba ya ce kalli can kamis ya kalla sai dai shi bega abin kallo ba mene kuma zan gani ka kalla mana me ka gani me kuwa na gani banda tarin yara pls ka dai kuma kallo wai ko dai kai gamo ne faruk kamis ya tambaya ni ban ga komi ba sai yara da mai suyar kosai.

     Yawwa pls kuma kallonta yaɗan kalle ta kamin ya ce mene kuma pls kata tama kama da me talla sosai ma gata nan ma tana abinta mtss faruk yaja tsaki gami da buɗe murfin motar zai fice kamis yai saurin jawo shi me kake nufi?, Ai malam ka jira ni kawai in sayo mana kosan can mafi jin daɗin shaƙatawar kamis ya ce kaime za ka ci abin kan hanya lalle yau da ruwa da ƙanƙara mutumin da a gida ma ba kowa ke girki ya ci ba Faruk yai murmushi gami da kwace rigar sa jirani pls.

     Ba kamar yadda ya za ta ba, awara ce ba ƙosai ba yadda ya ganta da ya matso kusa mamakinsa sai ya ninku fiye da na baya anya kuwa idon sa gaskiya yake faɗa masa wannan yarinyar ko kaɗan batai kalar wahala ba ya daurewa mamakinsa ya ce aban awara.

     Ibrahim dake gefenta ya ce ta nawa dubu ya miƙa masa ta ɗari biyu ok ya ce ya hau zuba masa ba haka yaso ba yaɗanso yaji muryarta ko zatai masa kama da ta ‘yan talla ita kuwa bama tasan yanai ba suyarta kawai take.

     Ibrahim na miƙa masa ya juya zai tafi tai saurin cewa baka ji ba ya ɗan jiyo da saurin jin muryar yai ta doki kunnensa bema tsaya tan tance damuryar yan talla ko yan ƙauye take kama ba sabida yadda yaji daɗin muryar.

     ta ce ka manta baka karɓi canjin ka ba yai ɗan murmushi no bar shi kawai yai gaba. Umar yayanta da ke gefe yai saurin amsar canjin ya bi shi dashi.

     Malam bakaji ba Faruk ya tsaya hannunsa umar ya kamo ya danƙa masa canjinsa gami da faɗin ba bara take ba in kana san kyautata mata za ka iya sayan abin da take saidawa zaifi wannan kuma za ka iya bawa mabarata kamar Faruk yai magana ya fasa ok tom na gode zam kiyaye ya juya yai gun motarsa.

     Yana shiga kamis ya haushi da jaraba kan ya tsaidashi shidai yamai banza gami da juya motar dan bema jin zai iya zuwa inda yai niyya.

     Kamis ya ce mene haka kuma ina za ka kaimu Faruk yaja tsaki pls karka dameni kadai san bazan sace kaba ko ya faɗa cikin zafin rai kamis ya taɓe baki iyi haƙuri gami da komawa ya kwanta a jikin kujerar da yake yabar faruk cike da tunani kala kala a zuciyarsa....

     💞Thanks for reading 😍

     💞 Don't forget to vote, comment, share and follow 💞😍

     Koda suka koma gida Faruk ko takan awarar baibi ba ya fice daga motar bare abi takan rufe motar malam mene haka kana nufin ni zan rufe ma ƙorar faruk ya watsa masa harara kabarta a buɗe to wannan fa ya nuna masa awarar kai na siyowa ya faɗa yana ƙara harararsa gami da barin gun Kamis yabishi da kallo yana murmushin mugunta.

     Hannu ya sa ya ɗauko awarar gami da rufe motar yai cikin gida kai tsaye kitchen ya nufa ya zuba a faranti ransa fal farin ciki dan ya san zai rama takaicin da faruk ya gama ba shi ɗazu.

     Yana fitowa ya ci karo da Bilkisu ƙanwar Faruk a'a yah me kuma zakai da awara bari kedai Faruk ya siyo tasa dariya taɓ kaima dai yaya ina Yaya faruk ina awara yai murmushi ai wannan ta dabance towo aci lpy tai ɓangaren ummansu.

     Yana shiga ya tadda faruk yai rigin gine yana duba wayarsa ya ba shi duka abaya yaiko saurin ɗagowa mene haka banfa san iskanci ya faɗa Kamis ya haɗe rai kafasan bakyau anobazzaranci ka sayo abu kaku kuma bar shi.

     Nace kai na siyowa a'a in baka ci kabaiwa almajirai ya koma ya kwanta.

     Ah to na gode ke nan me awarar ma zan iya neman aurenta ke nan ko faruk ya ce duk yadda ka gani kai anman na gode kamin zaɓi fa me kyau kaga malam kamin shiru fa.

    Kamis ya daure ya ɗauki awara guda ya gutsira ya ce kai anman wannan awara da daɗi take ga kyau a ido kamar me seda ta nifa nayi sa'a waya ganni ran bikina da me awarar nan kai mun fa dace ko Faruk takai ci ya ishi faruk ganin yai masa banza ya sa kamis taɓo shi ka mance baka faɗan sunan matar tawa ba.

     A zuciye Faruk ya ɗago ya kawowa kamis naushi kamis ya kauce yana dariya haushi ya kuma kama faruk cikin fishi ya ce agidan ubanwa ta zama matarka kamis ya nuna masa awarar hannunsa tinda na iya cin wannan ka kuma iya sayo min yana nufin nine mijinta.

