Kundin Digiri Na Farko (B.A HAUSA) Wanda Aka Gabatar A Sashen Nazarin Harsuna Da Al’adu, Tsangayar Fasaha, Jami’ar Tarayya Gusau, Jahar Zamfara, YULI, 2023
NAZARIN HAUSAR YAN LAKUM A GARIN GUSAU
Na
SABITU SANI
AMINCEWA
Wannan kundin Bincike na SABITU SANI mai Lamba 1820104005, ya cika ƙa’idojin da aka shimfiɗa dangane da neman takardar shedar digirin farko (B.A
Hausa) a Sashen Nazarin Harsuna da Al’adu
Jami’ar Tarayya Gusau.
SADAUKARWA
Na Sadaukar da wannan aiki ga mahaifana, Alhaji Muhammadu da Malama A’isha da
kuma Malama Marwanatu Shehu da kuma Matata Malama Aina’u Suleiman, da Alhaji
Mustapha Mudassir (Per-Master) da dukkanin sauran ‘yan uwana.
GODIYA
Dukkanin yabo da godiya sun tabbata ga Ubangijinmu mahalicci, Maɗaukakin Sarki, wanda shi ne ya ba da damar gudanar da
wannan bincike, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW)
fiyayyen halitta da iyalan gidansa da sahabbansa da kuma magabata, tare da
mutanen kirki da suka duƙufa wurin ba da ilimi ga al’umma.
Ina amfani da wannan damar domin miƙa godiyata ga mahaifina da fatar Allah ya jiƙansu da Rahama, haka
kuma ina mika godiya ta ga malamina kamar Dr. Adamu Rabi’u Bakura da Malam Abu
Ubaida Sani, da Muhammad Arabi, da Malam Isa Sarkin Fada, da Mal. Musa
Abdullahi da sauran ɗaukacin malamaina tun daga ajin farko har zuwa na ƙarshe. Ina kuma godiya ga dukkanin
waɗanda suka ba da gudummawa a wurin
karatuna da kuma wannan aiki, musamman maigidana Alh. Mustapha Mudassir
(Per-Master) wanda ya taka rawa ta musamman a wannan karatu nawa.
Daga ƙarshe ina miƙa godiya ta ga abokanan karatuna kamar Hajiya Rukayya Yusuf S/Fada, Zainab
Abdulkadir da Muhammad Yahaya da sauran su, da fatar Allah ya sa wannan karatu
ya amfani al’umma baki ɗaya.
TSAKURE
A duk lokacin
da aka samu waɗansu mutane sun keɓe kansu a
wani muhalli na daban, akasari a kan samu wanzuwar wani karin harshe na rukuni
wanda ya keɓenta ga waɗannan mutane
kawai. Duba da wannan ne ya sa aka gudanar da wannan bincike na Nazarin Hausar
‘Yan Lakum a garin Gusau. Wannan bincike mai taken Nazarin Hausar ‘Yanlakum
bincike ne da ya zaƙulo sabbin
kalmomi da jimloli da “Yanlakum suka samar a rukuninsu. Sannan binciken ya gano
hanyoyin da ‘Yan Lakum suka yi amfani da su yayin samar da waɗannan
kalmomin nasu. Baya ga wannan bincike ya kawo wasu daga cikin dabarun da ‘Yan
Lakum suke yi a lokacin da suke aiwatar da aikinsu na sana’ar Lakum. Sannan
daga ƙarshe aka zo da shawarwari ga ɗalibai da
masana da attajirai da ma ɗaukacin al’umma gaba ɗaya.
ƘUNSHIYA
i. Amicewa -- iii
ii. Sadaukarwa -- --
iv
iii. Godiya - -- -
-- v
iv. Tsakure- -- -
-- vi
v. Ƙunshiya -- -- viii
BABI NA ƊAYA: Gabatarwa
1.0 Shimfiɗa --
-- 1
1.1 Manufar Bincike -- -- - -- 4
1.2 Farfajiyar Bincike - -- 5
1.3 Hasashen Bincike -- -- - -- 5
1.4 Matsalolin Bincike -- -- - -- 6
1.5 Muhimmancin Bincike -- -- 8
1.6 Hanyoyin Gudanar da Bincike 10
1.7 Ra’in Bincike -- -- - -- 11
1.8 Naɗewa - -- -- 13
BABI NA BIYU: Bitar Ayyukan da Suka
Gabata
2.1 Bitar Ayyukan da suka Gabata 14
2.1.1 Bugaggun Littafai -- -- 15
2.1.2 Kundayen Bincike-- -- 19
2.1.3 Muƙalu da Mujallu -- -- 28
2.2 Hujjar Cigaba da Aikin Bincike 39
2.3 Naɗewa -- -- 44
BABI NA UKU: Fashin Baƙi a Kan Ma’anonin Shafi Taken Bincike
3.0 Shimfiɗa-- -- - -- -- 45
3.1 Ma’anar Nazari -- - -- 45
3.2 Ma’anar Kalmar Hausa -- -- 46
3.3 Ma’anar Kalmar Lakum ko ‘Yan Lakum - -- -- 50
3.2 Kashe – Kashen ‘Yan Lakum - -- 51
3.3 Wasu Daga cikin Dabarun ‘Yan Lakum -- -- -
-- 53
3.4 Badali -- -- -
-- 54
3.5 Amayo Allurai da fyatosu ta hanci -- -- 54
3.6 Tayar da Hayaƙi -- - -- 55
3.7 Yanka Wuƙa a jiki-- -- - --
55
3.8 Tayar da Wuta -- -- - -- 56
3.9 Naɗewa
-- -- 58
BABI NA HUƊU: Hausar ‘Yan
Lakum a Garin Gusau
4.0 Shimfiɗa --
-- 59
4.1 Taƙaitaccen Tarihin Garin Gusau 59
4.2 Hausar ‘Yan Lakum A Garin Gusau - -- -- - - -- 65
4.3 Sunayen Kuɗi a wurin ‘Yan Lakum - -- -- -
- -- 65
4.4 Kalmomi ta hanyar ƙirƙira - -- 67
4.5 Kalmomi ta hanyar kwatance da siffantawa- ---- 68
4.6 Kalmomi ta hanyar aro -- -- -
- -- -- 70
4.7 Kalmomi ta hanyar gusar da ma’ana - -- -- - -- 72
4.8 Jimlolin ‘Yan Lakum-- - -- 74
4.9 Naɗewa-- -- - - --
-- 76
BABI NA BIYAR : Sakamakon Bincike
5.0 Shimfiɗa-- -- - - --
-- 77
5.1 Sakamakon Bincike -- --
77
5.2 Shawarwari-- -- -
-- - -- 79
5.3 Naɗewa-- -- - -- -
-- 81
Manazarta -- - --
-
-- - -- 84
GABATARWA
1.0 SHIMFIƊA
Wannan aiki mai taken “Nazarin Hausar ‘Yan Lakum a Garin Gusau” bincike ne
da ya yi ƙoƙarin binciko yadda ‘Yan Lakum (Masu Wa’azin Turmi) a garin Gusau su ke yin
Hausar su domin sadarwa a tsakanin su da juna.
Wannan nazari ne da ya danganci ilimin walwalar harshe, kuma zai mayar da hankali a kan Karin harshen rukuni, wanda ya shafi Hausar ‘Yan Lakum ta fuskar sara a wajen mu’amala ta sadarwa tsakaninsu da juna ko da sauran jama’a.
Wannan gabatarwar ita ce fitila wadda ta haskaka dukkan abin da ya wakana a cikin wannan kundin bincike, domin ita ce ke ɗauke da dukkan tubalan ginin wannan aiki.
Domin samun sauƙin gudanar da wannan
aiki, an tsara wannan aiki a kan tsarin babi-babi, tun daga babi na ɗaya har zuwa babi na
biyar.
A babi na ɗaya an yi tsokaci a kan manufar wannan bincike da farfajiyar bincike da hasashen bincike, da matsalolin bincike, da muhimmancin bincike da hanyoyin gudanar da bincike, da ra’in bincike, sai kuma aka zo da naɗewa a ƙarshen babin.
A babi na biyu, mai kanun bitar ayukkan da suka gabata, bayan an yi shimfiɗa, sai bitar ayukkan da suka gabata, am fara da rubutattun littafai, sai kundayen bincike da aka rubuta a matakai daban daban na ilimi, sai kuma maƙalu da mujallu, duka dai masu nasaba da kuma alaƙa da wannan bincike, sai kuma hujjar cigaba da bincike, daga ƙarshe aka zo da naɗewa.
Babi na uku, mai kanun fashin baƙi a kan ma’anonin da suka shafi taken bincike, bayan an
yi shimfiɗa, an kawo ma’anar kalmar Hausa, da
ta Lakum da kuma ‘Yan Lakum, sannan an kawo kashe kashen ‘Yan Lakum daga nan
kuma aka zo da wasu daga cikin dabarum ‘Yan Lakum sai kuma naɗewa.
Babi na huɗu, mai kanun Hausar ‘Yan Lakum a garin Gusau, an fara da shimfiɗa, taƙaitaccen tarihin Garin Gusau, Hausar ‘Yan Lakum a garin Gusau, an kawo kalmomin da ‘yan Lakum suka samar a wannan rukuni nasu, an kasa kalmomin ta la’akari da dubarar da aka yi amfani da ita ko hanyar da aka bi yayin samar da waɗannan kalmomi na ‘Yan Lakum, bayan nan aka kawo yankunan jimloli, da kuma jimlolin Hausar ‘Yan Lakum daga ƙarshe aka zo da naɗewa
A babi na biyar, mai kanun sakamakon bincike, bayan an yi shimfiɗa, sai aka kawo sakamakon bincike, daga nan kuma aka zo
da shawarwari, sai kuma jawabin naɗewa da kuma manazarta.
BABI NA ƊAYA
1.0 SHIMFIƊA
Wannan babi na ɗaya za a yi magana a kan manufar wannan bincike, da farfajiya ko kadadar bincike, da hasashen bincike, da matsalolin bincike, da muhimmancin bincike da hanyoyin gudanar da bincike da ra’in bincike, sai kuma daga ƙarshe a zo da naɗewa.
1.1 MANUFAR BINCIKE
A rayuwa babu wani
abu da za a aiwatar ba tare da wata manufa ba, saboda haka wannan bincike ko
nazari an gudanar da shi domin cimma wasu manufofi kamar haka:
1) Zaƙulo
keɓantattun
kalmomin da 'Yan Lakum suka ƙirƙira
kuma suke amfani da su a zantukansu na yau da kullun.
2) Gano hanyoyi
ko dabarun da suke bi ko amfani da su yayin ƙirƙira
waɗannan kalmomi
nasu na fannu.
3) Zaƙulo
sabbin jumloli da kuma yankunan jimlolin da suka samar daga waɗannan kalmomi
nasu kuma suke amfani da su a lokacin sadarwa tsakaninsu.
1.2 FARFAJIYAR BINCIKE
Kasancewar harshen Hausa yana da manyan rassa
uku na nazari waɗanda suka
kunshi:
a. Adabi (literature),
b. Al’ada (culture)
c. Da kuma harshe (language).
Wannan bincike an gudanar da shi ne a ɓangaren
harshe, wanda ya kebanta a fannin ilimin walwalar harshe. Hasali ma an keɓance binciken
a cikin garin Gusau kacokam, musamman
yankin birnin ruwa a Gundumar Mayana inda nan ne yawancin masu wannan sana’a ta
lakum su ka fi yawaita.
1.3 HASASHEN BINCIKE
Kasancewar kusan kowane rukunonin al’umma
sukan keɓanta da Karin
harshensu, domin sadarwa a tsakaninsu, ana hasashen su ma rukunin masu sana’ar
lakum ya amsa sunansa na rukuni, ya zamana suna da:
v Kalmomi nasu
na fannu da suka ƙirƙira kuma suke
amfani da su tsakaninsu da juna.
v Hanyoyi ko
dubaru da suke bi ko amfani da su wajen samar da waɗannan kalmomi
nasu.
v Jimloli da
kuma yankunan jimloli da suka ƙirƙira
sanan kuma suke amfani da su yayin sadarwa da junansu.
1.4
MATSALOLIN BINCIKE
A kowane irin al'amari na rayuwa da ake
gudanarwa ba a rasa cin karo da 'yan matsaloli nan da can ba, musamman a
lokacin da ake gudanar da shi. Don haka, a yayin aiwatar da wannan
binciken an haɗu da wasu 'yan
matsaloli da ƙalubalai. Kaɗan daga cikinsu akwai:
«
Matsalar
masu gida rana (kuɗi)
Babu shakka,
wannan matsala ta kuɗi babbar matsala ce
da take ci wa al'umma tuwo a ƙwarya musamman mara sa ƙarfi (talakawa)
kasancewar wannan zamani komai sai da kudi. Lalle wannan matsalar ta kawo cikas
sosai yayin gudanar da wannan bincike, musamman ga dalibai irin mu da ba su da
isasshen lokacin neman na kansu, sannan ga shi komai ya yi
tsada.
«
Rashin
isassun kayan aiki
An samu matsalar rashin littatafai da maƙalu da kuma kundayen
bincike waɗanda suka yi magana
kai tsaye a kan Hausar masu sana'ar lakum (wa'azin turmi) a wani gari, bisa ga
dukkan alamu wannan ne karon farko da aka fara gabatar da bincike a kan wannan ɓangaren
hakan ya haifar da wahalhalu masu tarin yawa wurin samun bayanai.
