Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
740. Na gode wa Jalla Sarki Mabuwayi,
Wanda ka sa wuta
ta koma ta yi toyi,
Wanda ya ƙagi duniya yay yi
Nabiyi,
Da sahabbansa
Ahlihi had da waliyi,
Wanda ya ƙaddaro ni bokon Hausawa.
741. Masana Hausa ko guda ban ɗebe ba,
Ku duka kun yi ƙoƙari ban yada ba,
Ba tamkar ku ni
garan ba wai ne ba,
Dukkanninku na yaba,
ban ware ba,
Nai muku godiya ga ƙwazon koyarwa.
742. Ibrahim Yahaya Rabbu ka yafe mai,
Kai rahama gare
shi Rabbu ka ƙara mai,
Dukkan ni’ima
Ilahu an sa a daɗa mai,
Sannan zuriyarsa
Rabbu an ƙara ɗaga mai,
Babban malamin
Alu gun koyarwa.
743. Bari in ƙara godiya gun Ɗangambo,
Babban malaminmu
malam Ɗangambo,
Sannan Garkuwan
Adab ne Ɗangambo,
Farfesan adab a nemo Ɗangambo,
Babban malamin da
ba na mantawa.
744. Bayaro Malamin Alu ɗa ga Yahya,
Ba fa Alu kaɗai ba har ni da Ruƙayya,
Abdullahi Bayaro,
jikan manya,
Jikan Nana ‘yar
tsatson girma manya,
Jagoran Alu ga
B.A. farawa.
745. Ɗalhatu na yaba da alkancin ka,
Kai ka duba Ali ka
yi hukuncinka,
Ka lamunta, ka
yaba kai aikinka,
Ka yarda Alu ya
karɓi Dakta don doka,
Kakana na bincike
gun Hausawa.
746. Burina ga wagga waƙa a kiyaye,
Ai hattara wurin
rubutu kai waye,
A bi tsari na
gaskiya, kar fa a tauye,
Kowane ɗalibi ya duba ya kiyaye,
Dukkan ƙa’idar rubutun
Hausawa.
747. Ya zamo sun zamo jiki gun mai koyo,
Yai ta faɗinsu ba tsayi nan gun koyo,
Maimaicin ta ko’ina in har zai yo,
Ɗan baiti ya zanto ita
ce dai zai yo,
Ko tafiya yakai
yana iya rerawa.
748. Burina ƙasar ga kamin a naɗe ta,
Kowane yanki ya
koya ya rubuta,
Harshen Hausa yai yawa
sai gane ta,
Dukkan al’uma fa
tilas su iya ta,
Hausa ta mamaye
harasan Turawa.
749. Tun a Firamarenmu manyan makarantu,
Har da sakandare
mu su ne matsakaitu,
Har taciary, shirin ya zan zai yi nagartu,
Har can University abinmu ya ingantu,
Turanci ya bar
aji bai shirya ba.
750. Nahawun Hausa ga shi dai mun waƙe shi,
Mun yi shiri ga ɗalibanmu su gane shi,
Su ji sauƙi wajen biɗa da karanta shi,
Mun tsara shi mun
zuba, ga adadin shi,
Bisa baiti ɗari bakwai ga ƙarawa.
751. Sa hamsin cikin ƙidar ga jimillarsu,
Ɗauko ɗari bakwai ka sa lissafinsu,
Sai an tattara ka san kimaninsu,
Ka ji ɗari bakwai da hamsin ga ƙidansu,
Ga wuturi guda na
ƙarshen ƙirgawa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.