Ticker

Gajeruwar Mallaka

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

255. In ka duba duk halittunmu na raye,

 Wasu na nan tudu waɗansu ruwa ɓoye,

 Wasu na nan cikin ƙasa sama tsuntsaye,

A halittu kakan ishe wasu dogaye,

Wata kuma ‘yar gajeruwa mai burgewa.

 

256.  Haka nan ko a mallaka ma ya kasance,

 Ga mu da mallaka guda biyu bambance,

 Can daga baya doguwa muka tantance,

 Nan kuma wadda za ta zo ma a nazarce,

  Za ka tarar da guntuwa mai liƙewa.

 

257. Ba ware ta za a yi can gefe ba,

Dokokinta ga su in ba ka gane ba,

Duk abu naka wanda in an duba,

Ga rubutunsa in ka zo ƙarshe duba,

  Liƙe take zuwa da kalmar furtawa.

 

258. Dakanta a yanzu zan zana sifarta,

 In suna ya zo da liƙin da ka bin ta,

 Koko wakilin da da shi sai a rubuta,

 Harufa masu fayyace ta a gane ta,

  Harafin ‘r’ da ‘n’ wajen jinsantarwa.

 

259. Tsarin na da ƙa’ida sai mu kiyaye,

 Za a yi ɗofanen wakilin sunaye,

 Nan ƙarshe gaɓar abin nasu ko waye,

 Sai su bi mallakin rubutun a kiyaye,

  Za su haɗe da ‘r’ da ‘n’ ga rubutawa.

 

260. A misalan da za su zo ga bayaninmu,

 Su ne za su haskaka maka aikinmu,

Can ga faɗarka ka ga rigarmu, jiharmu,

Haka Ɗakinsu, ga gidansu da gefenmu,

  Ga dikunta ga zaninta na ɗaurawa.

 

261. Sa natsuwa da kyau ka duba misalinka,

 Ka ga ɗiyanka ga su zaune a falonka,

 Je ka gidanka can ka ɗauko motarka,

Dubi gidansa ko gidanta, bayaninka,

Alƙawalinmu, shawararki, ga hangowa.

 

262. A misalan da sun ka zo in ka duba,

Ba ɗangon da mallaka ba ta kutsa ba,

An kuma ɗofana ta ko ba ka gane ba,

Da wakilin abin ka ko ba shi ne ba?

  Kuma a gaɓa take fita can ƙarewa.

 

263. An saka ‘r’ da ‘n’ gurin an ƙuƙƙulla,

 Kuma aikinsu na ga jinsi tafi kalla,

 ‘n’ gefen maza, ‘r’ macce ta kalla,

Albishirinka ɗan’uwa ce madalla!

  Je ka yi bita kai kaɗai don ganewa.

 

264. Mun tattauna mallaka ga bayaninmu,

 Mun faɗi doguwa, gajera ta samu,

 Mun kuma tattaro misalan aikinmu,

 Tammat mun rufe gajeren babinmu,

  Ba da faɗa ba hankali ke nunawa.

Post a Comment

0 Comments