Fajaruddeen (Kashi na 8)

    Sun ɗan jima suna hira farida duk a takure take daurewa kawai take can ta ce Yah jikin fa patient ya motsa a rikice ya ce sannu meke damunku ta ɗan ya mutsa fuska ba komi to shi ke nan Allah ya ƙara afuwa bari in gudu se munyi waya ta daure ta ce ba za ka shiga ku gaisa da mami ba bari se na kuma zuwa.

     Ta É“ata rai so kake ta ce na kwace mata É—a ace kazo bazaka shiga ku gaisa ba gaskiya inbaka shiga ba za mu É“ata a'a to ba za ai haka ba muje tai gaba ya bita abaya ji yake kamar ya ce ta zo su jera sedai yana tsoron kar aljanun masifar ta su motsa ta butse masa.

     Sosai mami ta ji daÉ—in ganinsu tare fatan ta Allah ya sa Fatahun yayi nasarar shawo kan faridan.

     ****

    Shi kuwa Faruk tun daga wannan ranar kullin kome yake duk yadda aiki ya run ca É“e masa se ya yakice yaje inda Fatiha ke saida awarar ta ya siyo.

     Tun yana siyan ta É—ari biyu ya koma É—ari uku yanzu kullin ta É—ari biyar yake siya duda kuwa ko da wasa baya koda É—an É—annawa burin sa kawai ya É—ora idanunsa kan yarinyar duda kuwa magana ko kaÉ—an ba ta haÉ—a in ka É—auke ta nawa tashi se anjima mun gode shi ma se in Ibrahim me zubawa baya nan.

     Sosai tsarin yarinyar yake birgeshi sana'arta kawai take gashi da wuya kazo gun ka tadda maza da sunan cin awara sedai ta zuba maka ka tafi da ita sa'annan da wuya kazo babu wani Æ™aninta ko wanta a gurin azaune.

     Tun yana Æ™aryata kansa da maganar kamis har ya fara jin tabbas kamis gaskiya ya ke faÉ—a masa sedai yaka sa yadda anya kuwa ta yaya kamar shi zuciyarsa za ta so wata yarinya yarinyar ma wai me talla a hanya anya kuwa to anman me ya sa nake kasa samun sukuni in idanuna basu ganta ba ya tambayi kansa.

     Wayarsa ya É—auka ya kira kamis bugu biyu ya É—auka a'a mutumin yadai kira da sassafe haka Faruk ya ce matsalata dakai gajen haÆ™uri inkayi shiru baka tambaya bama ai zan faÉ—a maka to shi ke nan ina jin ka.

     Daman maganar yarinyar nan zanma kamis yai saurin cewa me awara faruk yaja tsaki Fatiha sunanta malam kamis ya sa dariya lalle an tafi dakai wato har sunanta ka samo tsaki faruk yai ni abin da shiririta wallahi.

     To na ji na dena shiririta me kake san faÉ—an tambayarka zan ina jin ka pls da gaske san yarinyar nan nake kuwa kamis ya sa dariya lallai naka wasa ne wallahi kaga ni ba iskanci nace kamin ba kawai kaban amsa.

     Sorry sir inji kamis ya faÉ—a cikin dariya kaga in bazaka faÉ—an amsata ba shike nan cikin sauri kamis ya ce gaskiya ban sani ba ko san ta kake anman ka jira zuwa anjima zan zo kanon se muyi maganar in kuma ban samu zuwan ba zan kuma kiran ka ok se mun haÉ—u faruk ya kashe wayar gami da miÆ™ewa dan zuwa ya kintsa.

    ******

    Tafe take cikin nutsuwa tai kyau sosai kallo ɗaya za ka mata kasan tana cikin nishaɗi sanye take da doguwar riga abaya baƙa mai adon duwatsu ja sai mayafin rigar da ta naɗa akanta Faiza ke nan ta fito ne zuwa gidansu malam fajar dan duba ƙanwarsa Fatima kuma ƙawarta.

     Kamar ko yaushe da faÉ—uwar gaba ta Æ™arasa cikin gidan da ummansu Fatiman ta fara cin karo a tsakar gida tana wanki har Æ™as ta durÆ™usa ta gaida ta gami da mata ya me jiki da fara'a umman ta amsa ai me jiki ma ta ji sauÆ™i ta ma fita ayya.

