Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
328. Harafin
m da za ka furta can laɓɓai,
Shi muka mai da
hankali na yallaɓai,
Harafin
m idan ya zo farkon gaɓɓai,
Matuƙar dai akwai wakili ya raɓai,
Kuma
a gabanta ga gaɓa mai bijirowa.
329. In
ta zo kusan waƙilin sunaye,
Ga ta a manne zan
kula sai a kiyaye,
‘Ma’ ta biyo a sa
wakilin sunaye,
Ka tsaya tsab ka
gane komai kai waye,
Sai a haɗe
su tare can ga rubutawa.
330. A misalan da za su zo ba inkari,
Kalmomin suna ga
jimla bari zari,
Dakanta ka daina
jawo mini tari,
Saƙona
garai ya kawo mini gari,
Tare da bokitin ruwana na jiƙawa.
331. Yau kam za ni taimaka miki dole na,
Ita ko sai ta
taimaka maka tilas na,
Kar ki sake ki
takura mishi yaro na,
Ga
zatona Abubakar yai miki ɓanna,
Na ga yana gudu yana wawwaigawa.
332. Tashi da hanzari ki miƙa mata Saude,
Ungo haɗa ki je ki damƙa mata ludde
Miƙa mata fittilar ta ko samu ta yade,
Bari
sai ta fito ka tura mata Kande,
Yanzu ta maƙare ta sai ta yi
haraswa.
333. Lura ka mai da hankali don ka yi koyo,
Baƙi sun ka zo muna masu oyoyo,
Mun
gaji ‘yan wajen ƙasa nai mana wayo,
Sun
bar mu da ɗakuna suna yi
mana yoyo,
Mu da ƙasarmu dukiya su ka
rabawa.
334. An
yi zaton da mun gani ai mamu wayo,
Ɗabi’un duk da sun zo su muka
koyo,
Sun kwakkwashe
dukiya sun mana wayo,
Noma arzikin ƙasa su muka tanyo,
An ga irin zubinmu tamkar ƙauyawa.
335. Nai
muku tambaya kuna son
ku ƙure ni,
Kuma na lura dai kuna son raina ni,
Me ke sa maza fita don ci rani?
Ga ɗabi’unmu yanzu mi ke muna rauni?
Ga amsa ƙiri-ƙirir
kun ƙi gayawa.
336. To
ka dai ga muku yadda ka zana ta,
In ka rubuta mu ku tabbata ka ɓata ta.
Zauran
nan da yab biɗa tai masa
cuta,
Tai masa
yaudara da har ya ƙyale ta,
Ta cinye shi har ƙashi
bai da ta cewa.
337. Yara a ko’ina suna son su ga taro,
Yanzu a zamanin ga
sun gagara horo,
Ga su tsayensu, mu
muna garkar Gyauro,
Regon
rijiya yana sa masu tsoro,
Ko ɗiban ruwa sukai ba a regawa.
338. Harafin
m cikin wakilin sunaye,
Ba a raba su ko’ina sai su yi goye,
To daɗa mai da hankali sai ka kiyaye
Sai ka haɗe cikin rubutu kai waye,
Tare suke zama suna tattaunawa.
339. Ba
a raba su ko alama ga rubutu,
Sa su a tare don rubutu ya karantu,
Haka nan ƙa’ida ta bayar ta
rubutu,
A haɗe ba space a huta ga karatu,
In ka raba su kai kure sai gyarawa.
340. In ma ta biyo wakili a taƙaice,
Ba a raba su wanga tsarin kalma ce,
Doka ta taho da tsarin a rubuce,
Ko
jam’u walau tilo in ya kasance,
Duk
ka haɗe su kar ka zan mai
ruɗewa.
341. Shi suna akwai lamirin kowanne,
Sa tilo ga su
jam’u nunin rukuni ne,
Ni, kai, shi, da
ke da ita tilo ne gane,
Mu, ku, su,
waɗanga nan duk jam’i
ne,
Ka ji kashinsu ukku farko da tuƙewa.
342. Ni,
ke, ta, zubin tilo ne ka kiyaye,
Ka, da ya, da ki, fa duk
ka kiyaye,
Ai shi da ita suna da kaya
jajaye,
Yanzu da ni da ke
har da ƙawaye,
Sa, na, duk gidansu ɗai ba a rabawa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.