Fassarar Mafarkin Malami Yana Dukan Dalibi

    TAMBAYA (45)

    Uncle, mafarki na yi kana duka na

    AMSA

    Ranar Asabar (7/10/2023 wanda ya yi daidai da 23-03-1445 ) da rana wata daliba ta a islamiyya yar babban aji, ta rubutomin tambaya kamar haka: "Uncle, mafarki na yi kana duka na. Bissalam"

    Ina shiga ajin sai na ganta a saman benchi sunata surutu, wanda daman malamai sun hana a dinga hawa saman benchi, dayake ta yi wannan laifin a lokacin sai kawai na yi mata bulala 5

    Nace mata to kin ga fassarar mafarkinki

    Lamarin ya bawa wasu mamaki wasu kuma abin yabasu dariya

    Fassarar mafarki abune mai fadi musamman idan muka duba cewar fassarar mafarki yanada asali. Annabi Yusuf AS ya kasance yana fassarar mafarki wanda ya taba fassarawa abokan zaman gidan yari mafarkin da sukayi. Akwai manyan malamai masana fassarar mafarki amman wanda aka fi kafa hujja da shi shi ne; Imam Ibn Seerin

    Imam Muhammad Ibn Seerin al-Basri ya kasance shahararren malamin abin kafa hujja, an haife shi ne a shekara ta 33 bayan hijira (653AD), ya kasance Tabi'i sannan kuma ya yi karatu a wajen Anas Bin Malik, Al-Hassan Bin Abi Al-Hassan AI-Basri, Ibn 'Aown, AI-Fudhayl Bin 'Iyadh, da sauransu. Ya samu yabon kyakkyawan hali daga Imam Malik, Hasanul Basri, Ibn Zuhair, Musa Ibn Mughira, Hafsat Ibn Seerin (Wato kanwarsa). Allah ya karbi rayuwarsa yana shekaru 76, a garin Basra wato shekara ta 110 bayan hijira (729 A. D. )

    Da akwai wata rana wani mutum ya zo wajen Imam Ibn Seerin ya tambayeshi fassarar mafarki. ya ce ranar nan na fasa farin kwai dafaffe, amman a maimakon na ga kwan duwa saidai na sake ganin wani farin, idan nasake fasawa saina sake ganin farin, sai Iman Ibn Seerin ya ce kai kada ka kawowa mutane wasa, je ka ba kayi ba, sai mutumin ya ce na yi, sai Imam Ibn Seerin ya ce a je a kirawo yan sanda a zo a tafi da shi domin kuwa barawon likkafani ne a kabari, idan an binne mamata kaine kake haƙa kabarin ka cire likkafanin ka je ka siyar

    Sai mutumin ya ce haka ne. Amman na tuba, kuma ba zan kara sata ba

    Watarana Imam Ibn Seerin yana zaune da hantsi a makaranta sai wani ya zo ya ce ala gafarta malam na yi mafarkin ana kiran sallah, sai Ibn Seerin ya ce masa albishirinka bana zakayi aikin hajji, can da la'asar kuma wani ya zo shi ma ya ce na yi mafarkin ana kiran sallah sai ya ce masa za ka yi sata a yanke maka hannu. Kuma duk hakan ta samesu a wannan shekarar. Daliban Ibn Seerin suka tambayeshi ya akai haka. Sai ya ce ai mafarkin na farkon "Simahu simal khairi” ma'ana "Na alkhairi ne” na biyu kuma "Simahu simas sharri” ma'ana "Mafarkin sharri ne”

    (Usmannoor: za ta iya yiwuwa na biyun yaji labarin fassarar mafarkin na farkoncan ne sai shi ma ya tambaya don ace masa zai je aikin hajji alhalin kuma shi din barawo ne, shi ya sa aka yanke masa hannu)

