Hukuncin Wanda Ya Manta Sujjadal Kabliyyah

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    As-Salaam Alaikum. Idan Sujudul Ƙabliyyah ta samu mutum, kuma ya manta bai yi ba har sai da ya yi sallama, yaya zai yi?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Ramatul Laah:

    Asali dai idan mutum ya yi ƙari a cikin sallah Sujada Baadiyyah yake yi. Idan kuma ragi ne ya yi, ko ragi da ƙari a haɗe sai ya yi Sujada Ƙabaliyyah.

    Sannan idan mutum ya manta da Sujadar Ba’adiyyah malamai sun yarda cewa, lallai ya yi ta a duk lokacin da ya tuna. Haka ma Ƙabaliyyah da ya manta bai yi ba sai a bayan sallama ya tuna, malamai sun yarda ya yi ta a bayan sallamar, ta zama Ba’adiyyah kenan.

    Ko ba komai dai, akwai malaman da suka yarda da halaccin yin kowanne daga cikin Sujadar ko Ƙabaliyyah ko Ba’adiyyahi a kan kowace irin Rafkanuwa:

    Al-Haafiz Ibn Hajr ya ce:

    وَرَجَّحَ الْبَيْهَقِيُّ طَرِيقَةَ التَّخْيِيرِ فِي سُجُودِ السَّهْوِ قَبْلَ السَّلَامِ أَوْ بَعْدَهُ وَنَقَلَ الْمَاوَرْدِيُّ وَغَيْرُهُ الْإِجْمَاعَ عَلَى الْجَوَازِ وَإِنَّمَا الْخِلَافُ فِي الْأَفْضَلِ وَكَذَا أَطْلَقَ النَّوَوِيُّ.

    Al-Baihaƙiy ya rinjayar da hanyar zaɓi a cikin Sujudar Rafkanuwa kafin sallama ko a bayan sallama. Kuma Al-Maawardiy da waninsa daga cikin malamai sun ciro ijma’in malamai a kan halaccin hakan. Sun yi saɓani ne kawai a kan wanda ya fi. Haka kuma shi ma An-Nawawiy ya faɗi maganar a sake. (Fat-hul Baariy: 3/94).

    Shi kuma An-Nawawiy ya ce:

    قَالَ الْقَاضِي عِيَاضٌ رَحِمَهُ اللَّهُ تَعَالَى وَجَمَاعَةٌ مِنْ أَصْحَابِنَا: وَلَا خِلَافَ بَيْنَ هَؤُلَاءِ الْمُخْتَلِفِينَ وَغَيْرِهِمْ مِنَ الْعُلَمَاءِ أَنَّهُ لَوْ سَجَدَ قَبْلَ السَّلَامِ أَوْ بَعْدَهُ لِلزِّيَادَةِ أَوِ النَّقْصِ أَنَّهُ يُجْزِئُهُ وَلَا تَفْسُدُ صَلَاتُهُ وَإِنَّمَا اخْتِلَافُهُمْ فِي الْأَفْضَلِ، وَاللَّهُ أَعْلَمُ .

    Al-Ƙaadiy Iyaadh (Rahimahul Laah) da waɗansu daga cikin malaman mazhabarmu sun ce: Babu saɓani a tsakanin waɗannan malaman da suka saɓa wa juna da waɗansunsu cewa, ya wadaci mutum idan ya yi sujada kafin ko a bayan sallama domin ƙari ko ragi, kuma sallarsa ba ta ɓaci ba. Saɓaninsu dai kawai a kan wanda ya fi ne. (Sharhun Nawawiy: 5/56-57).

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.