Hukuncin Matar Da Take Ɗaukar Kuɗin Mijinta Ba Tare Da Saninsa Ba

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum malam, meye hukuncin matar da take daukar ma mijinta kuɗi bai sani, ko wani abu nashi ba tare da ya sani ba ta yi bukatunta da su? Wassalam.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus salam, matar da take ɗaukar kuɗin mijinta ta yi amfani da su saboda mijinta maƙeƙe ne ko mai ƙoro, ba ya ba su abincin da zai ishe su, to ya halasta ta teɓi kuɗinsa su ci abinci gwargwadon buƙatarsu ba tare da ɓarna da almubazzaranci da dukiyar ba, dalili a kan haka shi ne: Nana A'isha Allah ya ƙara mata yarda ta ruwaito hadisi cewa: Lallai Hindu ƴar Utbata ta ce: Ya Manzon Allah lallai Abu Sufyana ya kasance mutum ne maƙeƙe, ba ya ba ni abin da zai ishe ni da ƴaƴana, face sai abin da na ɗauka daga wurinsa bai sani ba, sai Manzon Allah ya ce: "Ki ɗauki abin da zai ishe ki da ƴaƴanki tare da kyautatawa". Bukhariy 5364.

    Wannan hukuncin ya keɓanta ne kaɗai ga matar da mijinta ba ya ciyar da su yadda ya dace saboda maƙo alhali yana da hali. Amma duk matar da mijinta ke ba su haƙƙoƙin ciyarwa gwargwadon hali, to idan ta ɗebi kuɗin mijinta bai sani ba ta yi amfani da su, tabbas ta ci haramun, sai ta biya shi gobe Alƙiyama, kuma abin da ta yi sunansa ha'inci, ko zamba cikin aminci.

    Amma raguwar abinci ko raguwar abinsha da a al'adance mace kan yi sadaka da shi ga baƙi ko makamantansu wannan babu laifi don mace ta bayar da su sadaka. Amma rumbun abincinsa bai halasta ta ɗebo ta yi sadaka da shi ba sai da saninsa.

    Allah S.W.T ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.