«
Rashin
samun haɗin kan waɗanda bincike ya shafa.
Wannan ma wani babban ƙalubale ne da aka
fuskanta, yayin tattara bayayanan wannan bincike, domin waɗansu mutanen
ba su bayar da amsa idan an tambaye su, saboda suna tunanin za a ɗauki sirrinsu a yaɗa wa duniya. Wannan
matsalar ta kawo tarnaki ainun a lokacin da ake gudanar da wannan bincike.
A takaice dai, waɗannan su ne kaɗan
daga cikin matsalolin da aka samu a yayin gudanar da wannan bincike.
1.5
MUHIMMANCIN BINCIKE
Alal haƙiƙa
harshe abu ne
mai muhimmancin gaske a
rayuwar ɗan'Adam, kasancewarsa
ɗaya daga
cikin abubuwan da ɗan'Adam ya
fi buƙata a
rayuwarsa. Harshe ne
tubalin ginin fannonin ilimi daban-daban,
ana amfani da
harshe musamman ma
harshen Hausa wajen
harkokin addini da sana'o'i
da tattalin arziki
a tsakanin al'umma.
Saboda haka ne
wannan binciken yake ganin
nazarin abin da ya shafi
harshe a cikin al'umma yana
da muhimmanci sosai
saboda waɗanda za su
amfana da shi ta
fuskoki da dama kamar:
v Wannan bincike
zai taimaka wa jami'an tsaro lokacin gudanar da binciken da ya danganci 'Yanlakum
da abokan hulɗarsu.
v Wannan
bincike zai taimaka wajen sanin ma'ana a zantukan 'Yanlakum.
v Wannan bincike
zai taimaka wajen ƙara samun abin nazari
ga masu bincike musamman a fagen ilimin walwalar harshe.
v Nazarin sara
muhimmin fage ne a fannin
ilimin walwalar harshe, wannan ne
ya sa manazarta ilimin
walwalar harshe za
su amfana da
wannan nazarin sosai,
domin za su ƙara fahimtar
tagomashin da harshen
Hausa yake da
shi.
v Zai taimaka
ga bunƙasa rumbun kalmomin Hausa.
v Ɗalibai masu
nazarin halayyar zaman
jama'a da walwalarsu
(sociology) za su
amfana da binciken a matsayin madogara wajen
fasalta maganar Hausawa da
harshen Hausa.
v Zai taimaki
masu ilimin tsara ƙamus da
manazarta ta hanyar
ba su gudummuwa
wajen samun sababbin kalmomi da
ma'anarsu.
v Wannan bincike
zai taimaka wa malaman addini yayin aiwatar da wa'azinsu.
v Wannan bincike
zai taimaka wa
mutanen da ke hulɗa da 'yanlakum ta hanyar naƙaltar yadda
'yanlakum ke sarrafa
harshe, hakan zai sa su fahimce su daidai gwargwado.
v Wannan binciken
zai taimaki gwamnati
ga tsare-tsarenta game
da harsunan Nijeriya
ta hanyar killace salon maganar
wasu rukuni a cikin al'umma.
1.6 HANYOYIN
GUDANAR DA BINCIKE
Domin haƙa
ta cimma ruwa, kuma kwalliya ta biya kuɗin sabulu. A yayin
gudanar da wannan bincike an yi amfani da manya kuma sanannun hanayoyin gudanar
da bincike. Wannan bincike an tsara shi ne domin a nazarci Hausar 'yanlakum ta
fuskar sara a cikin lafuzansu. Hanyoyin da
aka bi wajen tattara bayanan wannan bincike, an same su kai tsaye
ne, wasu kuma sai da aka kai ziyara
duk inda ya
dace tun daga ɗakunan karatu, da ziyartar shafukan yanar gizo
da wasu
hanyoyi da dama domin zaƙulo abubuwan
da suka shafi wannan nazarin. Hanyoyin da aka bi wajen tattara bayanan wannan
nazarim suna da dama daga cikin waɗannan mashahuran hanyoyi da aka bi ko
aka yi amfani da su sun haɗa da:
a. Bitar ayyukan da
suka gabata,
b. Ganawa ko zantawa
da masu wannan harka,
c. Ziyarar shafukan
yanar gizo,
d. ziyarar ɗakunan karatu
mabambanta
d. Sa ido da kuma lura (Observation).
1.7 RA'IN
BINCIKE
Wannan nazarin an ɗora shi ne
kan ra’ain da ake kira ra'in fage (field
theory) na Lehrer (1969). Ana amfani da wannan ra’in ne domin
fayyace irin canje-canjen da ake samu a cikin harshe, da yadda
ma’anar kalma kan
iya canzawa gaba ɗaya daga
ma’anar da aka
san ta. A kan
yi amfani da wannan ra’i wajen kwatancen harsuna kasancewar bambancin
da ake samu a
harsuna a sarari
suke tun daga
azuzuwan kalmomi, da muhallin da ake
samun kowace kalma. Kamar kalmomin da suka danganci yanayi na zafi, da muƙami,
da kaloli, da sunayen sassan jiki, da dabbobi da kayan marmari, da sauransu.
Field theory
by Lehrer (1969) that field theory can be used to illustrate language change.
The way semantic carved up and realized
in lexical items changes. It can also be used in contrastive analysis of
different languages. To illustrate how a given semantic area is
sub-divided similarly or differently in different languages. Languages often
differ even in apparently quite basic lexical division, and field such as temperature terms, kinship terms, colour terms, part of the
body and divisions of animal vegetable world will divide
the semantic space
differently and reflect this in
the vocabulary items covering those field.
Malmljar, K. (1991).
Wato wannan
ra’i ne na
rarrabe ma’ana a
tsakanin kalmoni domin
su dace da
muhallin da aka same
su sannan a
gano irin sauye-sauyen
da aka samu
a cikin harshe
da kuma yadda
suka taimaka wajen haɓaka
harshe. Har ila yau
wannan ra’i na
nuna dangantakar da ke tsakanin kalmomi ta
fuskar ma’ana. An yi
amfani da wannan
ra’i wajen nazarin Hausar
‘yanlakum domin a ga
irin canje-canjen da ake
samu na kalmomi a cikin harshe sakamakon
yunƙurin masu wannan sana’a ta Lakum.
Har ila yau wannan ra’in
ya samu karɓuwa ga waɗanda suka
bi wannan ra’i
irin su Gumperz, (1962),
da Lyons, (1970),
da Hudson (1980),
da Wales (1989), da Ahmed
(2015). Har aka gangaro zuwa
yanzu da wannan
bincike ya ɗauki
ra’in domin amfani
da shi wajen gudanar da wannan bincike.
1.8 NAƊEWA
Wannan babi da ya
gabata, wato babi na ɗaya, babi ne da aka tattauna game da abubuwa
da dama, kamar manufar wannan bincike, ko kuma dalilin aiwatar da wannan
bincike, sannan an tattauna akan farfajiya ko kuma a ce kadadar bincike, sai
hasashen bincike, da matsalolin bincike, da muhimmancin bincike, da hanyoyin
gudanar da bincike, da ra’in bincike, daga ƙarshe aka zo
da naɗewa.
BABI NA BIYU
2.0 BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA
Hausawa na cewa
waiwaye adon tafiya, kuma da na gaba ne ake gane zurfin ruwa. Don haka a wannan
babi na biyu mai taken bitar ayyukan da suka gabata, babi ne da yayi waiwaye a
kan ayyukan da suka gabata waɗanda masana da manazarta da dama suka
gudanar a shekaru mabambanta. Haka zalika, a karkashin bitar ayyukan da suka
gabata, an tattauna a kan abubuwa uku zuwa huɗu waɗanda suka haɗa da; duba
bugaggun littattafai da kundayen bincike da kuma maƙalu, da
mujallu waɗanda hannu ya
kai gare su. Kafin nan an taɓo ma'anar harshe, karin harshe, karin
harshen rukuni, da kuma dangantakar harshe da al'umma. Ko shakka babu, wannan
babi zai ƙara haska mana fitila a kan wannan bincike da
ake ƙoƙarin
aiwatarwa.
2.1 BUGAGGUN
LITTATAFAI
An yi ayyuka da dama
na wallafaffu ko bugaggun littatafai da masana da manazarta da kuma masu
bincike suka wallafa masu alaƙa ta kusa da
ta nesa da wannan aiki ko bincike kaɗan daga cikin irin waɗannan
wallafaffun littatafai akwai:
Salihi, T. M. (2012)
a cikin littafinsa mai suna "Sakace A kan karin Harshen Hausa", marubucin
littafin ya rubuta abubuwa da dama, inda ya yi bayani a kan ma'anar harshe da
ma'anar karin harshe, da bambanci tsakanin harshe da karin harshe.
Haka kuma ya tattauna a kan matakan da ake bi wajen fito da bambancin harshe da
karin harshe da dai sauransu.
Bugu da ƙari,
a cikin littafin ya yi magana a kan tsarin matsayi a cikin al'ummar Hausawa,
karin harshen zamantakewa ko matsayi, da kare-karen harshe na matsayi na sana'a
wanda a nan ne ya kawo ire-iren Hausar masu sana'a kamar haka:
1. Hausar masu gyaran
Wayar Salula.
2. Hausar Mahauta.
3. Hausar masu
Gurasa.
4. Hausar ‘Yan
Karta.
5. Hausar Ɗalibai.
6. Hausar ‘Yan tasha.
7. Hausar ‘Yan
caca.
8. Hausar Maƙera.
9. Hausar Yan sanda.
10. Hausar Teloli.
11. Hausar Manoma.
12. Hausar Yan daba,
da kuma
13. Hausar Direbobi.
Salihi, (2012).
Saboda haka, wannan
littafin yana da alaƙa ta ƙut-da-ƙut
da wannan bincike domin an yi tsokaci a kan Hausar rukunin al'umma da dama.
Saboda haka suna da alaƘa da juna kasancewar
dukkaninsu sun yi magana a kan Hausar wasu rukunan al'umma a cikin Hausawa.
Yakasai, S. A. (2012)
a cikin littafinsa mai suna "Jagoran Ilimin Walwalar Harshe" wanda ya
rubuta a tsarin babi-babi inda ya rarraba littafin har babuka ashirin (20). A
cikin littafin, marubucin ya yi tsokaci a kan harshe da al'ada, da ma'ana da
nau'o'in jinsi. Ya yi magana a kan yanayi da tsarin sadarwa da dai sauransu. A
babi na takwas (8) na littafin mai taken "Dangakatar Harshe Da Rukunan
Jama'a" marubucin ya yi magana a kan yanayi da tsarin rukunin jama'a, salo
cikin dangantakar harshe da rukunin jama'a da harshe. Marubucin ya kawo
nau'o'in Hausa kamar haka;
1. Hausar Kasuwanci.
2. Hausar Mawaƙa.
3. Hausar Sarakuna.
4. Hausar Malamai.
5. Hausar Dattijai.
6. Hausar Matan aure.
7. Hausar Gidan
Magajiya
8. Hausar wurin zaman
makoki.
Yakasai,
(2012).
Saboda haka, wannan
littafin yana da alaƙa da wannan bincike.
Dalili a nan shi ne, a cikin littafin an yi magana a kan nau'o'in Hausa na wasu
rukunan jama'a.
Fagge, U. U. (2001).
Ya rubuta littafi mai suna"Ire-iren Karin Harshen Hausa na Rukuni"
wanda shi ma wannan littafin yana da nasaba da wannan aikin sai dai, ba irin sa
ba ne. A littafin, an yi tsokaci a kan nau'o'in Hausar rukuni da dama da kuma
sauran abubuwa da dama. A littafin, marubucin ya yi tsokaci a kan nau’o’in
Hausar rukunin jama’a da dama. Wannan ne ya nuna ayyukan suna da nasaba sosai
da sosai.
2.2 KUNDAYEN
BINCIKE
Salihu, N. A. (1987)
ya rubuta kundin bincike mai Taken "Code Switching among University of
Sokoto Hausa English Bilingual". An yi shi ne harshen Ingilishi wanda yake
magana a kan Ingausar Hausar da ɗalibai ke yi a yayin da suka fara yin
magana da Harshen Hausa amma daga ƙarshe a ƙarasa
da Harshen Ingilishi inda ya kawo misalai kamar haka;
Misali:
(a). Gaskiya i don't
like abun da kake yi man.
(b). Akwai wata close friend ɗinmu, we are
family friends'...."
(c). Gaskiya abin da Umar ya yi is not good at
all.
(d). Muna da exams tomorrow.
Dangantakar wannan
aikin da binciken Salihu ita ce, dukkan su an yi su ne a kan Hausar rukuni na
wasu jama’a kuma ɓangaren
harshe.
Yahaya, S. (1998) a
cikin kundin digirinsa na farko wanda ya gabatar a Sashen Nazarin Harsunan
Najeriya a Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo
Sakkwato mai taken "Hausa a Jami'a".
A cikin wannan kundin
bincike, manazarcin ya kawo misalan Hausa a jami'a kamar haka;
ƊALIBAI MAZA.
(a). ƘWARO:
Yana nufin ɗalibi mai ƙwazo.
(b). JIRGI:
Yana nufin Risho(Stove) na dafuwar abinci.
(c). WANKI:
Satar amsa ko juya aikin wani kalma zuwa kalma.
(d). AHLUL KITAB:
Ɗalibin da a
kodayaushe yake tare da abin karatunsa yana karatu.
(e). FARIN-WATA:
Na
nufin samun wata ‘yar matashiya game da abin da zai fito a
wajen Jarabawa.
