Ticker

Hadisin Rabuwar Al’umma

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Ina tambaya a kan hadisin Rabuwan al’umma gida saba’in da uku (73), dukkansu ’yan Wuta sai dai guda ɗaya, ga shi kowa yana tunanin ƙungiyarsa ce wannan ɗayar. To wace shawara malam zai ba ni domin in dace da wannan ɗayar ta gaskiya, kuma in samu rabauta a Lahira?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

[1] Da farko dai hadisin rabuwar al’ummar shi ne abin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

« أَلَا إِنَّ مَنْ قَبْلَكُمْ مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ افْتَرَقُوا عَلَى ثِنْتَيْنِ وَسَبْعِينَ مِلَّةً، وَإِنَّ هَذِهِ الْمِلَّةَ سَتَفْتَرِقُ عَلَى ثَلَاثٍ وَسَبْعِينَ: ثِنْتَانِ وَسَبْعُونَ فِي النَّارِ، وَوَاحِدَةٌ فِي الْجَنَّةِ، وَهِيَ الْجَمَاعَةُ »

Ku ji da kyau! Haƙiƙa waɗanda su ke a gabaninku daga cikin Ahlul-Kitaab sun karkasu zuwa gida saba’in da biyu. Kuma wannan al’ummar za ta karkasu har gida saba’in da uku: Guda saba’in da biyu suna cikin Wuta, guda ɗaya kuma tana cikin Aljannah: Ita ce: Ƙungiyar Jamaah. (Ahmad: 17211 da Abu-Daawud: 4597 suka riwaito shi daga Hadisin Muawiyah Bn Abi-Sufyaan, kuma Al-Haafiz ya hassana shi, haka ma Al-Albaaniy).

A wata riwaya kuma ya ce:

« كُلُّهُمْ فِي النَّارِ إِلَّا مِلَّةً وَاحِدَةً »، قَالُوا : وَمَنْ هِيَ يَا رَسُولَ اللَّهِ؟ قَالَ : «مَا أَنَا عَلَيْهِ وَأَصْحَابِي»

Dukkaninsu suna cikin Wuta sai dai addini guda ɗaya: Suka ce: Wacce ce ita, Manzon Allaah? Ya ce: Abin da na ke a kansa ni da Sahabbaina. (At-Tirmiziy (2641) ya riwaito shi, kuma Al-Albaaniy ya hassana shi a cikin Sahih Al-Jaami’: 5219).

Sai kuma ya ƙara bayanin hanyar tsirar a hadisin da Abdullaah Bn Masud (Radiyal Laahu Anhu) ya riwaito cewa:

خَطَّ لَنَا رَسُولُ اللهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَخَطًّا ، ثُمَّ قَالَ : " هَذَا سَبِيلُ اللهِ " ، ثُمَّ خَطَّ خُطُوطًا عَنْ يَمِينِهِ وَعَنْ شِمَالِهِ ، ثُمَّ قَالَ : " هَذِهِ سُبُلٌ - قَالَ يَزِيدُ: مُتَفَرِّقَةٌ - عَلَى كُلِّ سَبِيلٍ مِنْهَا شَيْطَانٌ يَدْعُو إِلَيْهِ "، ثُمَّ قَرَأَ : (وَأَنَّ هَذَا صِرَاطِي مُسْتَقِيمًا فَاتَّبِعُوهُ وَلَا تَتَّبِعُوا السُّبُلَ، فَتَفَرَّقَ بِكُمْ عَنْ سَبِيلِهِ)

Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya zana mana zane, sannan ya ce: Wannan ce hanyar Allaah. Sai kuma ya zana zanunnuka a damansa da hagunsa, sannan ya ce: Waɗannan su ne hanyoyi (mabambanta). A kan kowace hanya daga cikinsu akwai sheɗani yana kira zuwa gare ta. Sai kuma ya karanta: (Kuma lallai wannan ita ce hanyata tana miƙaƙƙiya, sai ku bi ta. Kar kuma ku bi yan hanyoyi, sai su rarrabe ku a kan hanyarsa). (Sahihi ne, Ahmad: 4142 da An-Nasaaiy (Al-Kubraa): 11109 suka riwaito shi daga hadisin Abdullaah Bn Masud).