     Shiru yaÉ—an ratsa kamin Faiza ta ce umma kawo wankin in tayaki umma tai murmushi a'a yarnan ki bar shi ki je É—akin Æ™awar taki ki jirata na san tana hanya ba nisa taiba a'a gaskiya umma ki kawo in taya ki kinga indai aiki kike san tayani to ga kwanukan nan wanke min farin ciki ya kama faiza tai É—akin Fatima ta É—auko zani ta É—aura saman rigarta ta hau wanke wanke.

     Sama sama suke fira da umman wanda duk dai kan karatune sosai umma kesan yarimya dan akwai hankali tanaiwa Fajaru sha'awarta matsayin mata dan tasan zai ji daÉ—in aurenta sedai ganin shi baya tunanin haka kuma tana tunanin ko yarinyar nada wanda take so ya sa take barin komai cikin ranta.

     Fa'iza na wanke wanken ne Abbansu fajar ya shigo a'a yau su Faiza ne agidan tai murmushi ta gaidashi aiki ake haka ne eh to Allah yayi albarka ta amsa amin umma ta cika da mamaki yadda taga sun gaisa faram faram da Abban su Fajar tai mamaki sosai dan sanin da tai masa tun bayan abin da ya sameshi na biyu ko yaransa bai damu da shiga sabgarsu ba tai mamakin har sunan yarinyar ma ya sani.

     Se ta ji tabbas yarinyar nan ta kuma kwanta mata anman zatai Æ™oÆ™arin tambayarta inta gane ba ta da wanda take so itakam za ta sa fajar ya nemi aurenta in anyi sa'a sun dedai ta itakam zatai farin ciki dan ta gaji da ganinsa ba aure da uzirin da yake ba ta mara kan gado.

     ******

    Duk yadda farida takai ga É“oye damuwarta ta gaja duk ta rame hankalim iyayanta duk ya tashi musanman mahaifinta da Allah ya É—ora masa santa.

     Mubasshir ne ya shigo É—akin nata dan sanar mata da kiran Dad sedai yadda yaganta yasashi ruÉ—ewa yai sauri Æ™arasawa jikinta zafi rau alamun zazzaÉ“i se rawar É—ari take ba shiri yai waje ya faÉ—awa Dad da gudu Dad É—in yai É—akin Faridan hankalinsa ya tashi sosai mubasshir ya sa ya kira likita yadda Dad ya tada hankalinsa ko mami ba ta damu haka ba.

     Koda likita ya zo ya dubata ya ba ta magani a falo yake faÉ—awa su Dad ai jininta ya hau sai malaria kuma hankalin Dad ya tashi da jin yarinya kamar Faridan sanace jininta ne yahau itakam meke damunta.

     Abakin gadonta Dad ya zauna yana shafa kanta tausayinta duk ya cika masa zuciya ji yake kamar ya sa kuka gani yake duk lefinsa ne.

     Koda ta farka kan dad É—inta ta fara É—ora idanunta tausayinsa ya kamata tasan dad É—inta na santa ta ji sauÆ™i bakamar É—azu ba nan dad yasata agaba yana tambayarta damuwar me tasa aranta haka tai ta ce masa ita ba ta sa komi aranta ba seda ya ba ta abinci taci suka É—anyi hira kamin ya fice zuwa nasa É“angaren.

     Yana shiga kukan da yake É“oyewa ya kwace masa akullin baya jin sukuni in baiyi kukan nan ba sedai yau duda yanayinsa zuciyarsa ba ta dena masa É—acin takaici da dana sani ba damuwarsa ba ta Æ™ara Æ™aruwa ba seda yaga farin cikin faridansa ya fara yin Æ™aura tun alokacin damuwarsa ta fi ta da sedai tayau tafi ta koyaushe.

     Farida yake gani abaya yaÉ—anji sanyi sedai baisan kuskurensa ya shafeta.

     Mami ce ta shigo É—akin danjin Alhaji shiru yadda ta ganshi ya É—aga mata hankali tasan lokaci lokaci yakan keÉ“e yayi kuka sedai baya bari ta ganshi sedai fa yau kamar damuwarsa tafi ta kullin.