ƊALIBAI MATA.
(a). MALAM MAI JAR
HULA:
A wajen mata yana nufin jinin al'ada.
(b). ADAMA:
Na nufin mace mai yawan tsegumi.
(c). FARFAƊIYA:
Na nufin mace mai yawan faɗuwa, ma'ana mai yawan zina.
(d). B.Z (widow):
Ana nufin bazawara, wato wadda ta yi aure ta fito.
(e). B.G.Z
(Ballegaza-Disorganise woman)
Suna nufin mace marar
kimtsi da kamun kai da dai sauransu.
Akwai alaƙa
ta ƙut-da-ƙut a tsakanin
aikin Yahaya (1998) da wannan bincike, dalili kuwa shi ne dukkaninsu sun keɓamta a ɓangaren
harshe, kuma an yi nazarin su ne a kan Hausar rukuni na wasu mutane.
Muntari, H. (2008) A
binciken da ta gudanar mai taken "KarinHarshe Na Rukuni A Hausa: Nazari A ƙasarZazzau".
Kundin Digiri Na biyu. Sashen Harsuna
Da Al'adun Afrika Zariya: Jami'ar
Ahmadu Bello. Ta fara ne da kawo tarihin ƙasar Zazzau a
taƙaice da kuma bayanin karin harshen rukuni da
dalilan da suke kawo karin harshen. Ta duba rukunoni da dama na masu sana'o'i
mabambanta a ƙasar Zazzau, ta nazarci Hausar Asibiti da
Hausar ‘Yan acaɓa da Hausar
Fada da Hausar Kotu da Hausar Mahauta. Ta kawo misalai na kalmomin da aka ƙirƙira
ga kowanne rukuni su ke amfani dasu, waɗanda suka keɓanta ga
wannan rukuni kawai.
Binciken nata ya yi
kama da wannan domin ta kalli rukunin wasu masu sana'a ne, da yadda suke samar da
kalmomi da jumloli sababbi a harshe. Haka ma wannan yana ƙoƙarin
bayanin yadda masu sana'ar lakum ne, ke samar da kalmomi da jumloli domin bunƙasa
harshen Hausa.
Ahmad, H. ( 2015) A
cikin kundin neman digirinsa na biyu da ya gabatar a Sashen Nazarin Harsuna Da
Al'adun Afirika, Tsangayar Fasaha, Jami'ar Ahmadu Bello Zariya. Mai taken karin
harshen rukuni, nazarin Hausar masu sana'ar kayan gwari a garin Zariya. A cikin
aikin nasa ya kawo tarin kalmomi da wannan rukuni na masu sana'ar kayan gwari
suka ƙirƙira da waɗanda suka faɗaɗa
ma'anarsu.Ga misalin wasu daga cikinsu
kamar haka:
Kalma Ma'ana
v Ƙwara
-- -- Albasa mafi kyau
v Gwarama
-- -- Mutum mai rigima da yawan cin bashi.
v Fiya -- ƙaramin
buhun Zuba tattasai.
v Solo -- Babban
buhu mai cin Kwando ashirin.
v Gwalagwaji --
Ruɓaɓɓen tumatir ko
tattasai.
Wannan bincike da ake
gudanarwa yana da alaƙa da binciken Ahmad,
H. dalili kuwa shi ne dukkaninsu an yi su ne a kan abin da ya shafi harshe na
rukunin wasu mutane masu aiwatar da wata sana'a a cikin Hausawa.
Yero, Z. S. (2017). A
cikin kundin digirinta na biyu da ta gabatar a Sashen Nazarin Harsuna Da Al'adun
Afirika, Tsangayar Fasaha, Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya. Mai taken Hausar yaran
mota a garin Zariya, a cikin aikin nata ta yi bayanin yaran mota da ayyukansu
da kuma abokan hulɗarsu, sannan ta kawo kalmomin da suka samar a
rukuninsu, tun daga waɗanda suka ƙirƙira
da na aro da waɗanda aka faɗaɗa ma'ana da
dai sauransu. Ga misalin wasu daga cikinsu:
Kalma Ma'ana
v Garau -- -- -- Tsohuwar
mota.
v Awiizoo-- -- wasa da mota kan titi.
v Fyau -- -- -- Sabuwar
mota.
v Kaco -- -- -- Ɗan
kwaya.
v Garau-garau--
Sabuwar mota.
v Gudubale -- -- Babbar mota mai buɗaɗɗen baya.
Bayani
v Garau: yaran mota na kiran tsohuwar mota da garau.
Kuma kalma ce da suka ƙirƙira
domin amfani da ita a tsakaninsu.
v Awizo: kalma
ce da yaran
mota suka ƙirƙira kuma
suke amfani da
ita wajen irin wasan ganganci da direbobi ke yi da
mota a kan titi.
v Fyau: kalma
ce da yaran
mota suka ƙirƙira kuma
suke amfani da
ita wajen kira ko nuna
cewa kuɗi sabon fitowa
daga Banki ne ko lanƙwashewa bai yi
ba.
v Kaco: suna
ne da suka ƙirƙira suna
kiran wanda ke
shan ƙwaya da
sunan Kaco.
v Garau-garau: suna
ne da suka ƙirƙira suna
kiran tsohuwar mota
wadda ba a morar ta
sosai.
v Gudubale: suna
ne da yaran
mota suka ƙirƙira suna
kiran babbar motar ɗaukar itace.
waɗannan
kalmomin da suka gabata, kalmomi ne waɗanda yaran mota
suka ƙirƙira suke kiran wasu abubuwa waɗanda
suka danganci sana'arsu, ko dai
ta la'akari da sifar abun ko kuma ta la'akari da
halayyarsa, ko kuma don kawai
suna ganin sunan da ya dace
da su kenan.
Waɗannan ayyuka
biyu suna da dangantaka sosai da sosai, domin dukkaninsu sun shafi ilimin
walwalar harshe kuma an yi su ne a kan Hausar wani rukuni na wasu mutane a
cikin Hausawa.
Abdulƙadir,
M. (2018) A cikin kundin bincikensa na neman digiri na farko mai taken
"Hausar Rukunin 'Yan Banga A Garin Gusau" wanda ya gabatar a Jami'ar
Tarayya Gusau, Sashen Nazarin Harsuna Da Al'adu. Shi ma wannan kundin binciken
yana da alaƙa da wannan binciken. Kasancewar dukkaninsu
an yi su ne a kan harshe kuma a ɓangaren ilimin walwalar harshe wanda
ya shafi Hausar rukuni. A cikin kudin bincikensa, manazarcin ya kawo Hausar yan
banga kamar yadda za mu gani a nan;
KALMOMI.MA'ANA
v Sabce:Na
nufin kayan sata a wajen yanbanga.
v Sabci-faɗi:
Bulalace irin ta dorina.
v Tambaya:
Na nufin maganin tsarin jiki ko buwaya.
v Mugu:A wajen
yanbanga yana nufin ɓarawo.
v Makuba: A wajen 'yanbanga ana nufin wurin zaman 'yan daba ko masu aikata laifi.
Dangantakar wannan
kundin binciken da wancan kundin binciken ita ce dukkansu suna a ɓangaren
harshe, kuma ko a ɓanagren harshe duk sun shafi Hausar rukuni na
wasu al’umma waɗanda ke zaune
ko suke rayuwa a Gusau.
Tukur, A. (2020) a
Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsuna da Al'adu,
Jami'ar Tarayya Gusau. Mai taken: "Hausar masu sana'r waya a garin
Gusau". Manazarcin ya yi bayanai masu tarin yawa, kamar ma'anar wayar
salula, ire-iren waya, wuraren da ake sayar da waya na da da na yanzu a garin
Gusau, da dai sauran abubuwa da dama. Sannan ya kawo kalmomin da masu sana'ar
waya suka ƙirƙira kuma suna
amfani da su ga kaɗan daga ciki:
-- Kalma
-- --
-- Ma'ana
1) Ƙetare -- -- Kada
ka sayi waya.
2) Kilin Waya mai kyau.
3) Guduma Ƙatowar waya.
4) Jagwal -- waya
marar lafiya.
5) Sumuni Dubu ɗari.
6) Ƙundu
Bandur na kuɗi.
Wannan kundi yana da
alaƙa sosai da na Tukur, A. (2020) domin kuwa duk
suna magana ne a kan Hausar rukunin wasu al'umma ne a cikin garin Gusau.
2.2.1 Muƙalu Da
Mujallu
Abubakar, I. A.
(2001) ya rubuta muƙala a kan Hausar
gardawa a cikin birnin Kano da kewaye. Gardawa su ne almajirai da suka girma
suka kai lokacin gardanta. Wato bayan shekara 28 sun haddace Alƙur'ani
tare da iya rubuta shi. Ya kawo misalai na kalmomi da ma jumloli da suke amfani
da su domin sadarwa. Akwai alaƙa sosai
tsakanin aikin Abubakar da wannan aiki da ake yi. Domin duk sun yi tsokaci a
kan Hausar wani rukuni na jama'a.
Fagge, U. U.
(2002:99-101), ya bayyana cewa akwai wani salon magana da zawarawa suke yi.
Binciken ya nuna cewa su dai zawarawa a sanadiyar lokutan da suka ɗauka a gida
kafin su samu damar yin wani aure shi ne yake haifar da ire-iren karin harshen
da ake samu a tsakaninsu. Ga wasu misalansu kamar haka:
Kalma -- Ma'anar
yau da kullum Sabuwar ma'ana
v Ɗan-birni
-- wayayye Matashin saurayi
v Kwasa -- -- Ɗibar
wani abu Aure
v Ƙarfe -- -- Ƙarfe
-- -- Marowaci
v Tulu -- -- Abin
zuba ruwa Mai ƙaton ciki
Haƙiƙa,
akwai abubuwa da dama da karin harshe ya haifar ga wannan rukunin na Hausawa.
Kaɗan daga
cikinsu akwai, azanci wanda ya bai wa zawarawan damar sarrafa harshen Hausa ta ɓangarori
daban-daban, wanda yin hakan kan jawo sanya wa wani abu suna, kuma ma'anar ta
dace, kuma ta zauna daram ba tare da haifar da wata matsala ba a harshe. ko
shakka babu waɗannan ayyukan
biyu suna da dangantaka sosai.
Musa, A. (2011:273)
ya gabatar a kan Karin harshen Hausar niga ya fara da bayar da ma'anar
Hausa-Niga inda ya bayyana cewa wani rukuni ne na matasa Hausawa masu haɗin gambiza na
al'adu biyu Watau, al'adunsu na Hausa da na aro na Nigan Amerika, wanda suke
gani a fina-finan sinima da satilayi (dish) da bidiyo. Ya cigaba da cewa bayan
al'adunsu na asali. Hausa-Niga sun ƙirƙiri
sababbin kalmomi na sadarwa a tsakaninsu. Kuma waɗannan kalmomi
suna yin tasiri a tsakanin sauran matasa, kuma har suna samun karɓuwa da bunƙasa.
Ya yi nuni da ɗabi'un
Hausa-Niga da cewa aske kai ƙwalkwabo yana
ƙyalli. Amma suna da shiga ta asali ta
Hausawa.
Akwai kuma shigarsu
ta Amerika-Niga Watau, T-shat marar hannu mai kama da singileti ko shat da
wando jins koɗaɗɗe ko mai jiki
duk faci ko wanda yake kira cinos mai aljihu barkatai daga sama har ƙasa,
ga yin zanzaro, da ƙaton takalmi sawu
ciki (but), ko waje ko kambas. Wani lokaci Niga kan sa sarƙa da ɗankunne.
Hausa-Niga sun ƙirƙiri kalmomin
sadarwa waɗanda suka keɓanta da
rukuninsu na matasa. Misali:
Kalma -- -- Ma'anar
asali -- Ma'ana wurin Hausa niga
v Tsami --
Ɗanɗano mai tsami Rashin wayewar kai
v Haɗuwa -- Gamuwa -- Yin
ado
v Sharewa -- Kauda
datti --
-- Mantawa/ Ƙyalewa
v Mai
tsada Marar sauƙi ƙyaƙƙyawa
v Django Suna Mahaifi
Waɗannan Ayyukan biyu sun yi kama da juna domin dukkaninsu nazari ne a kan Hausar wani rukuni na al 'umma, sannan
kuma suna ƙirƙira kalmomi
da jumloli da suke amfani da su a cikin rukuninsu.
Munnir (2010)
ya yi nazarin
Hausar 'yan tasha
a garin Gusau
da ke cikin
jihar Zamfara. Ya nazarci
yadda suke faɗaɗa ma'anar
kalmomi, da yadda
suke juya guraben
haruffa a cikin kalma
ba tare da
ma'anar kalma ta canza
ba. Wannan aikin yana da
dangantaka da wanda
za a yi kasancewar
duk a kan
sarrafa harshe ne.
Yakasai, S. A. (2010)
ya yi nazarin dangantakar harshe da muhallin magana. Ya
nazarci yadda ake magana
ko taɗi a
al’adar Hausawa da
kuma tsarin da
ake bi wajen
aiwatar da maganar
ko taɗi. Ya
bayyana abubuwan da kan zo
a zuciyar mutum
a duk lokacin
da zai yi
magana ko taɗi, ko bayar
da umurni. Waɗannan abubuwa
sun haɗa da:
v Darajar mai
sauraro a idanun mai magana.
v Abin da ake magana ko hira a kai.
v Wurin da ake gudanar da hulɗoɗi.
