Ticker

6/recent/ticker-posts

Farajuddeen (Kashi na 1)

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI

Zaune take tana bin ɗaliban dake kaikawo a tsallaken da take nan Faculty of earth and environmental kamar yadda ya za ta kamar ko yaushe tana gurin ya faɗa aransa ya rasa shikam mai take a gurin kullim ya zo wucewa yakan ganta a gurin a zaune.

 Ya jima a gefenta yana Nazarinta wanda ita ko kaɗanma ba ta san yanai ba daurewa yai ya matsa dab da inda take gami da mata sallama tai nisa sosai cikin tunani hakan ya sa in dutse yaji sallamar sa to itama ta ji agogonsa yaɗan duba ganin zai makara ya sa shi barin wajen.

 Kai tsaye Department ɗin su ya nufa yana parker motarsa ɗaliban da ke karatun cikin runfar da malumma ke ajiye mota suka hau gaidashi amsawa kawai yake ba tare da ya ko juya ya kalli masu gaisuwar ba.

 Muktar ne ya dubi Nasir gami da faɗin Allah mutumin can girman kansa yai yawa tsaki Na jir yaja bari kawai ai wallahi shi ya sa nake dagewa in fito da first class ko nima na ƙaro wulaƙanci jibi fa yadda mata ke shisshige masa bari kawai yana wani ja musu class inji Nasir.

 Ummi da tun da suka fara magana ba ta tofa ba sai yanzu ta ce ai wallahi bazaku gane ba D. Ko cleaner ne se mata sunso shi guy ɗin fa ya gaji da haɗuwa towa kaga mu ci gaba da karatunmu tai dariya yami da buɗe shafin gaba.

 Deen ke nan matashi wanda bai fice shekara ashirin da takwas zuwa talatin ba malami ne a tsangayar karantar kimiyar tunanin ɗan adam wato phsycology.

 FAJARUDDEEN wanda ɗalibai musan man ‘yan matan da yake birgewa ke kira D abokai ke kiransa da Deen.

 ‘Yan mata da dama sun jima da kauwa da san Malaminsu wanda wasu da dama kuma yake cikin jadawalin mazan da ke birgesu burin da dama daga cikinsu ace yau wata hulɗa ta haɗa su da D. Ko yaya take kuwa.

 Da yawa sukan kai kansu gurinsu wasunsu da sunan soyayya wasunsu ma da ɓatanci dan zatonsu in sukai haka zai iya amsar buƙatarsu sai dai ina ko fuska basa gani yake fatattakarsu.

 Tun da ya shigo harabar Department ɗin yake amsar gaisuwa fuskar nan ɗaure babu annuri atattare da ita kai ka ce baisan yadda ake dariya ba.

Zainab ta dubi Bilkisu ta ce kinsan Allah na rasa me ya sa guy ɗin can ke burgeni duda kuwa ba malamin mu bane Bilkisu ta ce ni kinsan me na rasa me ya sa ko kaɗan nake jin ba burgeni yake ba zainab ta zaro ido towo to me yake miki wallahi ji nake kaman sansa nake tsaki zainab taja.

 Abin da hauka Kefa Bilki kina da matsala kin mance nanda wata uku za mu miƙa ki ɗakin mijinki tai dariya shi ne sai an ɗoran hauka eh mana ina kuwa kika ga hankali ni kinga mubar zancen haka Nidai na san ina sansa inma ba so bane to tsaki zainab taja shaiɗan ke ɗawainiya dake wallahi.

 Tun da ya tada salla yaji buƙa ƙofar office ɗin hakan ya sa yaɗan hanzarta ya idar gami da cewa su shigo.

 Ƙamshin turaren su da yaɗan bugi hancinsa ya sa shi ɗagowa yaɗan kallesu gami da kauda kai ya ci gaba da addu'ar sa.

 Sai da ya shafa ya miƙe yana mai ninke sallaya ganin haka ya sa Farida saurin taɗin barka da yanma sir barka dai ya ce ya faɗa yana mai ƙoƙarin zama gami da sake haɗe girar sama data ƙasa.

 Lafiya dai me ya kawo ku cikin rawar murya farida ta fara magana ganin haka ya sa ma'u faɗin daman sir kayi test ne tayi missing to sai akai yaya mene nawa a rashin yin test ɗinta tai saurin cewa daman ba ta da lafiya ne ina medical report ya faɗa aɗan ƙagare alamar ya ƙosa subar masa office.

 Bamu zo da shi ba ta faɗa ok randa kuka zo da shi kwa dawo suka kalli juna ma'u ta ce ok sir pls ka bamu number ɗinka sabida in munkawo muji ko kana nan ba'a cika samuka ba anan kallon da ya watso mata yasata ta kasa ƙarashe zancen nata.

 Kuje ku sami level coordinator ɗinku inya kawon letter zan faɗawa Captain ɗinku koma mene zatayi as make up ok sir mun gode suka faɗa gami da yin waje rai aɓace ba haka suka so ba sunso samun wayar tasa.

 Suna fita idanun farida suka kawo ruwa Ma'u tai saurin goge mata haba farida mene haka kuma dan Allah ma'u ki duben ku faɗan me na rasa da kallo ban ishi mutumin nanba.

 Ki dubi yanda maza ke sona ni inanan ina famada san maso wani ki dubi yadda ko anan sch ɗin ma kaza masu aji ke kawo ƙoƙon bararsu gunni Farida kan inso su Ma'u ce taja ta zuwa jikin motarta tasa ciki itama ta zagaya ta shiga gami da rufe motarta.

 Baki rasa komi ba Farida ina tabbatar miki wallahi ƙarya yake ya ce baki burgeshi ba ina tabbatar miki babu wani namiji dazai ganki ya ce baki masa ba ina tabbatar miki yana sanki kawai girman kansa ke hanashi nunawa.

 Ahab kinji ko ba sona yake da gaske ba ke nan kin mance waye Fatahu anman haka ya sauke girman kansa ya ce yana sona yake kuma bina kullin kan insoshi pls ma'u ki faɗan yaya zan yi D. Ya fahinci ina sansa wallahi da gaske nake ko yau aɗaura mana aure ma'u pls ki faɗan mezan yi in cire masa wancan girman kan dake damunsa.

 Kinga yanzu banan ba kisa Dad ya ma level coordinator ɗin magaha ki je ki yi test in tukun kamin mu samo mafita ok kawai ta ce gamu da ƙara goge hawayenta taja motar suka bar Sch ɗin.

Rubutawa

Faɗima Fayau

Fajaruddeen

Post a Comment

0 Comments