Ticker

Tasirin Rubutun Turanci

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

697. Wasulan Hausa ba a mai da su baƙaƙe,

 Lura da kyau a hankali malam miƙe,

 Zabura sai ka ɗauko littafi take,

 Nemo wurin da kag ga sun canza baƙaƙe,

  In ka ga an yi ai kure sai gyarawa.

 

698. Amma Hausa babu shi ko a karance,

 Kar ka saka shi ka jiya malam kauce,

 Doka ce ta Hausa ta zo a rubuce,

 Turanci yake da wannan a rubuce,

  Har lafazinsa ma yana iya ɗaukawa.

 

699. A wajen Hausa ƙa’ida za a tsayawa,

 Sai a rubuta yadda lafazi ke furtawa,

 Dole a sa baƙi ga ƙa’ida ta rubutawa,

 Ba wasali kamar rubutun Turawa,

  Ba ƙari bale ragi ga hukuntawa.

 

700. “Zaria” Ingilishi ne don ka kiyaye,

 Ba a rubuta “a” muhallin a kiyaye,

 Dole a zo da “y” rubutun kai waye,

 Ya zama “ya” ba “a” ba ta cika ehe,

  “Zariya” za a sa rubutun Hausawa.

 

701. “Funtua” ma kuren baƙi ne ga rubutu,

 An saka “a” ta ya ake so ya karantu?

 Harshen Hausa na da tsari na rubutu,

 Ankara kar ku dambale masu karatu,

“Funtuwa” za ka sa ka zan mai ganewa.

 

702. “Kankia” ka yi shirɓace sai gyarawa,

 An shafe baƙi na “y” ka zan mai ganewa,

 Nan ga bagirenta  “a” ta zo ga wakiltawa,

 An yi kure cikin rubutun Hausawa,

“Kankiya” mun ka san ta mu kan Hausawa.

 

703. Sa “Najeriya” kure ne ga rubutu,

 “A” bagirenta “i” ya dace a rubutun,

 Bai dace ba sam a tsari na rubutu,

 Don haka lura ku masu karatu,

  Ko ‘Nageria” a dai ƙara kulawa.

 

704. Haka “Nijeria” baƙi an ɓata shi,

 Duk an hautsine shi du an kwaɓe shi,

 An saka Hausa, sannan Ingilishi,

 Wanga jagwalgwale ba a karanta shi,

  Sa “Nijeriya: ka zan mai ganewa.

 

705. “Saudi Arebia” rubutun London ne,

 In an sa shi Hausa to ka san akasi ne,

 Wasali bai maye baƙi, a Hausa haramun ne,

 Doka ta yi tanadi ko ka gane?

  “Saudi Arebiya” musulmi ke cewa.

 

706. “Birnin Kebbi” ka ji shirmen Turawa,

 Sun raɗa sunan ƙasar muhallin na Kabawa,

Saurara ka ji mu yadda muke cewa,

 Ai “Kabi” mun ka san ta shi muka furtawa,

Sa “Kabi” kar ka zamto jikan Gwarawa.

 

707. Shehu Mujaddadinmu Ɗanfodiyo ke nan,

 Ya yi gwagwarmaya,ƙasar ga jihadin nan,

 Kuma yai taimako, ya ceci addini sannan,

 In an zo rubuta suna nai to nan,

Kar ka rubuta “O” kwatancin Turawa.

Post a Comment

0 Comments