Wato ba haka nan
kawai ake yin magana ba. Kowacce magana
tana da zubi da tsari. Wannan ya nuna cewa akwai zumunta tsakanin waɗannan ayyuka
biyu.
Azare, Y. M.
(2011:224) ya bayyana cewa mata na amfani da wasu nau'in kalmomin harshe domin
sadarwa a tsakaninsu, ta yadda ba kowane mutum kan fahimci ma'anar da suke nufi
ba. Ya kalli rukunonin mata da dama, daga matan aure masu ilimi (boko ko
mahammadiya da marasa ilimi, sai mata marasa aure wato, 'yan mata masu ilimi na
sakandare da 'yan jami'a da 'yan islamiya da kuma marasa ilimi kamar 'yan
talla, sannan zawarawa da kuma karuwai. Kasancewar kowane rukuni na da irin
Hausar da suke amfani da ita domin sadarwa a tsakaninsu. Misali:
Kalma/Yankin
jimla -- -- Ma'anarta a wurin matan
v Sayar da
manja Jinin al'ada.
v Rijiya gaba
dubu Mace mai yawan aure.
v Daƙiƙi
Ragon namiji.
v Sandar girmaAl'aurar
namiji.
v Burodi
Audugar al'ada.
v Wancan magana Jima'i/ saduwa.
A ƙarshe,
ya nuna cewa ko tantama babu domin kuwa a kan sami sauyi a harshe ta la'akari
da yanayin hulɗoɗin al'umma,
wanda kan haifar da ƙirƙirar
harshe, wato karin harshe domin ya dace da hali ko yanayin da ake ciki. Wannan
kan haifar da samuwar sababbin kalmomi waɗanda daga baya sukan
koma ga al'umma. Watau, al'umma su zaɓi waɗanda za su
rika amfani da su, su kuma yi watsi da wasunsu. Alaƙar wannan
aiki da wanda ake gudanarwa ita ce, sun kasance suna magana game da karin
harshen rukuni.
Adamu, S. (2022) ya
rubuya muƙala mai taken kalmomin teloli a garin Gusau a
cikin aikin manazarcin ya kawo ma'anar tela da kashe kashen teloli ta fuskar
kayan aiki da kuma ta fuskar muhallin da suke aiki, baya ga wannan kuma ya kawo
wasu kalmomi da suka ƙirƙir
kuma suke amfanin da su a ɓangaren maza da na mata ga misalin
wasu daga cikinsu kamar haka:
NA MAZA
Sace: Babbar riga
ce ta sarakuna da manyan mutane (dattijai da attajirai). Ana yi mata shuggai
irin na Yar-shara.
Gare: Ita ma
babbar riga ce wadda mafi akasari matasa kan sa. Shigganta a jirge ake yanka
su, sama ya fi ƙasa faɗi.
Shakwara: Wannan ma
babbar riga ce wadda ake yanka shiganta faɗi ɗaya daga sama
zuwa ƙasa.
Yar-Bunguɗu: Wannan
babbar riga ce wadda ake ɗinkawa da ƙoran saƙi,
na saƙar hannu.
Wuyan-Wundi: Nau'in ɗinki ne da ake
yi wa babbar riga zagayayyen wuya, mai aiki ko maras aiki. Duk nau'o'in manyan
riguna ana iya yi musu wuya wundi.
Yar-Shara: Nau'in rigar
maza ce wadda mafi akasari guntuwa ce zuwa guwayyu, tana da shiggai amma ba ta
da hannuwa.
Ɗan-itori: Wando ne
wanda ake yi wa ƙarin hantsa daga wannan idon sawu zuwa
wancan.
Tsala mai
bulala: Wando
ne wada ake yi wa ƙarin hantsa daga
guiwa zuwa guiwa. Kuma ana yi masa taki gefen aljifai daga sama zuwa ƙasa
wanda ake kira fitsarin bajini.
Na Annabi ya
zo kasuwa:
Nau'in ɗinki ne wanda
ake yi wa riga aljifai guda biyu hagu da dama, kuma aljifan wajen rigar ake
manna su.
Sardauna a
ofis:
Nau'in ɗinki ne wanda
ake lanƙwaso wani ƙyalle a yi
masa tsini a wuyan hannun riga a take shi da ɗinki.
NA MATA
Buba: Rigar mata ce
mai zagayayyen wuya, wadda ba a yo wa kwalliya. Mafi akasari tsofaffi suka fi
saka ta.
Agwada: Babbar riga
ce ta mata mai zagayayyen wuya, ana take gefen hamata zuwa ƙasa
kaɗan na hagu da
dama. Wasu kan yi mata kwalliya wasu kuma ba sa yi.
Amaliya: Babbar riga
ce, amma iyakacin ta bakin guiwa.
Amburela: Nau'in rigar
mata ce mai shan bance, kuma gajeruwa ce ƙwarai ba ta
kai guiwa ba, amma ƙasanta yana da faɗi. Hannuwanta
ƙanana ne, an yi ma wuyan zugen atamfa ko
barnina.
Baba na isa
aure: Riga
ce gajeruwa mai wuya mai faɗi da kan bayyana sassan nonuwa.
Zura hannunka
masoyi:
Riga ce wadda hannunta ba ya rufe hamata kuma gajeruwa ce.
Umar, M. M. &
Abbas, N. I. (2020). Sun rubuta wata mujalla mai taken Nazarin Hanyoyin Samar
da Hausar Wasu Rukunan ‘Yan Kasuwa a Cikin Garin Sakkwato a cikin aikin nasu
manazartan sun yi bayanin Hausar kasuwanci inda suka ce "Hausar kasuwanci,
Hausa ce da
take ƙunshe da
kalmomin fannu waɗanda
suka shafi kayayyakin
da 'yan kasuwa ke
sayarwa, da yadda
suke gudanar da hulɗar kasuwanci
tsakaninsu da masu
sayen kaya da
sauran 'yan kasuwa.
A taƙaice,
ana iya cewa
Hausar kasuwanci karin
harshen rukuni ne
na musamman da
ya keɓanta ga
'yan kasuwa da
masu sana'o'i wadda ke
bayyana yadda suke
amfani da Hausa
a sadarwarsu ta
yau da kullum.
Misali, da zarar
'yan kasuwa sun yi
wa juna irin
wannan Hausa za
ka ga sun
san abin da
suke nufi. Fagge
(2004) ya ce,
“Bisa ga al'ada
'yan kasuwa kan yi
amfani da wani nau'in harshe
a tsakaninsu don
tafiyar da hankulan
masu sayen kaya.” Hanyoyin Samuwar Hausar Wasu Rukunan
‘Yan kasuwa a Cikin Garin Sakkwato.
1. Faɗaɗa Ma’anar
Kalmomi
v Faɗaɗa ma’anar
kalmomin asali
v Faɗaɗa ma’anar
kalmomin aro
2. Ƙirƙira
v Ƙirƙira daga
kalmomin asali
v Ƙirƙira sabuwar
kalma da babu
ita a da
a harshen Hausa
v Ƙirƙira ta haɗin gambizar
kalmar asali da ta aro
3. Sarrafa
Kalmomin Aro
v Sarrafa
kalmomin Larabci
v Sarrafa
kalmomin Ingilishi
Kalma -- Ma'ana
-- -- Ma'ana ta asali
v Takalmi -- wurin aza ƙafa na babur -- Abin kare tafin ƙafa daga rana ko ƙaya.
v Katawa babur wanda ya tsufa -- Tarkon ƙarfe na kama ɓera.
v Haɗi Canja wa ƙaramin babur inji Gauraya wani abu da wani.
v Kura Dillalin dake ƙayyade -- -- Dabbar daji. kuɗin la'ada
v Baƙoo Mai sayen kaya -- -- Mai ziyara ko sabon abu.
Waɗannan ayyuka
biyu suna da alaƙa ta kut-da-kut, domin suna magana ne a kan
karin harshen rukunin wasu mutane.
2.2.2 Hujjar Cigaba Da Bincike
Idan aka yi duba ga
bayanan da suka gabata, a inda muka yi tankade da rairaya a kan ayyukan da aka
aiwatar, a kokarinmu na kwatanta kudurin wannan nazarin da abin da magabata a
fagen nazari suka aiwatar, za mu fahimci cewa, har zuwa yanzu ba a ci karo da
wani bincike da aka gudanar dangane da Hausar 'yanlakum, ko da a wani gari saɓanin garin
Gusau ba. Wannan dalili ne ya tabbatar muna da cewa, an bar wani babban giɓi da ke
bukatar cikewa, musamman a ɓangaren ilimin walwalar harshe.
Littafin Salihi
(2012). Yana da alaƙa taƙut-da-ƙut
da wannan bincike domin a cikin littafin an yi tsokaci a kan Hausar rukunin al'umma
da dama. Ayyukan suna da alaƙa da juna kasancewar
dukkaninsu sun yi magana a kan Hausar wasu rukunan al'umma a cikin Hausawa. Haka
kuma, sun bambanta da juna domin a littafin ba a yi magana a kan Hausar
'Yanlakum ba, amma, shi wannan binciken an yi shi ne a kan Hausar 'Yanlakum a
garin Gusau.
Haka zalika littafin
Yakasai (2012). Shi ma yana dangantaka da wannan bincike sosai da sosai,
kasancewar dukkaninsu sun yi tsokaci a kan Hausar rukunin wasu al'umma. To amma
sun sha bamban, saboda shi wannan bincike an yi shi ne a kan nazarin Hausar 'Yanlakum
a garin Gusau kawai.
Bugu da ƙari,
littafin Fagge (2001) shi ma yana da alaƙa da wannan
bincike na nazarin Hausar 'yanlakum saboda dukkaninsu sun yi magana a kan
Hausar rukunin wasu mutane a cikin Hausawa. Sai dai abun da ya bambanta su shi
ne fagge bai yi magana a kan Hausar 'yanlakum ba kamar yadda wannan bincike ya
yi.
Alaƙar
binciken Salihu (1987), da wannan binciken ita ce dukkansu an yi su ne a kan Hausar
rukuni na wasu jama’a kuma a ɓangaren harshe. Abin da kuma ya bambanta
su shi ne, wancan aikin an yi shi ne a kan Ingausar Hausar da dalibai ke yi a Jami’a.
Yayin da wannan aikin an yi shi ne a kan Hausar masu sana’ar lakum a Gusau.
Akwai alaƙa
ta ƙut-da-ƙut a tsakanin
aikin Yahaya (1998) da wannan nazari, dalili kuwa shi ne, dukkaninsu an yi su a
ɓangaren harshe,
kuma an gudanar da su ne a kan Hausar rukuni
na wasu mutane.
Amma wurin da suka farraƙa
kuwa shi ne, a wancan kundin binciken an yi nazari a kan Hausar ‘Yan Jami’ar Usmanu
Ɗanfodiyo Sokoto. A wannan kundin binciken kuma,
ana nazari ne a kan Hausar 'Yanlakum a garin Gusau
Binciken Ahmad, H.
(2015) bai zo daidai da wannan ba, domin
an yi shi ne, a kan Hausar masu sana'ar kayan gwari a zariya, shi kuma wannan
aiki ana aiwatar da shi a kan Hausar masu sana'ar Lakum a garin Gusau.
Aikin Zainab, S. Y.
(2017) ya bambanta da wannan domin aikin Zainab an yi shi a kan Hausar yaran mota
a garin Zariya. Wannan kuma ana gudanar da shi a kan Hausar 'Yanlakum a cikin garin
Gusau.
Haka zalika, abun da ya
bambanta aikin Abdulkadir (2018) da Wannan shi ne, Abdulkadir yayi
aiki a kan Hausar Rukunin ‘Yan Banga a garin Gusau. Yayin da shi kuma wannan binciken
an yi shi ne a kan ‘’Hausar Rukunin 'Yanlakum a garin Gusau’’.
Kundin Tukur, A (2020) ya sha bamban da
wannan, domin wannan ana yin shi ne a kan Hausar 'Yanlakum
a garin Gusau shi kuma wancan an yi shi ne a kan Hausar masu sayar da waya
a garin Gusau.
Aikin Abubakar (2001) ya bambanta da wannan
nazari domin shi ya yi nasa aiki a kan Hausar gardawa a garin kano.
Fagge (2002 : 99-101) ya yi aiki a kan salon
maganar zawarawa.
Musa (2011 : 273) ya yi bincikensa a kan
Hausar Hausa-niga.
Munir (2010)
ya yi aiki a kan Hausar 'yan Tasha a garin Gusau.
Yakasai (2010) ya yi nazarin dangantakar
harshe da muhallin magana.
Azare (2011: 224) ya yi aiki a kan Hausar
rukunin mata daban-daban daga matan aure, zawarawa, 'yan talla, da sauran su.
Adamu, S. (2022) ya rubuta muƙala mai taken "kalmomin teloli a garin Gusau.
Umar, M. M. &
Abbas, N. I. (2020), sun rubuta wata mujalla mai taken "Nazarin Hanyoyin
Samar Da Hausar Wasu Rukunan 'Yan Kasuwa a garin sakkwato.
Idan aka yi la'akari
da bayanan da suka gabata za a fahimci cewa, bincike a kan"Nazarin Hausar
'YanLakum A Garin Gusau" yana da hujjar da za a ci gaba da gudanar da shi.
Saboda bitar ayyukan da magabata suka yi, da kuma sauran ayyukan da suka gabaci
wannan bincike, su suka tabbatar da hakan.
