𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu'alaikum
Malam muna lafia, ya dalibai? Allah yayi mana jagora. Amin. Malam Dan Allah a
taimaka a amsa mani wannan tambayar. Malam mutum ne Allah be bashi mijin aure
ba, se aka bashi wani maganin wai rinka sha bayan sallar asuba da Nono wanda
farar yar fulani ke saidawa ko kuma ya haɗa
da yoghurt se yayi addu' a Allah ya biya mashi bukata shi. To Malam menene
hukuncin shan irin abubuwannan, dan ni gaskiya basu kwanta mani ba irin
abubuwan nan ba. Allah ya saka da alheri. Amin
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis
salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Imani da
Qaddara yana daga cikin Ginshikan Imani. Kuma dogaro ga Allah da kuma juyawa
zuwa gareshi ko yaushe yana daga cikin alamomin Imani da Qaddara ɗin.
Wannan abin da
suka ce ki yi ɗin
yana kunshe da surkulle ta ɓangaren
kalar irin Matar da zaki sayi nonon awajenta. Da kuma yanayin yadda za'ayi
amfani da maganin. Don haka ki watsar da irin waɗannan
surkullen. Ki rike Alqur'ani da Sunnar Manzon Allah ﷺ da kuma fa'idodin addu'o'in da Malamai masu
tsoron Allah suka fitar.
Ga sunayen
Allah nan guda 99 duk wacce take neman Mijin aure ta rika yawaita ambaton Allah
da Waɗannan sunayen
sannan tayi Salati ga Manzon Allah ﷺ
sannan tayi addu'arta. Bayan ta gama addu'ar kuma sai ta Qara maimaita salati
ga Manzon Allah ﷺ.
Akwai hadisi daga Manzon Allah ﷺ
cewa Duk wanda ya kira sunan Allah "YA AR-HAMAR RAHIMEEN" Sau uku, to
wani Mala'ika zai tsaya kusa da shi yace masa "GA ARAHMANUR RAHIMEENA NAN
YA JUYO GAREKA". Nan take duk abin da mutum ya roka Allah zai amsa masa.
Ki riki waɗannan addu'o'in ki kyale
waɗancan abubuwan.
Allah zai yaye miki damuwarki, Zai biya miki bukatarki.
WALLAHU
A'ALAM.
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.