Hukuncin Mijin Da Ya Bar Wa Matarsa Jariri

    𝐓𝐀M𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Mene ne hukuncin musulunci idan miji ya ce, ya bar wa matarsa jariri ko jaririyar da ta haifa masa?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

    Idan har haka abin ya auku, to da farko wajibi ne a janyo hankalinsa ya san cewa: Ƙullin aure a musulunci yana ɗauke ne da waɗansu nauye-nauye masu girma musamman a kan mazajen auren, nauye-nauyen da Allaah Subhaanahu Wa Ta’aala ya siffata su da cewa alƙawari ne mai kauri:

    وَكَیۡفَ تَأۡخُذُونَهُۥ وَقَدۡ أَفۡضَىٰ بَعۡضُكُمۡ إِلَىٰ بَعۡضࣲ وَأَخَذۡنَ مِنكُم مِّیثَـٰقًا غَلِیظࣰا

    Kuma alhali sun riƙi alƙawari mai kauri daga wurin ku. (Surah An-Nisaa: 21)

    Daga cikin hakan akwai nauyin kula da haƙƙoƙin jaririn da mata suka haifa a kan shimfiɗar mazajen aurensu.

    Dole ne shi kansa miji ya san cewa jaririn da aka haifa masa ba daidai ya ke da rigarsa ko motarsa ko wani kaya mallakarsa ba, wanda yake iya sayarwa ko yin kyauta ko sadaka da shi.

    Ba zai yiwu ya gama biyan buƙatarsa da jin daɗin saduwa da uwar jaririn ba, sannan bayan an samu albarkar auren ya yi ƙoƙarin kaucewa daga ɗaukar nauyin da ke a ƙarƙashin hakan. Allaah Taaala ya ce:

    نِسَاۤؤُكُمۡ حَرۡثࣱ لَّكُمۡ فَأۡتُوا۟ حَرۡثَكُمۡ أَنَّىٰ شِئۡتُمۡۖ وَقَدِّمُوا۟ لِأَنفُسِكُمۡۚ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَٱعۡلَمُوۤا۟ أَنَّكُم مُّلَـٰقُوهُۗ وَبَشِّرِ ٱلۡمُؤۡمِنِینَ

    Kuma su uwaye suna shayar da ’ya’yansu na tsawon shekaru biyu cikakku ga wanda ya so cika shayarwar. Kuma wajibi ne a kan wanda aka haifa masa ciyar da su da tufatas da su yadda yake sananne a shari’a. (Surah Al-Baƙarah: 223)

    A ƙarƙashin wannan ayar malamai suka fitar da hukuncin Ar-Radaa’, watau shayar da jariri:

    1. Matuƙar dai maaurata suna tare da juna, to haƙƙin uwa ce ta shayar da jaririn da ta haifa har na tsawon shekaru biyu cif-cif ko ƙasa da haka, da gwargwadon yadda suka amince ita da mijinta.

    2. Sannan wajibi ne a kan mijin da aka haifa masa jariri ya ɗauki nauyin ciyarwa da tufatarwa ga matarsa, watau mahaifiyar jaririn a tsawon wannan lokacin da take shayarwar.

    3. Lallai ne ciyarwa da tufatarwa su dace da irin ƙarfin tattalin arziƙin mijin, ba tare da ƙoro ba, kamar yadda kuma ba za a ɗora masa abin da ya fi ƙarfin samunsa ba.

    4. Idan kuma sun zaɓi cewa, wata matar ce za ta shayar musu da jaririn, a nan ma dai nauyin biyan albashin mai shayarwar yana a wuyan mahaifin jaririn ne, ba mahaifiyarsa ba.