Saboda duk da cewa an
yi ayyuka da dama da suka gabaci wannan aiki masu alaƙa da shi ta
kusa da ta nesa, to amma ba a samu wani aiki da zo daidai da wannnan bincike
ba, na nazarin Hausar 'yanlakum musamman a garin Gusau.Wannan dalili ne ya
zaburar da wannan bincike domin cike gurbi ko giɓin da masana
da manazarta da ɗalibai
'yan'uwa suka bari domin amfanin al'umma baki ɗaya.
2.2.4 NAƊEWA
A wannan babi na biyu
bayan an yi shimfiɗa, an tattauna a kan muhimman abubuwa da dama
kamar bitar ayyaukan da suka gabata da kuma hujjar ci gaba da bincike. A ƙarƙashin
bitar ayyukan da suka gabata, an yi tsokaci a kan abubuwa uku zuwa huɗu kama daga
bayanai daga bugaggun littattafai da kundayen bincike. Daga ƙarshe
kuma, aka yi bayani a kan wasu muƙalu da
mujallu masu alaƙa da wannan kundin bincike, domin samun tudun
dafawa.
BABI NA UKU
FASHIN BAƘIN
MA'ANONIN KALMOMIN
DA SUKA SHAFI LAƘABIN
BINCIKE
3.1 SHIMFIƊA
A wannan babi na uku mai suna
fashin baƙin kalmomin da suka shafi laƙabin
bincike, za a duba ma'anonin kalmomin da suka fito a cikin laƙabin
bincike domin fahimtar abin da suke nufi, sannan za a duba kashe-kashen 'Yanlakum
da kuma wasu daga cikin dabarun da suke yi a lokacin gudanar da wannan sana'ar
tasu domin karɓar kuɗi a wurin al'umma, daga
karshe a zo da naɗewa.
3.2 MA'ANAR NAZARI
Nazari zai iya ɗaukar ma'anar ayyuka dabam -
dabam da da ake aiwatarwa da manufar samun sani (ilimi), ko fahimtar wani batu,
ko kuma shiri domin gwaji ko jarabawa. Nazari yana bukatar aiki tukuru da
lokaci da lura sosai domin samun nagartattun bayanai, da bunkasa kwarewa, ko
kuma zurfafa fahimta a wasu ɓangarora na rayuwa da ake da buƙatar yin
hakan.
Sau da yawa ana dangantaka
nazari da ilimin boko inda ɗalibai da Malamai da masana suke bibiyar wasu
batutuwa na ilimi a makarantu da kwalejojan ilimi da jami'o'i domin gano ainihin
haƙiƙanin yadda waɗannan batutuwa su ke. Ta
hanyar karatun littatafai, tambayoyi, ƙwanƙwance bayanai, tattaunawa,
bitar ayyukan da suka gabata, da kuma tattara bayanai wuri ɗaya.
A wata mahangar kuma idan an
ce nazari to ana nufin zurfin tunani da hangen nesa domin gano hanyar shawo kan
wata matsala, ko kuma sanin wani abu da ya shige wa mutane duhu.
3.3 MA'ANAR KALMAR HAUSA
Masana da dama kuma a shekaru
mabambabanta sun tofa albarkacin bakinsu dangane da ma'anar kalmar Hausa, kaɗan daga cikinsu akwai:
Zarruƙ da
Wasu (1986:l6) sun
bayyana "Hausa‟ kamar
haka: “Koda yake can farko,
akwai ƙabilar Hausa.
Duk da haka
a yanzu wannan
suna ya zamana harshe,
ba na ƙabila ba.
Domin idan aka
ce ƙabila, ana
nufin al'umma mai asali
ɗaya da
yare ɗaya da ƙirar jiki
kusan iri ɗaya
da al'adu iri ɗaya da
falsafa ko ra'ayin zaman
duniya iri ɗaya.
Bayan haka kowa
cikin al‟ummar zai riƙa alfahari shi
ɗan ƙabilar ne.
Hausawa sukan ce su ƙabila ne. To
amma idan ka
matsa tambaya, za ka
ji haifaffen ƙasar Hausa
ya ce maka
asalinsa shi Bafilatani
ne, ko Babarbare ko
Banufe ko Buzu
ko dai ɗan
wata ƙabila daban.
Ga shi kuma a
wannan ƙabilar bai
san ko sannu
ba. Bayan haka
wannan kalmar Hausa
a wurin Bahushe ma'anarta
"harshe‟.
Idan aka yi
magana da wani
harshen daban, Bahaushe yakan
ce yana ji
ana wata Hausa.
Wato a nan
ka ga Hausa
sunan harshe ne ba na ƙabila.
Al'ummomin da
suka taru suke
yin magana da wannan harshe
su ne Hausawa.” Idan
ka bibiyi wannan
bayani na Zarruk
da Wasu (1986)
za ka gane cewa Hausa dai harshe
ne, masu yin
magana da harshen kuma sunansu Hausawa.
Adamu (1997:
48) cewa ya yi “Hausa suna
ne na harshe,
kuma masu wannan harshe
su ake kira
Hausawa, domin su
al'ummar Hausawa ba
su ɗauki kansu ƙabila
ba, don kuwa a gurinsu duk wanda ba Bahaushe ne ba, to shi suke ce wa ƙabila,
ko kuma bagwari, wato kamar yadda dai Larabawa suka ɗauki duk wanda ba Balarabe ba
da cewa Ajami ne”.
A ɗaya hannun kuma Adamu (1997:
48-49) ya nuna cewa “Idan mutum ya bibiyi ma'anar ƙabila sosai zai ga cewa
Hausawa sun shiga daidai wa daida. Misali bisa ga bayanan marubuta sun ce ƙabila
al'umma ce mai asali ɗaya da yare ɗaya da kamanni kusan iri ɗaya da al'adun gargajiya iri ɗaya da ra'ayin zaman duniya
(wato falsafa) iri ɗaya da dai sauransu, kuma lallai ne cikin
wannan al‟umma kowa ya zama yana
da'awar shi ɗan ƙabilar ne yana kuma alfahari
da ita (wannan ya yi daidai da bayanin da Zarruƙ da Wasu (1986) suka yi
dangane da ƙabila). Sai ya ƙara da cewa “Idan mutum ya
tarar da Hausawa kafin canzawar zamani da cuɗanya zai ga cewa komai na
wannan bayani ya yi daidai da su, don haka ashe bisa wannan ma'ana, Hausawa ƙabila
ne. Shi kuwa Amfani (2012: 4) cewa ya yi “Hausa harshe ne, kuma tana ɗaya daga cikin harsunan ɗan'Adam waɗanda ake samu a nahiyar
Afirka. A lissafin ko ƙididdiga irin ta masana
ilimin kimiyyar harshe, harshen Hausa yana cikin wani babban rukuni na kason
harsunan duniya wanda ake kira Afroasiatic. Shi ma wannan babban rukuni yana da
'ya'ya kuma kowane ɗa, shi ma ƙaramin rukuni ne mai ɗauke da harsuna. Ƙaramin
rukunin da Hausa ke cikinsa shi ake kira gidan harsunan Cadi. Wasu harsunan
'yan gidan Cadi, waɗanda 'yan'uwan Hausa ne, su ne Angas da Bole da
Ron”.
3.4 MA’ANAR KALMAR LAKUM
Kalmar ta samo asali ne daga kalmar larabci wato (لكم) mai ma’anar naku a
zahiri, yayin da a wannan rukuni ta ke da ma’anar Malam, saboda masu wannan
sana’a sukan shiga rigar malanta su fake ta hanyar shiga irin ta malamai da
kuma samun wasu addu’o’i da za a haddace, saboda yaudara barazana da kuma burga,
wani lokacin har da Ƙur’ani da tazbaha,
ko da yake akasarin su suna da ilimin addinin musulunci dai- dai gwargwado.
Ma’ana ta isɗilahi kuwa tana nufin sana’ar
wa’azi da sayar da magani da ba da laƙani ko laya da kuma duba (Istihara). Galibi sukan yi
amfani da amsa amo (speaker) yayin gudanar da wannan sana'a, kuma suna aiwatar
da sana'ar ne a cikin unguwannin birane da ƙauyuka, da safe ko da dare, ko kuma da rana a kasuwanni
da wuraren taruwar jama’a.
3.5 MA'ANAR 'YANLAKUM
‘Yanlakum (masu wa’azin
turmi) rukunin jama’a ne da ke wa’azi da sayar da maganin gargajiya ko na
musulumci ko bayar da wani laƙani ko guru ko laya, bayan
sun kammala wa’azi. Wannan rukunin jama'a, galibi sukan gudanar da wannan
sana'a tasu ne da safe ko da dare a cikin unguwannin gari da ƙauyuka.
Wani loton kuma da rana a kasuwanni ko masallatan juma'a da sauran wuraren
taruwar jama’a. Akasari sukan yi amfani da amsa-amo (speaker) wadda suke azawa
a kan mota ko wani gini ko bishiya (itaciya) da ke kusa da su domin jiyar da
al'umma.
3.1 KASHE-KASHEN ‘YAN LAKUM
‘Yan lakum sun kasu zuwa gida uku manya kamar haka:
a . ‘Yanɗaiɗai,
b. Sunƙuru,
c. Rufani.
a. ‘Yan Ɗai-ɗai
Wannan kaso na ‘Yan lakum shi ne kason da ke sayar da
maganin lalurori iri daba-daban, ɗaya bayan ɗaya kamar matsalar sanyi, zahi, ciwon daji, ulsa da makamantansu. A
nan bayan ɗan lakum ya gama addu’o’i da gabatarwa da tambihi sai
ya tsunduma cikin tallar magani daki-daki, wato bayan ya yi tallar maganin
sanyi kimanin mintuna goma zuwa sha biyar sai ya ko ma na Basir daga nan kuma
sai na olsa haka dai zai yi ta yi har lokacin da zai tashi, sannan yana yi yana
rage farashin maganin. Su ma sun kasu kashi biyu akwai ‘yan-siba wato masu aiki
kasuwa-kasuwa da rana, akwai masu aikin safe da dare acikin unguwanni su kuma
waɗannan ba su cin kasuwanni.
b. Sunƙuru
Wannan kaso na ‘Yanlakum, su ma suna sayar da magani amma
su ba kamar ‘yan-ɗai-ɗai ba. A nan marar lafiya zai zo ya
yi masu bayanin duk abun da ke damuwarsa da tsawon lokacin da ya ɗauka yana fama da wannan lalura, sai a haɗa masa magunguna a ce ya ba da naira kaza, saɓanin 'yan dai-dai da ke sayar da magani ɗaya bayan ɗaya kuma kowanne ƙulli da nashi farashi, amma kuma wani lokacin ‘yan daidai
sukan yi sunƙuru idan sun fahimci wanda ya zo
neman maganin yana da ƙiri (kuɗi) wato yana da abun
hannunsa.
c. Rufani
Wannan kaso na ‘yanlakum babban aikin su shi ne duba
wato istihara idan wani abu ya ɓace ko an sace shi za su yi
istihara domin gano inda abun yake, ko kuma wanda ya sace shi, wai an ce suna amfani da rufanai dalilin da ya sa ake
kiransu ruhani ke nan, daga cikinsu akwai masu ruhanai na gaskiya, akwai kuma
na ƙarya, duk da yake kashi casa’in da
tara cikin ɗari (99/100) su ne na ƙarya, wato waɗanda ba su da rufanai, kawai suna
amfani da dubaru da hikimomi da kuma mamare ne.
3.2 WASU DAGA CIKIN DABARUN ‘YAN LAKUM
Kira da Riƙe Mutane Kada su Watse: A nan idan ɗan lakum zai fara sana’arshi ta
lakum yana amfani da wasu dabaru domin jawo hankalin mutanen da ke nesa kusa,
da kuma riƙe na kusa gare shi kada su watse,
ta hanyar faɗar wasu kalamai kamar:
Duk masoyin Annabi (S.A.W) da ke kusa ya samu wuri ya
natsu, wanda yake nesa kuma ya matso kusa don jin maganar ɗan gata Rasulullahi, Shi kuwa munafuki yanzu ka ga ya kakkaɓe rigarshi ya ƙara gaba.
Sannan wani lokaci za su ce, za su nuna wani abin ban
al’ajabi, wanda faɗin hakan zai sa na nesa su matso, su haɗu da na kusa, su kasa su tsare, domin ganin wannan abu na ban
al’ajabi, amma daga ƙarshe ba su nuna
komai, dama sun yi ne kawai domin tara mutane da kuma hana su watsewa.
3.3 BADALI
Idan an ce badali a nan ana nufin duk wata dabara ko
waibuwa da za su aiwatar yayin gudanar da sana’arsu da nufin baddalar da
jama’a, wato su sauyar da tunanin jama’a idan sun aikata wani abu na ban
al’ajabi sai jama’a su ɗauka da gaske ne, alhali ba gaskiya ba ne, abu ne da
kowa zai iya yi idan yasa kansa ba wani abun mamaki ba ne wanda sai wane da
wane, daga cikin dabarun na badali akwai:
3.4 AMAYO ALLURAI DA KUMA FYATO
SU TA HANCI
‘Yan lakum sukan ɓoye allurai a cikin bakunansu ko a
cikin hantunansu a lokacin da za su gudanar da aiki, da nufin amayo su ko fyato
su a gaban jama’a a yayin da suke aiwatar da sana’arsu. Idan hakan ta faru
jama’ar da ke wurin za su yi tunanin cewar sun amayo su ne ko sun fyato su ne
daga cikin ciki ko kai, wanda a zahirin gaskiya sun ɓoye su ne a cikin baki ko hanci.