A wani hadisin kuma Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

« لَا تَزَالُ طَائِفَةٌ مِنْ أُمَّتِي ظَاهِرِينَ عَلَى الْحَقِّ، لَا يَضُرُّهُمْ مَنْ خَذَلَهُمْ، حَتَّى يَأْتِيَ أَمْرُ اللهِ وَهُمْ كَذَلِكَ »

Waɗansu jama’a daga cikin al’ummata ba za su gushe ba suna a kan gaskiya, wanda ya yi watsi da su ba zai cutar da su ba, har sai al’amarin Allaah ya zo. (Sahih Muslim: 1920-170).

[2] Malamai da dama sun yi bayanin waɗanda ake nufi a waɗannan hadisan:

As-Shaikh Abdulqaadir Al-Jeelaaniy ya faɗa a cikin littafinsa: ‘Al-Ghunyah’ cewa:

أَمَّا الْفِرْقَةُ النَّاجِيَةُ فَهِيَ أَهْلُ السُّنَّةِ وَ الْجَمَاعَةِ ، وَ أَهْلُ السُّنَّةِ لَا اسْمَ لَهُمْ إِلَّا اسْمٌ وَاحِدٌ، وَ هُوَ أَصْحَابُ الْحَدِيثِ.

Amma Al-Firqatun Naajiyah su ne dai Alus-Sunnah Wal Jamaa’ah. Su kuma Ahlus Sunnah ba su da wani suna sai suna ɗaya, shi ne: As-haabul Hadeeth.

Kafin shi ma Ibn Al-Mubaarak (Rahimahul Laah) ya ce:

« هُمْ عِنْدِي أَصْحَابُ الْحَدِيثِ »

A fahimtata su ne: As-haabul Hadeeth, wato malaman hadisi.

Al-Bukhaariy kuma ya ce: Aliyu Bn Al-Madeenee (Rahimahumal Laah) ya ce:

« هُمْ أَصْحَابُ الْحَدِيثِ »

Su ne: Malaman Hadisi.

Ahmad Bn Hambal (Rahimahul Laah) kuma ya ce:

« إِنْ لَمْ تَكُنْ هَذِهِ الطَّائِفَةُ الْمَنْصُورَةُ أَصْحَابَ الْحَدِيثِ ، فَلَا أَدْرِي مَنْ هُمْ »

Idan dai waɗannan At-Taa’ifatul Mansuurah ba su zama Malaman Hadisi ba, to kuwa ban san ko su wanene ba?!

[3] Su kuwa malaman Hadisi mutanen masu falala sosai, kamar yadda Al-Khateeb Al-Baghdaadiy (Rahimahul Laah) ya rubuta a cikin littafinsa: Sharfu As-haabil Hadeeth, shafi: 7-9:

« وَقَدْ جَعَلَ اللهُ تَعَالَى أَهْلَهُ أَرْكَانَ الشَّرِيعَةِ ، وَهَدَمَ بِهِمْ كُلَّ بِدْعَةٍ شَنِيعَةٍ ، فَهُمْ أُمَنَاءُ اللهِ مِنْ خَلِيقَتِهِ ، وَالْوَاسِطَةُ بَيْنَ النَّبِيِّ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَسَلَّمَ - وَأُمَّتِهِ ، وَالْمُجْتَهِدُونَ فِي حِفْظِ مِلَّتِهِ ، أَنْوَارُهُمْ زَاهِرَةٌ ، وَفَضَائِلُهُمْ سَائِرَةٌ ، وَآيَاتُهُمْ بَاهِرَةٌ ، وَمَذَاهِبُهُمْ ظَاهِرَةٌ ، وَحُجَجُهُمْ قَاهِرَةٌ »

