Ticker

Haduwar Wakilin Suna da Lamirin Lokaci

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

314. In suna ya zo gashin kansa yakan ci,

A rubuta daban saboda akwai ‘yanci,

In ko ka haɗe shi ka sani kai lalaci,

Ka lalata duk rubutun ya ɓaci,

  Haka nan na’ibinsa in zai aikowa.

315. ‘Yanci ne ga duk wakilan a taƙaice,

Amma duk da ya kasance ‘yantacce,

 ‘Yancin nan yakan kasance ɓatacce,

In ya haɗe da lokaci sun ka riɓince,

  Sun zama ɗai ga lisafi ga rubutawa.

 

316. Yanzu a duba ‘yan misalai na kwatance,

Tamkar dai ka ce yana nan ɗaka kwance,

 Ya ita nan wurin wakili ta kasance,

 Lura akwai wurin da bai tsayawa a kaɗaice,

  Ga ta tana ganinsa ta ƙi kusantowa.

 

317. In ka yi bincike kana gane kurenka,

 Yau ta kai ga ko’ina ana yi ta zagin ka,

 Hatta ɗanka ma yana yi ta kushe ka,

 Ga matarka can tana jin haushin ka,

  Kar ku bi tasa in kuna son tserewa.

 

318. Ga Jimmai a can tana murguɗa baki,

 Shi ko mijinta ga shi nan ƙofar ɗaki,

 Ya kuma bayyana ya ce “zan hora ki”,

Bi shi a sannu in kina son haƙƙinki,

  In kika bi shi duk shina iya badawa.”

 

319. Yaran nan suna ta faman yin wasa,

 Na ji su sun daɗe suna yin sa-in-sa,

 Ba ni zaton suna faɗa sai dai wasa,

 Ga shi abin da sun ka shirya don gasa,

  Kun ƙyale kuna zaton ba su iyawa.

 

320. Na yi zaton kamar ina iya juya shi,

 Mai kunnen ƙashi yana son a taɓa shi,

 Ya yi ta yunƙuri, ana da]a taushe shi,

 Su suka ce da ni, suna iya gyara shi,

  Na fara ana ganin ban ƙyalewa.

321. Lura dukansu sun taho ga su a jere,

 Nahawun Hausa ba ya yarda su yi ware,

 Ba a rarrabe su don ba su da bare,

Doka ce ta tattara su, su zan tare,

  Bisa kalma guda ya zan ba a rabawa.

 

322. Dokokin ga sai ka sanya su ga kanka,

 A rubutu ka sa su sai a fahince ka,

 Dokokin ga su ka saitin aikinka,

In ka raba su sai ka ɓata bayaninka,

  Duk hikimarsa babu mai iya ganewa.

Post a Comment

0 Comments