3.5 TAYAR DA HAYAƘI
‘Yan lakum sukan yi amfani da fankon ashana sai su ciro
wurin da ake ƙyasta kan ashana sai su juya shi su
goge shi ya koma lafai-lafai sai su shanya ya sha iska su aza wannan abun da
suka goge a birkice a kan cokali, sai su kunna masa wuta idan ya ƙone zai bar maski a kan cokalin, sai su shafo wannan
maskin a kan yatsunsu, to da zarar sun murza yatsun sai hayaƙi ya tashi a kan yatsun.
3.6 YANKA WUƘA A JIKI
Anan kuma ‘Yan lakum sukan yi amfani da wuƙa mai kaifi biyu sai su koɗa (wasa) ɗayan ɓangaren ya yi kaifi sosai, ɗayan ɓagaren kuma su dallasar (da kusarwa) da shi ta hanyar
goga shi a kan kwalba. Sukan fito da wannan wuƙa a lokacin da suke gudanar da sana’arsu, su yanki wani
abu take kaga ya rabe biyu, sannan sai ku ga kamar sun juya ɗayan ɓangaren wuƙar amma a zahiri ba su juya ba, su sake yankan abun sai
ka ga ya sake rabewa biyu, a ganin jama’a kowane gefe yana da kaifi amma a
zahiri gefe ɗaya ne ya ke da kaifi, wato wanda suke amfani da shi
yayin yankan wani abu, amma idan za su yi gwaji a kan jikinsu sai su yi amfani
da gefen da ba ya da kaifin ma’ana dakusasshen ɓangaren. Su kan yi haka ne don nunawa jama’a cewa su ba hakanan
suke kara zube ba, a shirye suke, alhali kuma ba haka abun yake ba, dabaru ne
da hikinkimu wanda kowa ma zai iya yi.
3.7 TAYAR DA WUTA
'Yan Lakum musamman 'yan
rufani suna amfani da wani abu da ake kira mai kwalli da ake sayar wa a wurin
'yankoli da kuma sinadrin gilasirin sai a sa a takarda a naɗe su wuri ɗaya sai a samu wuri a ɓoye naɗin ko ƙullin, a duk lokacin da wani
mai wata lalura ya zo da matsalarsa sai su ce suna buƙatar ƙasar sawun ƙafarsa,
sai a ce ya cire takalminsa ya taka ƙafarsa a ƙasa sai
su ɗebi ƙasar sawun tafin ƙafar
tasa su naɗe shi a takarda tamkar yadda
suka naɗe waccen takardar ta mai
kwalli da sinadrin gilasirin, daga nan sai su kaikaici Idanun mutun su musaya
takardar da suka naɗe ƙasar tafin ƙafar
mutum da takardar da suka ɓoye, wadda suka naɗe da sinadrin gilasirin da
maikwalli, a lokacin da suke riƙe da takardar da suka naɗe da gilasirin da
maikwalli a hannunsu sai su yi wata burga da barazana ta yin
addu'a su aje ƙullin ƙasa, sai su umurci mai matsalar da ya taka wannan
takarda da suka aje kimanin sakan (second) biyu zuwa uku, to dama wannan haɗi na gilasirin da maikwalli
nauyi kaɗan kuma na ɗan lokaci ƙalilan
yake buƙata wuta ta tashi, da zarar ya taka kimanin
sekan biyu zuwa uku yana ɗauke ƙafarsa sai wuta ta tashi, sai
su faɗi masa cewa akwai babbar
matsala domin akwai masu son su ga bayansa, a gaya masa yana da tarin maƙiya da
mahassada a kewaye da shi saboda haka sai ya tashi tsaye, amma yanzu za a ba ka
taimako wanda idan ka kiyaye amfani da
shi to sai dai ta Allah ba dai mutun ba. Sai su haɗa masa magani su karɓi kuɗi masu tsoka a hannunsa. A
tunanensa ƙasar tafin ƙafarsa ce da aka ƙulle a
takarda ta kama da wuta bai san an musaya ta da wani ƙullin na gilasirin da
maikwalli ba.
3.8 NAƊEWA
Wannan babi na uku da ya
gabata mai kanun fashin baƙin ma'anar kalmomin da suka
shafi taken bincike babi ne da ya yi bayanin ma'anar kalmomin nazari, Hausa,
lakum, da kuma 'yan lakum, sannan an yi bayani game da kashe kashen 'Yanlakum da
kuma wasu daga cikin dubarun da suke yi a lokacin gudanar da sana'arsu daga ƙarshe
aka naɗe babin.
BABI NA HUƊU
HAUSAR 'YAN LAKUM A GARIN
GUSAU
4.0 SHIMFIƊA
Wannan babi na huɗu babi ne mai matuƙar
muhimmanci a wannan aiki domin a ciki ne aka kawo takaitaccen tarihin garin Gusau,
Hausar 'Yan lakum a garin Gusau, an fara kawo kalmomin da 'yan lakum suka samar
a wannan rukuni na su, an kasa kalmomin ta la'akari da dubarar da aka yi amfani
da ita, ko hanyar da aka bi yayin samar da waɗannan kalmomi na 'Yan lakum, bayan
nan aka kawo yankunan jumloli da kuma jumloli na 'Yanlakum, daga ƙarshe aka
zo da naɗewa.
4.1 TAƘAITACCEN
TARIHIN GARIN GUSAU
Garin Gusau gari ne da aka
kafa a shekara ta dubu ɗaya da ɗari takwas da sha ɗaya (1811) a hasashen
kundayen bincike, wato bayan tasowa daga Yandoto a shekarar (1806).
Gusau na ɗaya daga cikin manya-manyan
garuruwan tsohuwar jihar Sakkwato, kafin garin ya zama babban birnin jihar
Zamfara a shekara ta (1996). Kamar yadda kundin bayanin tarihin ƙasa na
shekarar (1920) ya nuna, garin Gusau yana kan babban titin Sakkwato zuwa Zaria,
wato kilo mita ɗari biyu da goma (210)
tsakaninta da Sakkwato, kilo mita ɗari da saba'in da tara (179) tsakaninta da
Zaria. A ɓangaren gabas Gusau ta yi
iyaka da ƙasar Katsina da Kwatarkwashi, daga Arewa kuma,
ta yi iyaka da ƙasar ƙaura-Namoda. A ɓangaren yamma kuma, Gusau ta
yi iyaka da Bunguɗu. A ɓangaren kudu, Gusau ta yi
iyaka da ƙasar Ɗansadau da Tsafe. (Gusau, 1912:7).
Zuwan almajiran malam Shehu
Usmanu Ɗanfodiyo wato malam Sambo ɗan'Ashafa ya kafa garin Gusau
tare da sauran jama'arsa. Malam Sambo ɗan'Ashafa da almajiransa
malamin addinin Musulunci ne, don haka, babu ruwan su da bautar iskoki, da
tsafi da duk abin da ya shafi imanin Bahaushe na gargajiya da dukkanin
camfe-camfensu.
Duk irin bautar iskokin da
Hausawa ke yi kafin zuwan addinin Musulunci malam Sambo ɗan'Ashafa da almajiransa ba
sa yin su kuma a lokacin da ya zo Gusau bai samu irin waɗannan abubuwa na bautar
iskoki a Gusau ba. Don haka, a wannan lokacin garin Gusau ba ya da tarihin
Jahiliyya. Hakan ya sa duk al'adun Gusau al'adu ne irin na addinin Musulunci.
Hakazalika, shigowar wasu mutane baƙi a Gusau bai sa garin ya gurɓace ba kuma Waɗannan kyawawan al'adun ba su
lalace ba. Dalili a nan shi ne mafi yawan baƙin mutanen da ke shigowa a
Gusau malamai ne na addinin Musulunci da kuma almajirai.
Bugu da ƙari, Fulani da wasunsu kan zo
garin Gusau domin samun tsira da addininsu, mutuncinsu da kuma dukiyoyinsu.
Wannan ita ce shimfiɗar da al'adun Gusau ke kwance a kai kuma suke
gudana a kan koyarwar addinin Musulunci da kyawawan al'adu irin na Fulani da
Hausa waɗanda ba su ci karo da tsarin
shari'ar addinin Musulunci ba.
A Zamanin Mulkin Sarkin
Katsinan Gusau wato Malam Muhammad Modibbo (1867 – 1876) aka samu kwararowar baƙi da ƙungiyoyin
mutane daban-daban. Zuwan waɗannan baƙin ya sa garin ya samu bunƙasa a
cikin ƙanƙanen lokaci. Haka kuma, a
wanman lokaci ne aka samu sukunin gudanar da harkokin addinin Musulunci waɗanda suka shafi karatu,
karantarwa, da kuma harkokin ibada ba tare da wata takura ko tsangwama ba. Bugu
da ƙari, akwai cikakken tsaron rayukan mutane da
dukiyoyinsu. Don haka, a wannan lokaci babu abin da ya sha wa mutanen Gusau kai
face harkokin karatu, noma da kuma kasuwanci.
Zuwan Turawan mulki mallaka a
ƙasar Hausa da tasirin karatun boko ya sa wasu
al'adu tsiruwa. Ana cikin haka sai ga shari'ar Musulunci ta sake kawo kai. An
samu canje-canje da dama a wannan lokaci, domin an samu mutane da suka shahara
da gudanar da tafsiri masallatan Jumu'a da wasunsu a garin na Gusau. A yanzu
dai, garin Gusau yana da masarauta ɗaya rak, babban sarki ɗaya wato emiya (Emir).
Wakilai ko uwayen ƙasa goma sha uku (13), yan
majalisa goma sha takwas(18), sarautun fada kuma akwai akalla ɗari ɗaya da goma (110).
Daga lokacin da aka kafa
garin Gusau ya zuwa yanzu, an tabbatar da cewa an yi sarakuna da dama a lokuta
daban-daban kimanin Sarakuna goma sha biyar (15), wato daga shekarar (1806) ya
zuwa shekarar dubu biyu da ashirin da uku (2023). Saboda haka, Sarakuna da dama
sun Jagoranci masarautar Gusau da mutanen garin Gusau. Don haka, ga jerin
sunayen Sarakunan da suka yi mulki a masarautar Gusau daga shekara ta dubu ɗaya da ɗari takwas da shida (1806)
zuwa shekara ta dubu biyu da ashirin da uku (2023) kamar haka;
1.
Malam Muhammad Sambo (1806-1827)
2.
Malam Abdulkadir (1827-1867)
3.
Malam Muhammad Modibbo (1867-1876)
4.
Malam Muhammad Tuburi (1876-1887)
5.
Malam Muhammad Gide (1887-1900)
6.
Malam Muhammad Murtala (1900-1916)
7.
Malam Muhammad (1916-1917)
Akwai wasu sarakunan da suka
yi sarautar Gusau bayan wadannan Sarakuna wadanda ba 'ya'yan wancan gidan na
farko ba. Don haka, wadanda suka yi Sarautar masarautar Gusau ba daga gidan
malam Sambo ba sun hada da;
8. Muhammad Ummaru Malam
(1917-1929)
9. Muhammad Mai-Akwai
(1929-1943)
10. Usmnan Dansamaila
(1943-1945)
11. Ibralhim Marafa
(1945-1948)
12. Muhammad Sarkin Kudu
(1948-1951)
13. Alhaji Suleiman Isah
(1951-1984).
Waɗannan su ne suka yi sarauta
waɗanda ba ya'yan malam Sambo
ba. Bugu da ƙari, bayan wani lokaci, sarauta ta dawo gida.
Sarakunan da suka yi mulki bayan sarauta ta dawo gidan sun hada da;
14. Alhaji Muhammad Kabir
Danbaba (1984-2015)
15. Alhaji Ibrahim Bello
(2015-ya zuwa Yau). (Wikipedia Masarautar Gusau).
A takaice dai, waɗannan su ne Sarakunan da suka
mulki masarautar Gusau daga shekarar (1806) zuwa shekarar (2021). Haka kuma,
wannan shi ne takaitaccen tarihin Gusau ta malam Sambo.
4.2 HAUSAR 'YAN LAKUM A GARIN
GUSAU
Kasancewar ‘Yan lakum rukuni ne na jama’a masu gudanar da hulɗoɗinsu da al’amurransu na yau
da kulln a cikin al’ummar Hausawa, sannan ga su da dubaru da hikinkimu na karɓar kuɗi hannun mutane ya tilasta su samar da nasu karin
harshen rukuni wanda idan ba cikinsu ka ke ba, ko sun yi magana a gabanka to da
wahalar gaske ka iya fahintar abun da suke nufi. Sun ƙirƙiri kalmomi da jimloli masu tarin yawa domin sadarwa a
tsakaninsu, ga wasu daga cikin irin waɗannan kalmomin nasu tare da
ma’anarsu a daidaitacciyayar Hausa.