    Imam Malik (Malamin Ibn Seerin) shi ma ya taba mafarkin mala'ikan mutuwa (Malakul Maut) ya tambayesa yaushene ranar mutuwa ta, sai Malakul Maut ya yi masa haka (Ya nuna masa yan yatsu 5), sai Imam Malik ya ce shekaru ne, Malakul Maut ya ƙi magana, watannine, yaƙi magana, kwanaki ne, nanma ba amsa, sai malaikan mutuwa ya yi tafiyarsa. Imam Malik ya farka hankakinsa a tashe nan da nan ya kira dalibinsa (Ibn Seerin) ya sanardashi, sai Ibn Seerina ya ce ai ba komai, ba shekaru ba neba, ba watanni ba ne ko kwanaki, karanbani ka so kayi, abin da mala'ikan mutuwa yake nufi shi ne: Mafatuhul Gaibi (Mabudan Gaibu) guda 5 a wurin Allah suke, ba wanda ya sansu sai shi, (Usmannoor: a nan ana nufin shi kansa Malakul Maut bai san ranar da Allah zai aikoshi ya dauki ran Imam Malik ba) sannan fa hankalin Imam Malik ya kwanta

    Don haka fassarar mafarki kyauta ce ga wanda Allah yake wa. ilimin fassarar mafarki fadi ne da shi sosai

    Ga 5 daga cikin mafarkan da na yi kuma suka faru a zahiri;

    1) Mafarkin mun je neman aiki a wani company ni da wani abokin karatu na

    Kuma wani ikon Allah a satin da na yi mafarkin ya cemin na debo ƙualifications dina zamuje wani company suna buƙatar ma'aikata

    Muna zuwa wajen sai na tuno cewar fa last week ni da shi mun nemi aiki saidai ba mu samu ba. Kuma haka kuwan akai domin kuwa bayan anyi mana interview sai gani mukai wasu sun samu aikin mu kuma Allah bai ƙaddara za mu samu ba. Fassarar ta dace da ta mafarkin

    2) Ranar wata Juma'a (28/10/2022) Mu hudu mun kasance daliban ilimi, sai na yi mafarki daya daga cikinmu iftila'i ya sameshi, a mafarkin gashinan cikin wahala kamardai wanda mota ta taka ko kuma wanda ya taka sawun barawo haka. Na sameshi na ce masa na yi wani mafarki akansa amman ya dage da yin sadaka ga yara domin kuwa sadaka tana kauda bala'i da musiba. Na sanarwa da na biyunmu ya ce Allah ya kiyaye tabbatuwar hakan, shi kuma na ukunmu a satin sai gashi mota ta bigeshi ya samu karaya a kafa, na ce da tuni wannan karayar ta afku ga na farkonmu, suka tambayi ko meyasa na ce haka ? Nikuma na tambayi na biyunmu shin akwai wani abu da na farkonmu yake a kwanannan sai sukace tabbas yana sadakar koko da kosai, na ce da ace baya sadakar da tuni shi ne zai samu karayar, silar sadakar sai iftila'in ya tsallake na farkonmu ya afkawa na ukunmu. Fassarar mafarkin ta fito

    3) Mafarkin wani dattijo mai wadata wanda kwanannan ya rasu

    A mafarki an nunamin cewar yana mana nasiha a kan yanayin rayuwa, kwatsam sai ruwan sama ya sauko, aradu ta fado a kusa da gidan marigayin. Muka fita aguje don muganewa idanmu, ashe tsawar a gidan maƙocin marigayin ta fado

    A yanda na fassara mafarkin shi ne; marigayin yana bin mai wancan gidan kudi (bashi) wanda bai biyashi ba har ya rasu saboda tsawar tana nufin halin da mutumin ke ciki na rashin biyan bashin. Da na bi diddigi na tambaya sai akacemin shi ma ai ya dade da rasuwa. A karshedai musamman naje gidan marigayin da yake mana nasiha a mafarkin, na tambayi iyalansa ko akwai alaƙar kudi tsakaninsa da maƙocinsa dincan aka ce min eh tabbas kafin ya rasu yana bin mutumin wasu kudade masu yawa

    Nace musu a gaggauta zuwa gidan wancan marigayin a sanarda iyalinsa cewar ana binsa bashi kuma ya kamata a hanzarta biya. Nan muka rabu na yi musu fatan alkhairi. Fassarar mafarkin ta fito