Allaah Ta’ala ya sanya Malaman Hadisi matsayin wani rukuni na musamman a Shari’arsa, kuma da su ne yake rushe duk wata baƙar bidia a cikin addininsa. Don haka, su ne Amintattun Allaah a cikin halittunsa, kuma su ne gada ko tsani a tsakanin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da al’ummarsa, kuma su ne malamai mujtahidai masu ƙoƙari domin tsare addininsa. Haskensu mai tsananin kyau ne, darajojinsu masu yaɗuwa ne a ko’ina, karamominsu masu matuƙar burgewa ne, mazhabobinsu marinjaya ne a fili, kuma hujjojinsu masu tsananin ƙarfi ne.

[4] Daga cikin siffofin Ahlul-Hadeeth akwai cewa:

Suna lazimtar tafarkin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a cikin rayuwarsa, da kuma tafarkin Sahabbansa a bayansa.

Suna komawa ga Littafin Allaah da Manzon Allaah a lokacin jayayya da saɓani.

Ba sa gabatar da maganar kowa a kan maganar Allaah da Manzonsa.

Suna kulawa da Tawheed ta fuskar koyo da koyar da shi. Domin shi ne ginshiƙi ko tushe na asali wanda ake gina sahihiyar daular musulunci a kansa.

Suna rayar da Sunnonin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a cikin ibadojinsu da mu’amalolinsu a cikin rayuwarsu.

Ba su maƙalewa wata magana sai dai maganar Allaah da maganar Manzonsa kaɗai, wanda ya ke tsararre daga bin son zuciya ko sha’awar rai.

Su dai Ahlul-Hadeeth su ne waɗanda mawaƙi yake faɗi a kan su cewa:

أَهْلُ الْحَدِيثِ هُمُ أَهْلُ النَّبِيِّ وَ إِنْ * لَمْ يَصْحَبُوا نَفْسَهُ أَنْفَاسَهُ صَحِبُوا

Ahlul-Hadeeth su ne mutanen Annabi kuma kodayake, ba su sahibci shi kansa ba amma dai sun sahibci numfashinsa.

Suna martaba manyan Limamai, amma ba su maƙale wa raayin wani guda daga cikinsu.

Suna umurni da kyakkyawan aiki kuma suna hana mummunan aiki.

Suna kiran musulmi ga su zama abu ɗaya ta hanyar maƙalƙalewa Sunnar Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da Sahabbansa.

Suna ƙyamar duk tsarin dokokin da mutane suka tsattsara waɗanda suka saɓa wa hukuncin Musulunci. Don haka suna kira zuwa ga yin hukunci da Littafin Allaah.

[6] Yadda ake gane waɗannan mutanen shi ne:

Su ne ’yan kaɗan a cikin mutane.

Mutane masu yawa suka adawa da su, kuma suna ƙulla musu sharri, suna jifan su da munanan laƙubba.

An tambayi Shugaban Manyan Malaman Saudiyyah As-Shaikh Abdul’azeez Bn Baaz (Rahimahul Laah) a kan Al-Firqatun Naajiyah, sai ya ce: Su ne Salafiyyah, da kuma duk wanda yake gudana a kan tafarkin As-Salafus Saalih (Magabata Na-ƙwarai), wato Annabi da Sahabbansa.

[7] Don haka shawara a gare ni da kai/ke da dukkan musulmi da sauran jama’ar duniya ma ita ce: Kowannenmu ya yi ƙoƙarin bincikowa da gano wannan ƙungiyar jamaar ta masu bin musuluncin gaskiya, kuma ya kafe a kan bin hanyarta na yin aiki da Al-Kitaab Was Sunnah a kan ganewa da koyarwar Magabatan wannan al’ummar har zuwa mutuwarmu.

Allaah ya taimake mu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments