Game Da Rayuwa

    Abu-Ubaida Sani
    Abu ne mai matuƙar kyau na sama ya lura da buƙatu da muradun zucin waɗanda ke ƙasa da shi. Ya ba shi damar fitar da waɗannan muradu ta hanyar sake masa fuska da ba shi damar bayyana tunani da ra’ayoyinsa. Wannan zai taimaka wa lafiyar ƙwaƙwalwar yara da bunƙasar kaifin basirarsu. (Sani, A-U. 2023)

    Abu-Ubaida Sani
    Wata hanyar gane muradu da buƙatun zuci na yara ita ce lura da alamomi da za su iya nunawa yayin da kawaici da kunya da sauran tanade-tanaden al’ada suka dabaibaiye ƙwarin guiwarsu. (Sani, A-U. 2023)

    Abu-Ubaida Sani
    Tauye tunani da muradun matasa ba tare da bayyana musu dalilin hakan da kuma yi musu ishara da mafifin zaɓi ba, na iya haifar musu da daƙushewar kaifin tunani da sallama rayuwa da fafutukan samun nagartaccen gobe da kuma sakankancewar da ka iya kaiwa ga wofantar zuciya. (Sani, A-U. 2023)

    Abu-Ubaida Sani
    Tara dukiyar da rayuwa da mutuwa ba za su amfana da ita ba, abu ne mai wahalar bayani a matsayin hankali ko hauka! (Sani, A-U. 2023)

    Abu-Ubaida Sani
    Abu mafi burgewa a duniya bai dogara kan halin farin ciki da walwala da kake ciki ba, ya fi dogara kan adadin mutane da sauran halittu da ke samun farin ciki da sauƙin rayuwa dominka - ballantana a lahira! (Sani, A-U. 2023)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.