Hukuncin Taƙaita Sallama (Abbreviation)

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalaamu Alaikum warahmatullah. Allah ya karawa malam lafiya da ilimi mai amfani. Malam dan Allah menene hukuncin abbreviating sallama, hamdala da kuma rantsuwa a shari'ah? Misali: Assalmu Alaikum (SLM) Wa'alaikum salam (WSLM) wallahi (WLH) Alhamdulillah (ALHDL) Sallallahu Alaihi Wasallam (S.A.W) dasauransu. Menene hukuncin rubuta waɗannan kalmomi in shortform?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh.

    Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

    Tabbas amfani da abbreviation ko kuma shortform na kalmomi abu ne da ya zamo ruwan dare a duniyar musulmi, har ya kai ga jumloli da sunan Allah da salatin Annabi duk ba su tsira ba a hannun masu yin hakan.

    Ko shakka babu yin amfani da taƙaita sunan Allah, salati, sallama da ababen da suke ibadah ne, bai halatta ba, duba da wasu dalilai kamar haka.

    Misali, idan mu ka ɗauki sallama, addu'a ce, ibadah Sunnah ce da Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) ya koyar mana a lafzance da rubuce. Don haka duk wanda ya zo da saɓani haka ya munana biyayya ga Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) kuma ya yi Bid'ah.

    Lokacin da Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) ya rubuta takarda zuwa ga wasu sarakuna bai taƙaita sallama ba, bayan bismillah, da shi da mai rubuta masa, babu wanda ya yi abbreviation na kalmomi ballantana jumloli da aka yi amfani da su.

    2820 - 1294 - «بسم الله الرحمن الرحيم من محمد عبد الله ورسوله إلى هرقل عظيم الروم سلام على من اتبع الهدى أما بعد; فإني أدعوك بدعاية الإسلام أسلم تسلم يؤتك الله أجرك مرتين فإن توليت فإن عليك إثم الأريسيين و {يَا أَهْلَ الْكِتَابِ تَعَالَوْا إِلَى كَلِمَةٍ سَوَاءٍ بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمْ أَلَّا نَعْبُدَ إِلَّا اللَّهَ وَلا نُشْرِكَ بِهِ شَيْئاً وَلا يَتَّخِذَ بَعْضُنَا بَعْضاً أَرْبَاباً مِنْ دُونِ اللَّهِ فَإِنْ تَوَلَّوْا فَقُولُوا اشْهَدُوا بِأَنَّا مُسْلِمُونَ} » .

    (صحيح) ... [حم ق ت] عن أبي سفيان. مختصر مسلم 1122.

    Na biyu, yana haifar da rashin fahimtar saƙo, misali, ana amfani da AA, A/A, SLM, WSLM, duk waɗannan ba za su bayar da ma'ana ba a musulunce ko a al'ada ba.

    Bayan haka shari'a ta tabbatar da cewa zuwa da cikakkiyar sallama yana da ƙarin lada da fifikon falala a kan wanda bai da cikakkiya ba, toh ina ga wanda ya zo da abin da shari'a ba ta san da shi ba?

    Daga ƙarshe dai, mu gane cewa rubutu, zance ne, kuma Allah zai kama mu da laifukan abin da muka faɗi da harsunan mu ko kuma muka rubuta da hannayen mu. Don haka ragi ko ƙarin harafi a cikin abin da ya shafi sunan Allah ko abin da ya shar'anta, ilhadi ne.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.