4.2 SUNAYEN KUƊI A WAJEN ‘YAN LAKUM
Kalma -- -- Ma’ana
- Kamsa -- -- Biyar
- Gunza -- -- Goma
- Muri -- --
-- Ashirin
- Kamsuna -- -- Hamsin
- Ata -- --
-- Ɗari
- Ata da kamsa -- -- Ɗari da biyar
- Ata da kamsuna --
-- Ɗari da
hamsin
- Ataini -- -- -- Ɗari biyu
- Ata kamsa -- -- Ɗari biyar
- Zugun -- -- Dubu
- Zugun wahid -- Dubu ɗaya
- Zugun kamsa -- -- Dubu
biyar
- Zugun ashara -- -- Dubu
goma
4.3 KALMOMI
TA HANYAR ƘIRƘIRA
Kamar sauran hanyoyin samar da kalmomi, Zarruk (1993)
ya bayyana ma’anar ƙirƙirar kalma da ƙago wani laƙabi ko wata magana don bayyana wata baƙuwar ma’ana. Haka kuma ya raba ƙirƙirar kalma zuwa gida biyu kamar haka: (i) ƙirƙirar bazata, da (ii) ƙirƙirar takanas. A nan za a yi bayanin wasu daga cikin
kalmomin da ‘Yan lakum ke amfani da su a cikin mu’amalarsu ta yau da kullum
wadda yanayin sana’arsu ce ta sa suka samar da kalmomin kuma suke amfani da su
a cikin harkokinsu. Wato ƙirƙirar kalmomin su ka yi, sannan alamu sun nuna cewa sun
samu kalmomin ne ta hanyar ƙirƙirar bazata. Waɗannan kalmomin sun haɗa da:
Kalma -- Ma’ana
- Asawa -- --
Mahaifi/tsohuwa
- Asawanya -- Mahaifiya/ tsoho
- Ɗarani --
-- Mashin
- Ɗan-gwabso -- Ɗan-daga
- Ɗan-tanko --
-- Mai shan taba
- Ɗanwara --
-- Ɗangiya
- Fariguza --
-- Rago
- Gulamin-ta-sulaiman --
-- Memori
- Guza -- -- -- Gaban namiji
- Kwasasshe -- Maikuɗi
- Kanɗa -- --
-- Sha
- Ƙiri -- --
-- Mai kyau
- Kiɗima -- Ɗaki
- Mago --
-- -- Magani
- Magori -- --
Mai magani --
- Mani -- -- -- Gaban mace
- Natuta --
-- Talaka
- Nazauran --
-- Bazawara
- Sogaye --
-- kaya
- Sunƙi -- -- -- Ɗaki
- Sunƙin mai duka -- Masallaci
- Sogan na sheɗan --
kayan kallo
- Sogayen nakare -- Takalmi
- Sogayen amalu -- Kayan aiki
- Takaka-- Bindiga
- Takakoki --
-- ‘Yan bindiga
- Sagin mai duka -- Hadari
- Samaka -- Mahaukaci
- Ta-baba-alula -- Keke
- Ta-sulaiman-- Waya (hanset)
- Watu -- -- -- Abinci
- Watun yarima --
-- -- Tuwon masara
- Watun risi --
-- Tuwan shinkafa
- Watun kwoc -- Tuwon dawa
4.4 KALMOMI TA
HANYAR KWATANCE KO SIFFANATAWA
A nan ‘Yan lakum sukan yi amfani da dabarar kwantance
ko siffantawa yayin laƙabawa wani abu
suna a rukuninsu, ta hanyar danganta wannan abun da wata ɗabi’a ko halayya ko yanayin halitta ta wani mutum ko wata dabba ko
wani abu da ya ke da wannan ɗabi’a ko kuma yake yawan aikata ta,
misali
Kalma -- -- Ma’ana
- Dage -- --
-- Faɗa
- Fara -- -- -- Tunkiya
- Jaa -- -- -- Akuya
- Kwata -- -- Jini
- Mai ƙafon tsumma -- Mai gari
- Na-kasa -- -- Barci/kwana
- Na-shanshani -- Ƙafafu
- Na-jaki -- -- Duka/bugu
- Na-tunku -- -- Kashi
- Kwaɗo --
-- Fitsari
- Na-auduga -- -- Dariya
- Na-maraya -- -- Kuka
- Na-amarya -- -- Kunya
- Na-zomo -- -- Gudu/Sauri
- Na-kura -- -- Tsoro
- Na-lawan -- -- Rago
- Na-kahu -- -- Karatu/Ilimi
- Na-giwa -- -- Girma
- Na-gyaɗa -- -- Fetur
- Na-kujeri -- -- Ɗuwawu
- Na jiyamu -- Ido
- Santal -- Gaskiya/Naƙwarai
- Sansiro -- -- Sanyi
- Ta-manzo -- -- Sadaka
- Tatalmizu -- Sadaka
- 'Yar gabas -- -- Sallah
4.5 ARO (BORROWING)
Rufa’i (1979) ya bayyana ma’anar aro a harshe da hanya ce
da harshe ke aro kalmar wani harshe ya sauyata zuwa harshensa. Wannan bincike
ya lura da cewa akwai kalmomin da ‘yanlakum suka samo kuma suke amfani da su ta
hanyar aro daga sauran harsuna musamman harshen larabci, da kuma kaɗan daga wasu harsuna. Misali:
Kalma -- -- -- Ma’ana
- Aƙalu
-- -- -- Hankali
- Ainu
-- -- Ido
- Badawi-- -- Gari
- Baɗalu
-- -- Ciki
- Dari
-- -- Gida
- Gulami
-- -- -- Yaro
- Gulama -- --
Yarinya
- Istoma
-- -- -- Ciwon olsa
- Jasadun --
-- Jiki
- Ju’i
-- -- Yunwa
- Ƙauli -- -- Magana
- Lahamu
-- -- -- Nama
- Lailu
-- -- Dare
- Labanu
-- -- -- Nono
- Lasuwaki
-- -- -- Kasuwa
- La --
-- Ba (Nagation)
- Maridanci -- --
-- Rashin lafiya
- Ma’i -- -- Ruwa
- Nari --
-- Zafi/ Wuta
- Naka --
-- Kwana
- Siyam
-- -- Shekara
- Rijalu -- -- Babban mutun
- Ra’asu -- --
-- Hula
- Sayyara -- --
-- Mota
- Sariƙu -- --
-- Ɓarawo
- Sariƙai -- --
-- Ɓarayi
- Sha'aru -- Gashi
- Ta’allaƙa -- --
-- Laya
4.6 KALMOMI TA HANYAR GUSAR DA MA’ANA DA JUYAR DA GAƁOƁIN KALMA
A nan ‘yan lakum suna ɗaukar wasu kalmomi na Hausa sai su sauya ma’anarsu, wato su ba su
wata sabuwar ma’ana koma bayan wadda aka san su da ita ta ainihi ko asali. Haka
kuma sukan ɗauki kalma sai su juyar da furucinta wato gaɓar farko ta koma ƙarshe ita kuma ta ƙarshe ta dawo farko, wanda ake kira (metathesis) a
harshen Ingilishi da harshen Hausa kuma ana ma shi lakabi da rawar 'yan mata.
Misali:
Kalma -- -- Ma’ana
- Bututu
-- Lasifika
- Duƙowa -- -- Zuwa
- Hita -- --
-- Ƙyale
- Isa --
-- -- Wanda bai jin Hausar
- Jewa --
-- -- Wani wuri
- Ƙashi --
-- Ɗan-Sanda
- Kattafawa -- -- Haɗawa
- Kafan -- -- Fanka
- Katako -- -- Soja
- Liman -- -- Aure
- Naɗewa -- -- Kamawa
- Saukewa -- -- Yi
- Saukewa -- -- Bada wani abu
- Sirba -- --
-- Basir
- Turba -- -- Batur
- Tuta --
-- -- Rashi/Babu
- Tsamaku -- -- Iskoki
- ‘Yankanɗe-kanɗe --
Shaye-shaye
- Zubawa/Zubairu
--
-- Tafiya
4.6.1 Jimlolin ‘Yan Lakum
Baya ga kalmomin da ‘yanlakum suka ƙirƙira sai kuma jimlolin da suka ƙirƙira kuma suke amfani da su a harkokinsu na yau dakullun.
Sun ƙirƙiri waɗannan jimloli ne ta hanyar harhaɗa waɗannan kalmomi nasu domin su ta da jimla mai ma’ana, ga
wasu daga cikin su:
4.6.2 Hausar ‘Yan Lakum -- -- Daidaitacciyar
Hausa
1. Magon magorin nan
santal ne -- Maganin mai maganin nan na gaskiya ne.
2. Zan zuba in sauke ‘yar gabas. -- Zan tafi in yi Sallah
3. Laja la ƙiri. -- -- Ba kasuwa
4. La sauke gulami -- Ba haihuwa
5. Ana sauke gulamai
suna bajewa. Ana haihuwa yaran na mutuwa.
6. Hita da shi. -- -- Ƙyaleshi
7. Maridanci ya naɗe ni. -- -- Rashin lafiya ta
kama ni.
8. Ɗaranin asawana ne. -- Mashin ɗin mahaifina ne.
9. Kattafa mani ta’allaƙa -- -- Haɗa mani laya.
10. Tsamaku sun nake mata ga baɗalu Aljanu sun mata kwance ga ciki
11. Mu zuba kawai. -- Mu tafi kawai
12. Ga ni nan duƙowa -- Ga ni nan zuwa.
13. Kwata la duƙowa -- Jini ba ya zuwa
14. La na-kahu -- -- Jahili/ ba ilimi
15. Jalabce --
-- -- Zauna
16. Ɗanka mai ƙiri -- Budurwa mai kyau.
17. Na faɗa da ɗankar nan -- -- Budurwar nan
ta burge ni
18. Sauke man ata kamsa. -- -- Bani ɗari biyar.
19. Asawan abokina ne ya baje -- Mahaifin abokina ne ya
rasu.
20. Yana dari yana naka. -- -- Yana gida yana barci
21. Naɗo shi a ta-sulaiman. -- -- Kirashi a waya.
22. Hita da gulamin nan -- -- Kyale yaron nan.
23. Na hita da ɗankar nan -- -- Na
ƙyale budurwan nan
24. Ɗankar nan ta naɗo ni -- -- Budurwan nan ta kira ni
25. Gulamin nan ya zuba -- -- Yaron nan yatafi.
26. Rijalun nan ya baje -- Mutumin nan ya mutu.
27. Jalabce ka yi watu -- Zauna ka ci abinci.
28. Ɗankar nan la nakahu --
-- Budurwar nan jahila ce.
29. Ka sauke ‘yargabas? -- -- Ka yi sallah.
30. Maridanci ya naɗe asawana -- Babana ba ya da lafiya.
31. Zuba kawai ga ƙashi nan duƙowa Tafi kawai
ga ɗan sanda nan
zuwa.
32. Tarani --
-- -- Na gane.
33. La tarani --
-- Ban gane ba.
34. Na Kwaɓe -- -- Na bari
35. Siyam wahid --
-- Shekara daya
36. Siyam salasa --
-- Shekara uku
37. Siyam hamsa --
-- Shekara biyar
38. Naka Wahid --
-- Kwana ɗaya
39. Naka arba --
-- Kwana huɗu
40. Naka sitta -- -- Kwana shida
41. Badalta -- -- -- Ɓoye
42. Kurantar da shi -- Tsoratar
da shi
43. Amalus subhi -- -- Aikin safe
44. Amalul laili -- -- Aikin dare
4.6 NAƊEWA
Wannan babi wato na huɗu babi ne da kusan ya
tattauna ilahirin aikin ɗungurungum, domin bayan an yi magana a kan taƙaitaccen
tarihin garin Gusau. Sai kuma aka kawo Hausar 'yanlakum a garin Gusau, an fara kawo
kalmomin da 'yanlakum suka samar a wannan rukuni nasu, an kasa kalmomin tala'akari
da dubarar da aka yi amfani da ita, ko hanyar da aka bi yayin samar da waɗannan kalmomi na 'yanlakum, bayan
nan aka kawo yankunan jumloli da kuma jumloli na 'yanlakum, daga ƙarshe a ka
zo da naɗewa.
BABI NA BIYAR
SAKAMAKON BINCIKE
5.0 SHIMFIƊA
A wannan babi na ƙarshe
mai kanun sakamakon bincike babi ne da zai yi magana akan sakamakon bincike da
kuma bayar da shawarwari ga ɗalibai da sauran manazarta. wannan bincike mai
taken "Nazarin Hausar 'Yan Lakum A Garin Gusau" Bincike ne da aka
gudanar da zummar gano manufa da kuma ma'ana a cikin zantukan 'yanlakum
musamman na garin Gusau an tsara binciken a kan tsarin babi babi tun daga babi
na daya har zuwa na biyar kowanne babi yana dauke da muhimman bayanai masu amfani
ga al'umma musamman ɗalibai da manazarta.
5.1 SAKAMAKON BINCIKE
Sakamakon wannan bincike ya yi daidai da maƙasudi ko manufar binciken domin kuwa an samu nasarar:
v Zaƙulo wasu
daga cikin kalmomin da ‘yanlakum suka ƙirƙira kuma
suke amfani da su a zantukansu na yau da kullun kamar yadda ya gabata.
v Zaƙulo
‘yankunan jumloli da kuma jumloli da suka ƙirƙira daga
waɗannan
kalmomi nasu na fannu kamar yadda ya gabata.
