Ticker

Hade Kalmomi a Rubutu: Gabatarwa

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

237. Mun ƙare baƙi wasulla haka gaɓɓai,

 Haɗuwar baƙi, wasal, samun gaɓɓai,

 Kalma samuwarta sai an haɗa gaɓɓai,

 Ɗauri ma yakan taho ne kan gaɓɓai,

Mun ga rawar baƙi da dokar ɗaurewa.

 

238. Yanzu taƙaice mun shigo ne a rubutu,

 Da akwai tsare-tsare mai kyau ga rubutu,

 Ga kuma ƙa’ida gare shi komi ya kyautu,

Don haka sai mu duba ƙaidar nan ta rubutu,

  Yadda ake sanin rubutu na haɗewa.

 

239. Doka mai haɗe rubutu mu gwada ta,

Mui nazari mu sa misalai mu misalta,

Kalmomi daki-daki za mu fasalta,

Har da waɗansu ‘yan misalai mu rubuta,

  Da dalilin haɗe su domin nunawa.

 

240. Ba a bin abin da duk bai dace ba,

Ba son rai, ina gani ne ilmi ba,

Kirdado ba a yi ba, ba ra’ayi ba,

Ba a hawan ƙawara, ba a yo shirme ba,

  Bin doka da ƙa’ida babu laɓewa.

 

241. Babin nasu zai fito da fasulla ne,

 Za a raba daki-daki ga bayani ne,

 Lura akwai wurin an so a haɗe ne,

 Ba a buƙatar rabe shi domin doka ne,

Bakin gwargwado ga doka ta haɗewa.

 

242. Yadda ake haɗe rubutu hikima ce,

 Ita ke rarrabe rubutu a karance,

 Shi ya zam ba kure da sauƙi a rubuce,

 Rubutu ya yi kyau a gane komi a karance,

  Don ma’anar abin ta zan daidaicewa.

Post a Comment

0 Comments