𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Menene
Hukuncin Sallah Abayan Wanda Yake Luwaɗi?
Kuma menene Ingancin Sallah abayansa?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله.
1. Da farko
idan An Tabbar da Mutum yana Aikata wata Alfasha, bai tuba daka Aikata taba,
kamar wannan babban laifi mai girma, Wajibine Ayiwa mutum wa'azi da nasiha da
tsoratar da shi Allah, Idan yaki tuba wajibine adakatar da shi daka limanci,
acanja shi da limami wanda yake adali tsayayye akan addininsa, Wanda yake
kwadayin Aikata ayyuka na tsoran Allah, Hakika Annabi sallallahu Alaihi
wasallam yahana wani mutum dayayi kaki yatofar agabansa inda Alkibla take yana
cikin sallah, yayi sallah a matsayin shi ne limamin mutanensa ya ce da shi (
Kai kacutar da Allah da Manzansa) Abu dawda (481) Albani yakyautatashi acikin
Sahihu Abu dawda.
Ina kuma ga
mai aikata wannan laifi mai girma, lallai shi ne yafi kamata da can-cantar
ahanashi limancin mutane.!!.
Saboda sanya
shi yazama limami girma mawace agareshi, Fasiqi kuma baya cikin wadanda ake
girmamawa, limami kuma Mutane Suna koyi da shi ne a galibi, suna koyan ilmi
daka wajansa, suna karɓar
Inda yafuskantar dasu a harkar rayuwa kota addini, yana kuma shiryar dasu, duk
lokacinda yazama tsayayye zai kasance yafi kusa da mutane su Amfana dashi, kuma
Sudunga karɓar
zancensa..
Amma idan
yazama fasiqine Mutane bazasu dunga karɓa
daka wajansaba, Saidai ma yazama sababi na lalacewar wasu yafitinesu da irin
nau'in fasikancin dayake aikatawa, Allah ya Tsare.
2. Abu Na
biyu: Ingancin Sallah Abayan fasiqi, Hakika malamai sunyi saɓani akan hakan, Abun da
jamhur din malamai suka tafi akai shi ne: Ingantuwar sallah abayansa tareda
karhancin yinta abayansa.
Imamun Nwawi
acikin Majmu'u fatawa ( 4/151) ya ce:
" Sallar
Abdullahi ɗan Umar
Abayan hajjaju bin yusuf ta tabbata acikin Sahihul Bukhary da waninsa hadisai
masu yawa ingantattu sun nuna ingantuwar Sallah Abayan fasiqi da kuma jagorori
Azzalumai fitinannu.
Malaman mu
sukace: Sallah abayan fasiqi ingantacciya ce ba haramun bace, saidai
makaruhice, haka makaruhice yinta abayan ɗan
bidi'a Wanda bai kafirta da bidi'arsa ba,
Imamu Shafi'i
ya nassanta acikin Muktasar karhancin sallah Abayan fasiqi da dan Bidi'a, idan
kuma mutum yayi ta inganta.
Shaikul Islam
ibnu taimiyyah Allah yajikansa da rahama Acikin Fatawa dinsa (23/341) Ya ce:
" Idan
mutum yana cikin masu kulada addini to wanda yafi sanin Alqur'ani da Sunnah
wajibine agabatar da shi akan wanda bai kaishi ba, idan kuma daya fajirine kamar
wanda aka sanshi da karya da fajirci dacin Amana da yaudara, da sauran nau'ikan
fasiqanci, dayan kuma muminine cikin ma'abota tsoran Allah, to nabiyun shi ne
yafi can-canta. da limanci, idan yana cikin ma'abotanta.
Idan fasiqin
masanine makaranci to lallai Sallah abayan fasiqi an hana, hani na haramci
awajan wasu malamai, awajan wasu kuma hanine na tan-tancewa, bai halatta
jagorantar da fasiqi ba tareda cewa za a iya sanya mutumin kirki.
Yasake cewa a
(23/375)
" Bai
halatta a jagorantar da maishan wiwi ko wanda yake aikata munanan ayyuka ya
limanci mutane ba, tareda cewa za a iya sanya mutumin kirki,.
Malamai Sunyi
ittifaqi akan karhancin Sallah abayan fasiqi, saidai sunyi saɓani wajan ingancin sallar
abayansa, wasu sukace ba ta ingantaba kamar faɗin
Malik da Ahmad a ɗaya
da cikin ruwayotinsa,.
Wasu sukace:
Ta inganta kamar maganar Abu hanifa da Shafi'i, Basuyi jayayya akan bai kamata
sanya shi yazama limami ba.
Duba Sharhin
Mumti'i ala zhadul Mustaqini'i (4/304, 308).
3. Na Uku:
Malamai Sun rarrabe abun da ya waba a'aikatashi akan limaminda yake fasiqi,
Mazinaci mai shan giya dan luwadi ɗan
fashi ɓarayo
makaryaci azzalumi Annamimi da sauran nau'ikan fasiqanci,* ya zo afatawa
Lajnatul da'imah.
" Idan
limamin Masallaci fasiqine yaki jin nasiha wajibine acireshi, idan hakan zai
iyu, fitina bazata faru ba, idan bazai iyuba wata fitinar datafi fasiqancinsa
tana iya biyo baya, wajibine ayi Sallah bayan mutumin kirki wanda ba shi ba,
dan zaburar da shi dakuma tsoratar dashi, idan babu wata fitina dazata biyo
baya akan hakan.
Idan Bazai iyu
ayi sallah abayan wanin saba, yahalatta ai sallah abayansa, dan tabbatar da
Maslahar Al'umma..
Idan Ana
tsoran faruwan fitina sai ayi sallah abayansa dan dakile fitina, da ɗaukar Abun da yafi sauqin
cuta sama dawanda illarsa babbace.
Fatawa
lajnatul da'imah (7/370)
Dan haka
sallah abayan mai luwaɗi
ingantacciya ce Matukar ya iyata, Amma makaruhine, laifin luwaɗinsa shi kaɗai yashafa bazai shafi
ingancin sallar mamu dasuke bayan saba.
Domin Allah
madaukakin Sarki ya ce: Ba'a dora laifin wani akan wani.
WALLAHU A'ALAM
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.