    Bani abata inji faruk kamis ya ce ta ƙarfi ne azo a kwata faruk ya miƙe yayin da kamis yai waje yana dariya yako bishi.

     Dakyar faruk ya amso awarar yazauna yana ci seda ya ci wajen shiga sannan kamis yako sheƙe da dariya yana faɗin woo ni gaskiya fa nai ƙoƙari koda yake kaine kai ƙoƙari waya san ma da wane irin kwano, ruwa gami da mai akai ledar ma fa harwa ƙarni ƙarni da wari wari take tuni amai ya tawowa faruk ya miƙe yai toilet kamis yaita dariya ko banza ya rama.

     ******

    Farida ce zaune tana duba tweet da retweet ɗin malam Fajar sosai take jin daɗin abin da take karantawa dan ayanzu ba ta da wani abin ɗebe kewa agunta fiye da karanta tweet ɗin sa da kallon hotonsa.

     Kiran Fatahu ne ya shigo wayarta wani ƙululun takaici ya ziyarci zuciyarta yana ɗaya daga abin da ke ba ta haushi da Fatahu baya taɓa tashi kiranta se tana cikin nishaɗin duba saƙon malam ba shi da aike se katse mata jin daɗi.

     Har kiran ya katse ba ta ɗauka ba ganin yaƙi dena kira ne ya sa taja tsaki cikin dakushasshiyar murya me cike da takaici tai sallama.

     Ya amsa cike da farin cikin samun nasarar yau anɗaga kiransa gimbiyata abar sona gami da burin zuciyata.....bata bari ya ƙarasa ba ta ce pls bana jin daɗi ne ka kira wataran tuni ya rikice me ya same ki nifa ince na ji muryar abar ƙaunar tawa wani iri ashe ba ta jin daɗi ne.

     Taja ɗan ƙaramin tsaki mara sauti yawwa sai anjima ban cika san jin hayaniya ba ok Allah ya ƙara afuwa sai nazo dubiya bai jira me za ta ce ba ya kashe dan ya san cewa zatai kar ya zo bacin ba abin da idanunsa ke san gani face fuskar faridansa sedai baida hujjar zuwa dan baya san ɓata mata rai dan ya fuskanci zuwansa ke ɓata mata rai.

     Ita ko tsaki taja tsabar wulaƙanci ni zai kashewa waya ta kuma jan tsaki kawai ta cigaba da dube dubenta a waya.

     Shiko fatahu ya kashe wayar ya kira abokinsa dake aiki a airport pls Nura jirgi da zaije kano nake so ok bari zan duba in gani ya ce ya kashe wayar gami da shiga toilet dan yin wanka.

     Tsaf ya kintsa yai ɓangaren iyayansa kai tsaye falon momy ɗinsa ya nufa dan ya san Abbansu ya fice yadda taganshi cikin walwala yasata farin ciki saida suka ɗan taɓa fira kamin ya faɗa mata yana san zuwa kano ta masa fatan alkairi gami da kashedin karya jima sannan ya fice.

     Bala driver ne ya ɗaukeshi zuwa airport yana zuwa Nura ya ba shi komi na tafiya ya masa godiya gami da alkairi mai yawa yai jirgi.

    Koda ya sauka a kano gidan kakanninsa ya nufa saida ya sake wanka sannan ya fice zuwa unguwar su Farida ko tsayawa hira da kakannin nasa bai ba dan hankalinsa yayi kan Faridansa.

    Tana zaune inda tai salla tana cin abinci yayanta ya shigo jaririyar Dady kinfayi baƙo ta ɓata fuska waye shi yaɗan saki murmushi yah fatahu ne ta waro ido wane fatahun mubasshir ya watsa mata harara ke fa baki cika M fatahu bako kara tai murmushi ai gani nan ɗazu mukai waya yana Abuja banyi zatonsa ba yanzu yai ɗan murmushi to dai yana jiranki.

     Abaya ta saka milki mai adon golden batai wata kwalliya ba ta naɗa mayafinta tai falon baƙi ga mamakinta baya ciki gashi ba ta fito da waya bare ta ji yana ina.

     Farfajiyar gidan ta fito ɗan nesa kaɗan ta hangeshi zaune bakin bishiyar mangwaro ta ƙarasa tana murmushi tun da ta tawo yake kallon ta ransa fal da farin ciki dan rabon da yaga murmushin Farida tun kan ya ce yana santa.

     Ta ƙaraso gami da gaidashi cike da mamaki ya amsa wai yaushi Farida ta gaida bai gama mamakinba ya tsincin muryarta na faɗin yanzu yah haka ake zuwa dubiya me makon ka shigo seka sa patient wahala.

     Cike da farin ya ce kai wani da wahalar da patient na san patient ɗin ba ta san motsa jiki temako nayi ko ta ɗan motsa nan suka shiga hira ran fatahu fal farin ciki ji yake kamar addu'arsa ce ta amsu ayayin da ita kuwa farida daurewa kawai take ganin yadda yai takakkiya ya taso duk dan kawai ya dubata.

     Tausayin sa takeji ganin tayi duk iya rashin mutun cin da za ta iya anman ya shanye gani take inta bi shi a hankula zaifi fahintar ta ya janye ƙudurinsa na santa.

    Thanks for reading 😍

    💞 Don't forget to vote, comment and follow 💞

    Rubutawa

    Faɗima Fayau

    Fajaruddeen

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.