Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
343. Mun
sa jam’u can a baya ka tantance,
Mun ko ga yadda nasa tsari
ya kasance,
Kalmomi
na jam’u babbar tawaga ce,
Za a biyo da nasu tsarin a rubuce,
Ga bayaninsu ko guda ba ya ragawa.
344. In
suka gwamatso lamirrai ga zubinsu,
To a yi ƙa’ida a gwama su
dukansu,
Ba a raba su dole
sai an gwama su,
Tare suke zuwa a
dokar tsarinsu,
Sai su shige gida guda ba su fitowa.
345. Babu
buƙatar daɗin bayanin jam’un nan,
Ka
san jam’u tun tuni mun gama wannan,
Mun
yi bayanin su baya ai ka riƙe wannan,
Har
da misalansu
mun ka yo tun babin nan,
Fasali kansu ya wuce tun da daɗewa.
346. In mun tuna jam’u tsari na lamirai,
Wakilcinsa
ga ɗaukacin halitta
duka mai rai,
Sai ka ga ya taho jikinai da lamirai,
To in
ya haɗe a ƙarshe
da lamirrai,
Can ƙarshensa gun gaɓa mai ƙarewa.
347. Za
a haɗe su tare don ba a
raba su,
Gun furuci a tare za ka ji sautinsu,
Haka a rubuce tare ne aka zana su,
Ka yi kure idan ka ce za ka raba su,
Dubi
waɗanga ‘yan misalai
da ka zowa.
348. Zancen
dukkaninsu koko dukkansu,
Ka yi kure idan ga zane ka rabe su,
Haka ma ba a so ka zana dukkan su,
Doka tai hanin ka ware rubutunsu,
Haka
nan kowannensu can ga rubutawa.
349. Ga
misalinsu nan ga jimla a rubuce,
Dukkaninsu tun tuni suka lamunce,
Kowannensu ya faɗa mini keɓance,
In ka
ji tarsashinsu duk sun lalace,
Ma’ana babu ko guda mai tserewa.
350. Kowannensu na da haurensa talatin,
Dukkanninsu yanzu sun zarce sittin,
Katin gayyatar ga,
ga ƙwara metin,
Matan
kowacensu ta haura talatin,
Ba sauran ƙurciya sai tsohewa.
351. A misali ka duba ƙari ga waɗannan,
Ga sharaɗi dukanku ko kun san wannan?
Ban
son kowanenku in gan shi wurin nan,
Tuni dai
kowannensu ya kauce dan nan,
Na fi
da son ku gurgusa can a ƙurewa.
352. Sam
ba a sanya dukkanin ku rubuce,
In ka zana kowannen ku to ka kauce,
Ga misali ka sanya
kalmar kowacce,
Don
me kowacenku in za ta yi zance,
Sai ta gilma rantsuwa don shaidawa?
353. A misalan da za su zo kai dubawa,
Ba a raba su in ka
zo ga rubutawa,
Dukkanninku, sai
ku duba da kulawa,
Ɗaiɗaikunku na ga kun fara
shigewa,
Sannu dukanku hankali na kawowa.
354. Lamirin
jam’i idan ya zo nan a rubuce,
To a
haɗe su babu sauran wani zance,
Ga wata ƙa’ida ku duba a
rubuce,
In
jam’in sifa ya ɗau nsu ga
zance,
Sai a haɗe su bai guda ba a rabawa.
355. Yanzu biyo na ba ku misalinsu,
Tamkar babbaƙunsu duk an ɗebe su,
In ka rubuta babbaƙun
su
to ka
ɓata su,
Ko jam’i na
ja in a ƙarshe
ya ɗau nsu,
Jajayensu an rufe ba su fitowa.
356. Kyawon
farfarunsu leshi da atamfa,
Korayensu, ɗazu na gan su a Kwaifa,
Shuɗayensu ga su can a cikin rumfa,
Guntayensu ga su baki na kumfa,
Dogayensu munduwa suka ɗaurawa.
357. Saurara ka kakkaɓe muna kunnenka,
In ka tuna sifa
ana nunnunka ta,
Haka kan nsu kan
zame ɗan rakiyarta,
Ƙara
kula sifa idan an nunka ta,
In ta haɗe da nsu to ba a rabbawa.
358. Siffofi
baƙi, fari ana
ninninka su,
Sannan sai a liƙa nsu tare a jera su,
Za a haɗe su, babu mai ware gaɓarsu,
Lura
idan ka ce baƙaƙe-baƙaƙensu,
Sun ɗara farfarunsu sauƙin
ganewa.
359. A misalan da za mu kawo na irinsu,
A mutane muke buƙatar mu gwada su,
Duba kalarsu yanzu
ko za a rabe su,
Amma
juriyar farare-fararensu,
Ya fi
na babbaƙunsu in za a gwadawa.
360. Je
ka yi bincike da himma ga shirin ga,
Za ka tarar da su ya su dukka waɗanga,
Su duka an haɗe su ba ware wa’yanga,
Kar ka taƙaita kan misalanmu
na nan ga,
Dangoginsu duk a nan ba a rabawa.
361. Lura aboki an ya zam kanka a waye,
In ka lura nan
wakilin sunaye,
A misalan da mun ka kawo
jeranye,
Su suka bayyanar
da jam’i kai waye,
Jam’u
yake zuwa da shi dinga kulawa.
362. Suna in ya zo da liƙi na ɗafi ne,
Ko a tilo ya zo walau ko jam’i ne,
Shi aka ɗofana a san wane nau’i ne,
Ɗofane
nsu babu shakka jam’u ne,
Ɗofane nsu ko
tilo shika nunawa.
363. Ka
dai ga irin gamon wakilin sunaye,
Kalmomi na jam’u
ga su a jeranye,
Dubi
abin da hankali don ka kiyaye,
A misalan
da mun ka ba da ka kiyaye,
Kuma
ka yi binciken misalan badawa.
364. In ka bincika ka samu fahimtar su,
Yanzu ka sa natso[1], lura dukkansu,
Ba a raba ba lura
nan ga rubuta su,
In ka
bi sannu sai ka hardace dukkansu,
Sannu da hankali abin ba rikitarwa.
[1]
Natso a nan na nufin natsuwa wato
dai mutum ya kasance cikin yanayi mai kyau wanda zai kasance da dukkan
tunaninsa, da hankalinsa a kwance.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.