Hukuncin Mutane Biyu Su Kwana A Shinfada Ɗaya

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum Meye hukuncin mutane biyu su kwana a shinfada ɗaya, shin ya hallata?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

    Amsar wannan tambaya tana a karkashin wannan hadisi na Abdullahi ibn Amr ibn al-Aas (radiyallahu anhu).

    `ﻋﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮﻭ ﺑﻦ ﺍﻟﻌﺎﺹ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ: ﻗَﺎﻝَ ﺭَﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ: ﻣُﺮُﻭﺍ ﺃَﻭْﻟَﺎﺩَﻛُﻢْ ﺑِﺎﻟﺼَّﻠَﺎﺓِ ﻭَﻫُﻢْ ﺃَﺑْﻨَﺎﺀُ ﺳَﺒْﻊِ ﺳِﻨِﻴﻦَ ﻭَﺍﺿْﺮِﺑُﻮﻫُﻢْ ﻋَﻠَﻴْﻬَﺎ ﻭَﻫُﻢْ ﺃَﺑْﻨَﺎﺀُ ﻋَﺸْﺮٍ ﻭَﻓَﺮِّﻗُﻮﺍ ﺑَﻴْﻨَﻬُﻢْ ﻓِﻲ ﺍﻟْﻤَﻀَﺎﺟِﻊِ.

    ( ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ (495) ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ " ﺻﺤﻴﺢ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ"

    An karbo daga Abdullai ibn Amr ibn al-Aas (radiyallahu anhu) ya ce; Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) ya ce; Ku umarci 'ya'yanku da suyi sallah idan sunkai shekara bakwai. Kuma Ku da kesu Idan sunkai shekara goma (basa yin sallah), kuma ku rarraba su a makwancinsu (a raba musu shinfida idan sun kai shekara goma).

    (Abu Dawuda, 495). Albani ya inganta shi a Sahih Abi Dawuda.

    ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨﻮﻭﻱ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ:

     ﻳﺠﻮﺯ ﺃﻥ ﻳﻀﺎﺟﻊ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﻭﻻ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻭﺍﺣﺪ ﻓﻲ ﺟﺎﻧﺐ ﻣﻦ ﺍﻟﻔﺮﺍﺵ، ﻭﺇﺫﺍ ﺑﻠﻎ ﺍﻟﺼﺒﻲ ﺃﻭ ﺍﻟﺼﺒﻴﺔ ﻋﺸﺮ ﺳﻨﻴﻦ ﻭﺟﺐ ﺍﻟﺘﻔﺮﻳﻖ ﺑﻴﻨﻪ ﻭﺑﻴﻦ ﺃﻣﻪ ﻭﺃﺑﻴﻪ ﻭﺃﺧﺘﻪ ﻭﺃﺧﻴﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﻀﺠﻊ.

    "ﺭﻭﺿﺔ ﺍﻟﻄﺎﻟﺒﻴﻦ ( 7/28 )"

    Imam Nawawi (rahimahullah) ya ce: Baya halatta ga namiji ya kwanta tareda namiji (a shimfida guda), ko kuma mace ta kwanta tareda mace (a shimfida guda), koda Ɗayansu yana a gefe ɗaya na shimfidar. Idan yaro ko yarinya suka kai shekara goma, ya zama wajibi a raba yaron (a shimfida) tsakaninsa da Mamarsa, Babansa, yar'uwarsa (kanwa ko yayarsa), da ɗan'uwansa a wajen barci. (Dole ne ya rika kwanciya a shifidarsa shi kaɗai).

    Rawdatul taalibeen, 7/28).

    Saboda haka bai halatta mutum biyu su kwana a shimfida ɗaya ba idan shekarunsu sun kai goma (10).

    Namiji bazai kwanta shimfida ɗaya da wani namiji ba.

    Namiji bazai kwana da wata mace wacce ba matarsa ba a shimfida ɗaya. Wannan haramun ne.

    Mace bazata kwana da wata mace ba a shimfida ɗaya.

    Mace bazata kwana a shimfida ɗaya da wani namiji wanda ba mijinta ba

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.