Hukuncin Likitan Da Yake Taba Jikin Mace Mara Lafiya

    TAMBAYA (38)

    Salãmun alaikum warahmatullah, Uncle barkada yamma, Dan Allah uncle meye hukuncin alwalar Wanda arashin sani konace bada wata manufaba wani ban gare na jikinshi yataba wani ban gare na jikin mace. Misali idan Dr ya zo yiwa yaro allura Sai manar yaron tariqe yaron to Sai ko hannunta kowani ban gare na jikinta yataba jikin Dr, ko hannunsa kafin yadauke daga inda yama yaron allura itakuma takawo hanu donta massaging din wajen,

    Komisalin yataba jikin yarinya qarama ya ji yanayin temperature jikin ta, Amma ranshi lafiya qalau Babu wata manufa Kota misqala zarratin

    AMSA:

    Haramun ne mutum namiji ya taba wadda ba muharramarsa ba

    An rawaito daga Ma'qil ibn Yassar RA ya ce: Annabi SAW ya ce: "A samu qusar qarfe a bugawa mutum a kansa shi ne ya fi masa sauqi akan ya taba macen da ba ta halatta a gareshi ba"

    Dabarani ne ya rawaitoshi a cikin al-Kabeer, 486. Shaykh Albani ya ingantashi a cikin Saheeh al-Jaami' 5045

    An karbo daga Urwah, Nana Aisha RA ta ce masa: Lokacinda matan Muhajirun sukai hijira zuwa Madina sun kasance suna Mubaya'a ne ba da musaffah ba (Gaisuwar hannu da hannu), tace: Annabi SAW bai taba shafa hannun wata mace da hannunsa ba. Saidai yana bayanine akan ga abin da Mubaya'a take nufi idan mace ta amince sai ya ce: Je ki an amshi Mubaya'ar ki"

    Sahih Muslim (1866)

    Haka kuma an karbo hadisi daga Umaymah RA yar Raqeeqah RA tace: Annabi SAW ya ce: "Bana gaisawa (musafaha) da mata"

    al-Nasaa'i (4181) da ibn Majaah (2874). Shaikh Albani ya ingantashi a cikin Saheeh al-Jaami' (2513)

    Hadisin da al-Tabaraani ya rawaito a cikin al-Kabeer da kuma al-Awsat da aka rawaito cewar Annabi SAW yana gaisawa da mata da karkashin hannun riga, wannan hadisi da'ef ne (Al-Haytham ya ce bai ingantaba saboda a cikin isnadin hadisin da akwai 'Ataab ibn Harb shikuma a ilimin hadisi da'eef ne)

    Majma' al-Zawaa'id, 6/39

    Shaykh Ibn Baaz (Rahimahullah) ya ce: fadin Annabi SAW: "Bana gaisawa (musafaha) da mata" kadai hujjace da ke kawarda duk wani hadisi wanda zai kawo shubha

    (Hashiyat Majmoo'at Rasaa'il fi'l-Hijaab wa'l-Sufoor, p. 69)

    Al-Zayla'i ya ce: Gameda riwayar da aka ce Sayyadina Abu Bakr RA yana gaisawa da tsofaffin mata, wannan ghareeb hadis ne"

    (Nasab al-Raayah, 4/240)

    Ibn Hajar ya ce: "Ban ga wannan hadisin ba"

    (al-Diraayah fi Takhreej Ahaadeeth al-Hidaayah, 2/225)

    Gaba daya mazhabobin Hanafiyya, Malikiyya da Hanbaliyya duk sun tafi akan hukuncin taba mace ko yin musafaha da ita haramunne

    Mazhabain Shafi'iyya kuma Imam an-Nawawi ya ce: "Haramunne taba mace ta kowacce siga". Shi kuma Wali al-Deen al-'Iraaqi ya kara da cewar saidai idan ya zamana idan har Annabi SAW wanda yake gudun fadawa zargi zai yi taka tsantsan to sauran mutane su ya fi cancanta su nesanta da hakan

    Manyan malamai sun karawa juna sani akan cewar haramun ne taba jikin wadda ba muharrama ba ko da kuwa fuskartace. Amman sun samu banbancin ra'ayi ta ban garen kallon mace idan babu sha'awa kuma hakan bazai haifar da wata fitina. Idan ya zamana akwai ad-darurat (larura) misali: rashin lafiya, cire haqori. Idan babu macen da za ta iya wannan aikin to ba matsala idan mutum ya taba wadda ba muharramarsa ba (misali: ya ji jikinta akwai zafi ko wani abu makamancin haka)

    Tarh al-Tathreeb, 7/45,46

    Don haka a takaicedai indai har babu wani abu da ya fita daga jikinsa silar sha'awa to alwalarsa tananan in sha Allahu saboda a bisa babin larurane ya taba wadda ba muharramar ta sa ba

    Hadisin "Innamal a'amali binniyati" shi ne zai aiki anan

    Idan ya yi ne a bisa ad-darurat (larura) to ba matsala amman idan da niyyar jin sha'awa ya yi to haramun ne

    Amsawa:

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.