    4) Haka kuma da yammaci ranar wata litinin a shekarar 2022 na yi mafarkin wani bawan Allah dan anguwanmu wanda a mafarkin aka nunamin cewar matarsa ta haihu ya mace kyakkyawa masha Allah, kamarsu daya da jaririyar, ya riƙeta inata tayashi murna

    Na farka. Tun litinin din naketa nemansa na sanardashi amman ba mu hadu ba sai ranar laraba a wani masallachi. na yi masa bayani, ya ce don Allah fa, ya nuna matuƙar farin ciki, ya cemin yaushe na yi mafarkin na ce masa ranar litinin

    Yacemin kasan wani abu kuwa ? na ce saika fada, ya ce yau kwana 3 muka je asibiti aka yi mata test aka ga tana dauke da juna biyu (Kuma kwana 3 din shi ne ya yi daidai da ranar da na yi mafarkin wato litinin tun da sai larana muka hadu dashi)

    Bayan watanni kadan, dayake na yi tafiya, nadawo gida aka hadu muka gaisa da shi na ce masa ya iyali ? ya ce Alhamdulillah ai anma samu ƙaruwa, me aka samu ya ce Aisha Humairah, na ce masa daman na sani, cikin mamaki ya ce ya akai na sani ? na ce masa ka tuna ai fassarar wannan mafarkin da na yi ke nan, wanda na ce matarka ta haifi ya mace. ya yi mamaki matuƙa. Fassarar mafarkin ta fito

    5) Shekaru 3 da suka shude na yi mafarkin wani bawan Allah muna da'awah taredashi, gashinan muna musuluntarda wasu mata Christians. Na sanardashi, yaji dadin hakan. Muka rabu cikin fatan alkhairi

    A watan (Safar 1445 AH) da ya gabata kuma na yi wani mummunan mafarki akansa, gashinan a masallachin (khamsus salawat) na gidanmu, shi da wasu yan mata an kunna kida a masallachin, sunata tiƙar rawa a cikin masallachin. Wal'iyazubillah

    Na sameshi daga ni sai shi, na ce masa to kaji mafarkin da na yi, don haka ƙalubale gareka, ka gyara alaƙarka da Allah. Ya tsorata kuma ya yi mamakin mafarkin sosai la'akarida fassarar ta zo daidai da halayensa na zahiri, saboda daga ni har shi da kuma mutanen anguwa ansan halayyarsa, ya ce in sha Allahu za a gyara. na ce masa Allah ya ba mu ikon gyarawa baki daya. Nan muka rabu

    A karshe ina jan hankalina da kuma sauran musulmai a kan mu gyara halayenmu. Sannan kuma a guji neman fassarar mafarki a wajen kowanne mutum domin kuwa hadisi sahih ya tabbata cewar duk wanda ya fara fassara maka mafarki to abin da ya fada shi ne yake kasancewa da izinin Allah. Kada ka kuskura kaje wajen wanda zai ce maka saika ba da kudi ko kuma saika yanka wata dabba, duk wannan yan bidi'a ne da kuma yan duba (Bokaye), don haka kaje ka samu malamin Ahlus Sunnah wanda zai kafa maka hujja da littafin irin manyan malamai kamarsu Ibn Seerin (Tabi'i kuma dalibin Imam Malik)

    Domin kawarda kokwanton da shaidan zai sanyawa mutum, zaifi sauƙi mutum ya dage da addu'a domin kuwa idan Allah SWT ya ƙaddara za ka samu iftila'i a mafarki, to addu'arka sai ta sauya ƙaddarar kamar yanda hadisi ya tabbata a cikin sahihin hadisin da Abdullahi Ibn Abbas RA ya rawaito

    (Duba littafin Tuhfat al-Ahwadhi wallafar Al-Mundhiri hadisi mai lambata 9, chapter 13)

    Wallahu ta'ala a'alam

    Allah ta'ala ya sa mudace.

    Subhanakallahumma wabi hamdika ash hadu anlailaha illa anta astagfiruka wa'atubi ilayk

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.