Sannan idan an lura da kyau a cikin gundarin aikin, za
a fahimci cewa daga cikin dabarun da 'Yanlakum suke amfani da su ko suke bi wajen samar da kalmomin su akwai:
v Ƙirƙira: Wato su ƙirƙiri wata
sabuwar kalma wadda babu ta kwatakwata a harshen Hausa domin ambaton waɗansu ababe.
v Aro: (Borowwing) 'yanlakum sun
ari kalmomi masu yawan gaske musamman daga harshen Larabci zuwa Hausar
rukuninsu.
v Kwatance da Siffantawa: Sannan sukan yi amfani da
dabarar kwatance da siffantawa wajen laƙaba wa wasu ababe suna
misali nakasa (bacci), na shanshani (ƙafafu) na maraya (kuka)
v Gusar da Ma’ana: Baya ga wannan sukan ɗauki wata kalma ta Hausa sai
su sauya ma’anarta da wata ma’anar ta daban saɓanin wadda ɗaukacin mutane suka sani.
v Sauya Gurabun Gaɓar Kalma: (metathesis) rawar ‘yan mata wato na gaba ya
koma baya inda ake ɗaukar gaɓar kalma ta farko amayar da
ita baya a ɗauki ta baya a mayar da ta
ta farko. Misali turba (batur), sirba (basir) da makamantansu.
5.2 SHAWARWARI
ko shakka babu harshen Hausa
harshe ne mai tagomashi da kwarjini a
idon duniya, harshe ne da Allah (S.W.A) ya azurta da hikimomi masu tarin yawa
da kuma al'umma masu kaifin basira da zalaƙa. Saboda haka ya zama wajibi
ga al'ummar Hausawa masana da su dukufa wajen rubuce rubuce cikin harshen Hausa
a fannona daban daban na ilimi tun daga ɓangaren kimiyya da fasaha da ƙere ƙere da
ma sauran fannoni na ilimi domin bunƙasa da ci gaban harshen Hausa
a duniya. Domin kowace al'umma ita ke ɗaukaka harshenta ta hanyar
girmama shi da darajanta shi, haka ita ke durƙusar da harshenta ta hanyar
wutaƙanta shi da tozarta shi. Don haka ya zama wajibi
gare mu Hausawa wajen ƙara azama da ƙoƙari don
ganin wannan harshe mai albarka ya ciri tuta a duniya.
Da farko dai muna kira ga ɗalibanmu na wannan lokaci su
yi ƙoƙari su rika zaɓar harshen Hausa a matsayin
abin da za su yi nazari akai idan za su tafi makarantun gaba da sakandare,
wannan shi zai kara bunƙasa harshen.
Sannan masu gudanar da bincike musamman ɗalibai, idan za a yi nazari
ko bincike a kan wani abu daga sassa ko rassan Hausa guda uku wato Harshe, da
Adabi, da kuma Al'ada, ya kamata a tsaya tsayin-daka a natsu tare da bin
ingantattun hanyoyi domin gudanar da bincike mai inganci da nagarta.
Bayan haka yayin gudanar da bincike
a riƙa yin amfani da harshe mai sauƙi domin
samun sauƙin fahimta.
Kira ga ɗalibai 'yan'uwa gaba ɗaya musamman masu nazarin
harshen Hausa da su ƙara faɗaɗa karatu idan an samu dama.
Haka kuma, a na ba da shawara
zuwa ga malamanmu na wannan sashe mai albarka, wato sashen nazarin harsuna da
al'adu, da su ƙara azma da ƙoƙari a kan wanda suke yi domin
ganin samun nasarar ɗalibansu da su kansu kamar yadda suka saba.
Daga ƙarshe, muna ba da shawara
zuwa ga masana, da masu ruwa da tsaki, da kuma masu sha’awa da harshen Hausa su
riƙa ɗaukar nauyin wasu ɗalibai suna tura su jami'o'i
daban-daban na gida da na waje domin nazarin harshen Hausa, da kuma ɗaukar nauyin buga littattafai
da rarraba su zuwa makarantu da ɗakunan karatu na makarantu daban-daban.
5.3 NAƊEWA
Hausawa na cewa Karshen
tikatika tik kuma komai nisan dare gari zai waye sannan komai nisan jifa ƙasa za
ta faɗo, haƙiƙa komai ya yi farko to shakka
babu zai yi ƙarshe, cikin iyawar mai kowa mai komi a nan
muka zo ƙarshen wannan bincike mai taken Nazarin Hausar
'Yan Lakum A Garin Gusau
A babi na ɗaya, an yi tsokaci a kan manufar
wannan bincike da farfajiyar bincike da hasashen bincike da matsalolin bincike da
muhimmancin bincike da hanyoyin gudanar da bincike da ra'in bincike sai kuma a ka
zo da naɗewa a ƙarshen babin.
A babi na biyu, mai kanun
bitar ayyukan da suka gabata. Bayan anyi Shimfiɗa, sai bitar ayyukan da suka
gabata, an fara da rubutattun littatafai, sai kundayen bincike da aka rubuta a
matakai daban-daban na ilimi, sai kuma muƙalu da mujallu duka dai masu
nasaba da kuma alaƙa da wannan bincike, sai kuma
hujjar ci-gaba da bincike, daga ƙarshe a ka zo da naɗewa.
Babi na uku mai kanun fashin
baƙi a kan ma'anonin da suka shafi taken bincike,
bayan an yi Shimfiɗa, an kawo ma'anar kalmar Hausa, da ta lakum,
da kuma 'Yan lakum, sannan an kawo kashe-kashen 'yan lakum, daga nan kuma aka
zo da wasu daga cikin dabarun 'yan lakum, sai kuma naɗewa.
Babi na huɗu, mai kanun Hausar 'Yan
Lakum a Garin Gusau. An fara da Shimfida, takaitaccen tarihin garin Gusau,
Hausar 'yan lakum a garin Gusau, an fara kawo kalmomin da 'yan lakum suka samar
a wannan rukuni nasu, an kasa kalmomin tala'akari da dubarar da aka yi amfani
da ita, ko hanyar da akabi yayin samar da waɗannan kalmomi na 'Yan Lakum,
bayan nan aka kawo yan kunan jumloli da kuma jumlolin Hausar 'yan Lakum, daga ƙarshe
aka zo da naɗewa.
A babi na biyar, mai kanun
sakamakon bincike. Bayan an yi shimfiɗa, sai aka kawo sakamakon
bincike, daga nan kuma aka zo da shawarwari sai kuma jawabin naɗewa da manazarta.
MANAZARTA
Abdulkadir,
M. (2018). “Hausar Rukunin Yan Banga a Garin Gusau.” Kundin Neman Digirin Farko
A Jami'ar Tarayya Gusau.
Abdulƙadir, Z. (2013). “Karin Harshen Rukuni: Nazarin Hausar Kan
Titi”.Unpublished M.A Thesis. Zaria, Ahmadu Bello University.
Abubakar, I. A. (2001). “Dangantakar
Harshe Da Addini: Nazari Akan Karin Hausar Gardawa a Birnin Kano da Kewaye”. Maƙala da aka Gabatar A taron ƙarawa Juna Ilimi Tsakanin Malamai da ɗalibai. Kano: Jamiar Bayaro. (Unpublished).
Adamu, A.U. (2008). “Salon Ta ɗin Mata Hausawa a cikin Garin Kano.” Kundin Digiri na Biyu,Sashen
koyar da Harsunan Nigeriya. Kano; Jamiar Bayero.
Adamu, M.T (1997). Asalin Hausa
da Harshensu. Kano Dansarkin Kura Publishers, 1997.
Amfani A.H (2012). “Hausa da Da
Hausawa: Jiya da Yau da Gobe, in Amfani, H.A, et al (eds.) Champion of Hausa
Cikin Hausa.” Zaria Ahmadu Bello University Press, 2012.
Azare,
Y.M.(2011). “Language In
Diversity: A Look
At The Role
Of Women Towards Language Development
In Hausa Socio-Lingustics Setting”.
In Studies In Hausa Language, Literature and Culture. The 6th Hausa International Conference.
CSNL, Kano: Bayero University.
Babanzara, M. H.
(2006). “A Typology
Of Hausa Jargon”.
In Journal Of
Humanities Vol.3.No.4, Fuculty of
Art and Islamic Studies, Kano: Bayero Universty.
Bunza,
A. M. (2017). Dabarun Bincike. Zaria, Ahmadu Bello University press
Limited.
Dawakin Tofa, M. I. (2005). “Karin Harshen
Mahauta.” Kundin Digirina Biyu, Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya Kano: Jamiar Bayero.
Fagge, U. U. (2002). “Zaurancen Zaurawa a Birnin
Kano Da Kewaye”. In Algaita
Journal Of Current Research In Hausa.
Vol.2 No.1.
Fagge, U. U. (1999). “Tasirin Karin
Harshe na Rukuni wajen ƙirƙirar Sababbin Ma’anoni a Hausa”. Takardar Da aka
Gabatar a taron ƙara wa Juna Ilimi. Sashen koyar da
Harsunan Nijeriya. Kano: Jamiar Bayero.
Fagge,
U. U. (2001). Ire-iren Karin Harshen Hausa Na Rukuni. Kano: Benchmark
Publishers Limited.
Rufa’i,
A. (1979). "Principal Resources of Lexeme – Formation in Hausa.” Harsunan
Najeriya. Kano. Bayero University.
Zarruƙ da
Wasu. (1986). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa. Ibadan University Press
Limtied.
Zarruƙ, R. M
(1993) Aro da Kirƙira A Harshen Hausa. Institute of Education.
Zaria. Jami’ar Ahmadu Bello.
https://www.amsoshi.com/2022/03/hausar-rukunin-masu-sanaar-waya-garin.html?m=1
https://www.google.com/amp/s/docplayer.net/amp/54653968-Karin-harshen-rukuni-nazarin-hausar-masu-sana-ar-kayan-gwari-hamisu-ahmed-ma-arts-16486.html
Muntari, H. (2008). “Karin Harshe
Na Rukuni A Hausa: Nazari A ƙasar Zazzau. Kundin Digiri na Biyu”. Sashen Harsuna da
Aladu na Afirka Zariya: Jamiar Ahmadu.
Musa,
A. (2011). “Hausa-Niga:
Nazari A Kan
Walwalar Harshe Da Zamantakewa Tsakanin Rukunin Matasa
Maza Hausawa A
Yau”. In Studies of Hausa
Language, Literature And Culture.
The Sixth Hausa International Conference. CSNL. Kano:
Bayero University.
Salihi,
T. M (2012). Sakace A kan Karin Harshen Hausa. Absur Comprint. F. C.E,
Kano.
Salihu,
N.A (1987). “Code Switching among University of Sokoto Hausa-English Bilingual”.
Kundin binciken digirin farko a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya: Jami'ar
Usmanu Danfodiyo Sokoto.
Sani, A.
& Sani, A. U. (2023) “Daga Hausar Rukuni Zuwa Boyayyiyar Al'ada”: Kebabben
Nazari A Kan Hausar Telolin Garin Gusau. Journal of Language, Literatire And
Culture: Publication of the Department of Languages and Cultures, Federal
University Gusau, Zamfara, Nigeria.
Tukur,
A. (2020) “Hausar Rukunin Masu Sana'ar Waya A Garin Gusau.” Kundin digiri na
farko wanda aka gabatar a Sashen Harsuna Da Al'adu, Jami'ar Tarayya Gusau.
Umar, M.
M. & Abbas, N.I. (2020) “Nazarin Hanyoyin Samar da Hausar Wasu Rukunan ‘Yan
Kasuwa a Cikin Garin Sakkwato”. Department of Nigerian Languages, Usmanu
Danfodiyo University Sokoto, Nigeria
Yahaya,
S. (1998). “Hausa a Jami'a. Kundin Neman” Digirin Farko A Jam'ar Usmanu
Danfodiyo Sokoto.
Yakasai, M.G.
(2004). “ Yanayin Karin
Sojoji A Barikoki”:
Nazari a kan
Barikokin Bukabu Da Na
Jan-Guza”. Kundin Digiri Na Biyu.
Sashen Koyar da Harsuna Nijeriya. Kano:
Jami‟ar Bayero.
Yakasai, S.
A (2005). “Aro
Ko Ƙirƙira: Nazrin
Samuwar Sababbin Kalmomin Hausa” A Jami‟a Da
Kuma Garin Sakkwato.
Takardar Da Aka
Gabatar Wajen Taron Ƙara Wa Juna
Sani. Sakwwato: Jami‟ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Yakasai, S. A. (1988). “Verbal Honorifics in
Hausa: A Sociolinguistics Analysis”. Phd
Theseis. Kano: Bayero University.
Yakasai,
S. A. (2010). “Dangantakar Harshe da Muhallin
Magana: Nazari Kan Magana Tsakanin
Hausawa”. In Harsunan Nijeriya Volume XXII.
Center For the Study of Nigerian Languages. Kano: Bayero University.
Yakasai,
S. A. (2012). Jagorar Ilimin Walwalar
Harshe. Sokoto: Garkuwa Media
Services LTD.
Yero, Z.
S. (2017) “Hausar Yaran Mota”: Nazarin Ma'ana Da Ginin Jimla. Kundin Digiri Na
Biyu. Sashen Koyar Da Harsuna Da Al'adun Afirika: Jami'ar Ahmadu Bello Zaria.
https://ha.m.wikipedia.org/wiki/Masarautar Gusau.
WAƊANDAAKAZANTADASU:
1. Malan Sanusi Muhammad (Malan Muhammadu) dan shekara 35, Ranar Lahadi 8/1/2023
2. Malan Umar Ibrahim shekare, ɗan shekara 25, Ranar Litinin 9/1/2023.
3. Malan Usman Malan Ibrahim Kagane, ɗan Shekara 40, Litinin 9/1/2023.
4. Doctor Sulaiman Shala Gusau, ɗan shekara 38, Ranar Talata1 0/1/2023.
5.
Malan Sule
Tsoho
Gusau, ɗan shekara 27, Ranar
Alhamis 6/7/2023.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.