    5. Sannan ko a bayan rabuwar aurensu ma haƙƙin ciyarwa da tufatar da jaririn ba su faɗi daga kan mahaifin ba.

    A bayan sun yaye jaririn, akwai sauran abin da malaman Fiƙhu suke kira da Haƙƙul-Hadaanah, watau kulawa da tarbiyyar yaro har zuwa lokacin da zai iya ɗaukar nauyin wasu al’amuransa shi da kansa. Allaah ya ce:

    یَـٰۤأَیُّهَا ٱلَّذِینَ ءَامَنُوا۟ قُوۤا۟ أَنفُسَكُمۡ وَأَهۡلِیكُمۡ نَارࣰا وَقُودُهَا ٱلنَّاسُ وَٱلۡحِجَارَةُ عَلَیۡهَا مَلَـٰۤىِٕكَةٌ غِلَاظࣱ شِدَادࣱ لَّا یَعۡصُونَ ٱللَّهَ مَاۤ أَمَرَهُمۡ وَیَفۡعَلُونَ مَا یُؤۡمَرُونَ ٦۝

    Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku tserar da kanku da iyalanku daga wata Wuta, makamashinta mutane ne da duwatsu. A kanta akwai waɗansu malã´iku mãsu kauri, mãsu ƙarfi. Bã su sãɓã wa Allah ga abin da Ya umurce su, kuma sunã aikata abin da ake umunin su. [Suratu Tahrim : 6]

    Abu ne sananne kuwa cewa, tsare iyali daga hakan ba zai samu ba sai da kulawa da tarbiyyarsu, da tsayuwa a kan gyara su, da tsare su daga dukkan munanan ɗabi’u da halaye.

    6. Waɗanda wannan haƙƙin yake hawa kansu a matakin farko su ne iyayen jaririn waɗanda suka haife shi, matuƙar dai suna tare da juna a matsayin miji da mata. Domin babu wanda ya fi su ƙauna da sanin irin abin da zai gyara yaronsu fiye da su.

    7. Amma idan iyayen sun rabu da juna, to a nan ne malamai suka tabbatar cewa nauyin kulawa da tarbiyyar yaron ya koma hannun mahaifiyarsa, matuƙar dai ba ta sake yin wani aure ba. Saboda hadisin Abdullaah Bn Amr Bn Al-As (Radiyal Laahu Anhumaa) da Ahmad (6878) da Abu-Daawud (2276) suka fitar kuma Al-Albaaniy ya hassana shi a cikin As-Saheehah: 368.

    8. Sannan ko a hakan ma nauyin kulawa da ciyarwa da samar da tufafi da sauran kayan buƙatun yaron, kamar kuɗaɗen makaranta da na asibiti da sauransu duk suna a kan mahaifin ne.

    9. Babu abin da zai sauka daga kansa na waɗannan nauye-nauyen sai a lokacin da aka tabbatar ba shi da ikon hakan, kamar saboda larurar taɓin hankali ko karayar tattalin arziki da makamantan hakan.

    10. Idan mahaifi ya kasa, to sai nauyin ya koma a kan dukiyar yaron idan yana da ita, ko kuma a kan dukiyar mahaifiyarsa, kafin sauran jama’ar musulmi. Dubi yadda malaman Fiƙhu suka tattauna matsalar kamar a cikin Tamaamul Minnah: 3/262-274.

    A taƙaice dai, dole kowane mahaifi ya san cewa nauyin da Allaah Ta’aala ya ɗora masa dangane da iyalinsa (iyaye da mata da ’ya’ya da yara da sauran dangi da ’yan uwansa) dole ne ya sauke su gwargwadon ƙarfinsa da ikonsa. Domin tabbas, za a tambaye shi a kansu Gobe Ƙiyamah. Hadisin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) wanda Anas Bn Maalik (Radiyal Laahu Anhu) ya riwaito ya tabbatar da cewa:

    إِنَ اللهَ تَعَالَى سَائِلٌ كُلَ رَاعٍ عَمَا اسْتَرْعَاهُ : أَحَفَظَ ذَلِكَ أَمْ ضَيَعَهُ ؟ حَتَى يَسْأَلَ الرَجُلَ عَنْ أَهْلِ بَيْتِهِ

    Lallai Allaah Ta’aala mai tambayar duk wani makiyayi ne a kan abin da ya ba shi kiwo: Shin ya kiyaye hakan ko ya tozarta shi? Har sai ya tambayi mutum a kan iyalin gidansa. (Sahih Al-Jaami’: 1774)

    Idan kuma duk waɗannan bayanan ba su gamsar da irin wannan mijin ba, bai komo ya cigaba da kulawa da haƙƙoƙinsa ba, to lallai a yi gaggawan ɗaukar maganarsa zuwa ga wani alƙalin musulunci na kirki. Allaah ya ƙara mana taimako.

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.