Ticker

Haduwar Wasalin ‘a’ da Lamirin Lokaci

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

323. Wasalin a yana laɓewa ga lamirrai,

Sai a yi hattara a kauce ma kurairai,

Shi ke bayyana ga wanda ake sa rai,

Ba ya bayyana ku san sai ga lamirrai,

  Su su laƙe wuri guda ba warewa.

 

324. Su uku ne a nan wurin zan jerowa,

 Farko ‘a’ da ‘ka’ aka gwamawa,

 Ko kuma ‘a’ da ‘ke’ ga rubutawa,

 Haka nan ‘a’ da ‘na’ a jere suke zowa,

  Don a yi harda yadda ba a mantawa.

 

325. Duba misalin ga ko kana gane nufina,

 In aka ce ba a yi da kai to tafi zauna,

 Kila ana gudun ga aikin ka yi ɓarna,

In ka ce karamta malam aka ƙauna,

  Jayayya da shi ake ƙi na ƙyacewa.

 

326. Kan maganar tsaro ana yi ta yin tsaki,

 Sun daki taiki, yau suna ta bugun jaki,

 Ba ga talakka ɗai ba yau har da saraki,

Na ga Bagobiri ana karkace baki,

  An sa Dikko yin gudu ba waigawa.

 

327. To a taƙaice a da na sai a haɗe su,

 Haka nan ‘su’ da ‘na’ ba a rabe su,

 Tare ake haɗa su, nan ga rubuta su,

Ka ga a nana nan wurin sai a haɗe su,

Haka aka son ka zan rubutu da kulawa.

Post a Comment

0 Comments