     Da hanzari ta Æ™arasa sedai me makon ya dena kuka kamar yadda ya saba in yaganta sedai yau kamar an tinzirashi.

     DaÆ™yar ta samu yai shiru haba Dadyn Farida yanzu in farida ta zo taganka ahaka yakake jin za ta ji dan Allah ka daure ka mance da abin da ya faru dan Allah.

     Haba Bilkisu taya kike gani zan mance bacin na san yana rubuce a littafina haka ne anman ai Allah gafururrahimu ne anman baya yafe haƙƙin wani kema kinsani hakane anman ya san yadda kayi nadama.

     Ni tsoro na kar abin da nayi ya juya kan yarana ina tsoron ko shike bibiyar Farida bama shi bane Allah ba ya zalunci baya kama wani da lefin wani ka ci gaba da neman yariyar sa su kuma karka kaza wajen musu sadaka tun da....se kuma tai shiru ka tashi ka je kayi wanka ta miÆ™e za ta shiga toilet É—in.

     Hannunta ya ruÆ™o ta jiyo ya ce na gode Bilkisu na gode Allah da besa nayi kuskure biyu ba kuskuren rabuwa da ke alokacin da idona ya rufe na gode da haÆ™urin da kikai dani ta murmusa karkaji komi har abada ni mesanka ce ya saketa ta shigo toilet É—inta.

     Tana shiga ta share kwallar da ta tawo mata dan mikin da ya daÉ—e a zuciyarta takejin kamar ya warke ya taso ji take kamar tasa ihu sedai tana san kwanciyar hankalin mijinta dole ta shanye damuwarta ta fito tana murmushi oga ruwa ya kammala ya shiga ita kuma tai nata É—akin.

     Ni kam na fito cike da tunanin ko mene suke kokawa akai oho

    💞 Don't forget to vote, comment and follow 💞

     Wajan biyu na rana kamis ya iso kano saida ya ci abinci sa'anan suka fara tattauna maganar da suka fara É—azu a waya.

     Faruk ne ya fara magana da faÉ—in ple kamis ka faÉ—an meke damun zuciyata game da Fatiha na kasa na kasa ganewa shin san ta nake ko kuwa, dariya sosai kamis ya sa cikin fushi fatuk ke faÉ—in kaga malam abin da iskanci dan kawai na tambaye ka bayana nufin na zama shasha ba da za ka tisa ni aga kana faman min dariya.

     Cikin dariya mai Æ™ular da tai kamis ke magana ai kai É—in ne dole ama dariya ace kaida zuciyarka baka sam me take ciki ba ina kuma gani da ba'a jiki na take ba.

     Mtsss faruk yaja tsaki gami da miÆ™ewa zai bar É—akin kamis yai saurin kamo hannunsa haba nawan da wasa nake ai kai kasan hakina sai slow zauna mu tattauna ya fara Æ™oÆ™arin kwace hannunsa kamis ya marairai ce haba nawankayi haÆ™uri mana kazauna in faÉ—a maka me na fahinta.

     Fuska a haÉ—e faruk ya koma ya zauna yayin da kamis ya fara da azahirin gaskiya faruk bana jin san yarinyar nan kake faruk ya É—ago cike da fara'a haba koda na ji nisan ba san ta nake ba wallahi shiru ya É—an ratsa kamin faruk ya É—ago ya dubi kamis to anman faÉ—an meke damuna game da ita da kullin nake san ganinta da san jin muryarta.

     Fakar idon faruk kamis yai yaÉ—anyi murmushi dan ya san yanayin dariya abu zai zama rigima.

    Eh to nima gaskiya abin da meke damun zuciyar ka da ita ba ina ganin kai za ka fi kai za ka fini sani cikin fushi faruk ke faÉ—in inda na sani ai da bazan kiraka neman shawara ba.

     Kasanme inji kamis duk alamu sun nuna zuciyarka ta kamu da san ta cikin fushi faruk ke faÉ—in Allah ya kiyaye ta yaya ma hakan za ta yiwu eh shi ya sa nace aÉ—azun nace gaskiya abin da meke damun burnin zuciyar ka ba sabida ita soyayya ba ruwanta da asali masoyi baya kyamar masoyinsa sai dai kai kana kyamar ta tun da bazaka iya cin abin ta ba ni abin da meke damunka ba dole ka yadda abin dai ba gaskiya kai za ka zauna ka gano da kanka in yaso sai mu gano mafita ya miÆ™e zai bar É—akin.

