𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin ya
halatta mace ta sha magani don Nonuwanta ko kuma Ɗuwawunta suƙara girma ko ta kara kiba idan ta kasance ramammene?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Dangane da
hukuncin shan magani domin neman ƙara ƙiba ajiki ko kuma dan saboda wani sashe
na jikin Mutum yaƙara girma kamar misali Mace tasha magani danufin Nonuwanta
kokuma Ɗuwawunta
suƙara girma, bayanin da Malamai sukayi akan haka shine,
akwai wanda yahalatta agareshi yasha maganin ƙara ƙiba, akwai kuma wanda haramunne agareshi
yasha wannan magani, wato ya dangantane da niyya ko sababin da yasa za'ayi
amfani da wannan magani.
Idan yaka sance
Mutum yana da wani aibu ko naƙasa ajikinsa wanda yawuce irin wanda aka
saba ganin Mutane da shi abisa al'ada, kamar misalin Mutumin da yayi asari
(Accident) wani sashe na jikinsa ya lalace ko wanda haƙoransa suka fito waje
dayawa zaƙo-zaƙo,
ko yaka sance Mutum arame yake sosai irin ramewar da tawuce wadda aka saba gani
a al'ada, kuma koda yanacin abinci maigina jiki haka yake baya ƙaruwa to ayanayi irin wannan Malamai sukace idan
masana kiwon lafiya (Likitoci) suka bashi shawarar cewa yasha maganin ƙara ƙiba
to ya halatta yasha, kokuma ayiwa Mutum aiki dan akawar da wannan aibu ko naƙasar
dake tare dashi, domin anyimasa hakane danufin akawar da wannan naƙasa
dake tare dashine kawai danhaka babu laifi.
Amma idan yaka
sance babu wata naƙasa ajikin Mutum irin naƙasar da tawuce wadda aka saba gani abisa
al'ada, Saidai kawai Mutum zaisha maganin ƙara ƙibane danufin yaƙara masa kyau, kokuma
Mace tasha magani danufin Ɗuwawunta suƙara girma ko danufin Nonuwanta suƙara
girma idan yaka sance ƙananane, kokuma arage musu
girma idan sun kasance Nonuwanta manyane sosai, domin taƙara
kyau dan tariƙa burge Mutane:, kokuma saboda kasancewar Mutum bashi da jiki
sosai acikin abokansa sai yakeso yasha magani danufin jikinsa yakoma irin nasu,
da dukkan wani wanda zeyi amfani dawani magani danufin yaƙara
kyau bawai wata larura bace mai tsanani tasa yabuƙatu da dole sai yayi hakanba, to dukkan
waɗannan abubuwa da
makamantansu haramunne aikatasu, domin yashiga ƙarƙashin hukuncin masu jirkita halittar Aʟʟαн(ﷻ) domin dama Shaiɗan yafaɗa cewa sai ya umarci
Mutane suna jirkita halittar Aʟʟαн(ﷻ) kamar yadda Aʟʟαн(ﷻ) Yafaɗa acikin wannan aya:
وَلَآمُرَنَّهُمْ فَلَيُغَيِّرُنَّ خَلْقَ اللَّهِ ۚ
Sai na
umarcesu da suriƙa jirkita halittar Aʟʟαн(ﷻ) (sūratun Nisá'i : 119)
Danhaka abune
mai matukar haɗari
haka kawai Mutum yace zaisha maganin kara kiba danufin yakara kyau, yakamata
asani cewa, duk yadda Mutum yakaiga rena kansa to ahakan shi abin sha'awane
awajen wasu Mutanen, hakanan kuma duk yadda Mutum yakaiga jirkita halittarsa
danufin yakara kyau, to ko rabin-rabin kyaun wani bazai taɓa kaiwa ba, danhaka
garama Mutum ya hakura da yadda Mahaliccinsa ya halicceshi sai yazauna lafi
lafiya.
Don neman
karin bayani sai aduba wannan littafi kamar haka:
"
فتاوى إسلامية" (4/412)
WALLAHU A'ALAM
AMSAWA:
Mυѕтαρнα Uѕмαи
08032531505
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.