     Har yakai bakin Æ™ofa ya dawo kasan me kamar yadda na faÉ—a É—azun ina jin a jikina kamar kuma yadda alamu ya nuna san ta kake sedai ego É—inka ya hanaka fahinta bai bi ta cewar faruk ba yai ficewarsa yayin da faruk É—in ya bi shi da mugun kallo cike da takaicin cewar da yai wai san ta mai awarar nan yake.

    *******

    Umman Fajar ce zaune suna hira da mai gidanta cikin dabara ta bijiro masa da abin da ke ranta Abban fatima ta faɗa murya ƙasa ƙasa a nutse ya kalle ta na'am umman fajar cikin nutsuwa take faɗin daman maganar Deeni ce nan da nan ya sauya fuska kardai kice wannan zsncen zaki kuma min ba shi bane saidai zai iya shafar sa to indai ba shi bane ina jinki.

     Eh to daman gani nake yaron nan ya girma ya kusa talatin da biyu ka duba ka gani duk suna da yara shi ne nake ganin ko za ka sa baki ya daure yayi aure ina ganin zaifi jin Maganarka tinda ni bai É—auki maganata da mahimmanci ba.

    Cikin fushi da faɗa yake faɗin ba nace miki ki dena sani cikin harkar yaran nan ba inyaga zai yi aure yayi in ma bazaiba ni babu ruwa na ya miƙe zai fice.

     To shi ke nan na ji zan yi iyayi na har ya yadda yayi auren kasan baida inda zai zauna ka ba shi izini koda iya É—akinsa na yanzu ne se ya zauna kafin Allah ya hore masa inma kinaso ni sai in dawo É—akinki ya haÉ—a da nawa É—akin kawai asani ciki ne bana so yai waje tai saurin cewa dan Allah ka dawo mu Æ™arasa wallahi bazan saka ka ciki ba.

     Dawowa yai ya zauna ita kuma ta É—ora da daman na yanke wata shawara ne na san baida wata budurwa shi ne nake neman shawarar ka kan ina san ya auri yarin yar nan É—alibarsa fauziyya matsayin ka na uba nakesan ji daga gareka inka amimce.

     Indai yarinyar ta amince ai ba komai nima na yaba da tarbiyyar ta shi ke nan ta ce eh ya tashi ya fice yai É—akin sa ransa a tunkushe shikadai ya san meke damunsa alwala yai yayi nafila gami da roÆ™on Allah inda alkairi a abin da da Salima kesan haÉ—awa Allah ya tabbatar.

     ******

    Duk yadda faruk yakai ga daurewa zuciyarsa kan bazai kuma zuwa gurin yarinyar nan mai awara ba sai dai hakan ya ci tura kusan kullin sai yaje yake samun sukuni sai ya dawo takaici da haushin kansa duk ya cika masa rai.

     Yau kusan kwana uku ke nan yana zaryar zuwa gurin saidai babu ita babu dalilinta hankalinsa duk ya kasa kwanciya.

     Sannu a hankali ya yardarma zuciyar sa tabbas tabbas ta kamu da san yarinyar nan so mai tsanani sai dai rashin ganin ta gurin sana'ar ta shi yafi komai É—aga masa hankali gashi ko ‘yan matasan da ke zama gurin baya ganinsu bare ya tambaye su.

     Kamis ya kira awaya kuka riris yake masa wai yai gamo sosai kamis yai dariya wallahi faruk kanada matsala na rasa yaushe za ka girma wataran in ina ma kallon gentle kawi se ka dawo sha..... Yai saurin rufe bakinsa dan ya san halin faruk da fushi ya sauya maganar da faÉ—in dan baka ganin ta ai ba yana nufin kayi gamo bane malam ka je area É—in ka tambayi address É—in gidansu cike da farin ciki sukai sallama faruk ya kashe wayar.

    💞 Don't forget to vote, comment and follow 💞

    Rubutawa

    FaÉ—ima Fayau

    Fajaruddeen

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.