Hukuncin Yaɗa Sallama Tsakanin Mata Da Maza

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum Inada tambaya, tambayata gata kamar haka Allah gafarta malam ina cikin tafiya a matsayina na namiji sai na tarar da mata a hanya toh ko zan iya yimasu sallama??

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

    Da farko dai Allah ya umarcemu da yaɗa sallama a tsakaninmu ya kuma wajabta mana mayarda sallama ga daukacin musulmai. Ya sanya sallama ta zama wani abu da ke yaɗa soyayya a tsakanin muminai. Allah ya ce:

    وَإِذَا حُيِّيتُمْ بِتَحِيَّةٍ فَحَيُّوا بِأَحْسَنَ مِنْهَا أَوْ رُدُّوهَا ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ حَسِيبًا ٦٨۝

    Kuma idan an gaisheku da wata gaisuwa, to, kuyi gaisuwa da abin da yake mafi kyau daga gareta, ko kuma Ku mayar da ita, kuma Allah ya kasance akan dukkan komai mai lissafi. [Al-Nisa'i 4:86]

    An ruwaito Abu Hurairah ya ce; Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) ya ce: bazaku shiga aljannah ba har sai kunyi imani, baza kuyi imani ba har sai kunso junanku. Shin bazan gaya muku wani abu ba wanda idan kunyi shi zakuso junanku?, Ku yaɗa sallama a tsakaninku, zaku so junanku"

    (Muslim ne ya ruwaito shi a hadisi mai lamba 54).

    Umarnin yaɗa sallama umarni ne ga kowa (maza da mata) kuma ya shafi dukkan musulmai. Ya haɗa da maza suyiwa maza sallama, mata suyiwa mata sallama, da sallama tsakanin muharraman juna. Anan an shar'anta sallama a tsakanin wannan sashe ya yi sallama ga ɗayan sashen da ya aka wajabta ma mayar da sallama.

    Amma akwai hukuncin da ya hana namiji yin sallama ga macen da ba muharramarsa ba idan ya ji tsoron aukuwar fitina a dalilin wannan sallama.

    Babu laifi ga namiji ya yiwa mace sallama batareda yin musabaha da ita ba, idan ita tsohuwa ce. Amma bazai yiwa wacce ba tsohuwa ba sallama idan baida tabbacin rashin aukuwar fitina. Wannan shi ne sharhin malamai Allah ya yi musu rahama.

    An tambayi Imam Malik shin za a iya yiwa mace sallama? sai ya ce: "Idan tsohuwa ce ban ga karhanci a sallamar ba, amma idan ba tsohuwa ba ce bana son haka"

    Al-Zarqaani ya yi bayanin dalilin da ya sa imam malik ya ce baya son haka, a sharhinsa na Al-Muwatta: Saboda yana tsoron fitina idan ya ji muryarta idan za ta mayar da sallama.

    Acikin (Al-Adaab al-Shar'iyyah 1/370) ance:

    Ibn Muflih ya kawo cewa Ibn Mansoor ya tambayi Imam Ahmad akan yiwa mata sallama sai ya ce: Idan matar tsohuwa ce babu laifi.

    Saalih (Dan Imam Ahmad) ya ce na tambayi babana akan yiwa mata sallama sai ya ce: sallamar da ta shafi tsofaffin mata babu laifi, amma wadanda ba tsofaffi ba baza'a sa suyi magana ba wajen mayar da sallama.

    Al-Nawawi ya ce acikin littafinsa mai suna Al-Adhkaar a shafi na 407) cewa: Sallamar mata ga mata yan uwansu kamar sallamar maza ne ga maza. Idan macen kuma matarsa ce ko baiwarsa ko muharramarsa, to kamar shi ne yake yin magana da wani namiji. Saboda haka za su yiwa juna sallama haka mayarwa.

    Amma idan wata mace ce daban kuma tanada kyau, kuma yana jin tsoron za ta fitineshi, to shi bazai yi mata sallama ba, idan kuma ya yi mata sallama, to bai halatta ta amsa masa ba. Hakanan itama bazata yimasa sallama ba, idan ta yi masa bazai amsa mata ba, idan ya amsa to ya yi makaruhi.

    Idan akwai taron mata, namiji zai iya yi musu sallama. Haka idan taron maza ne za su iya yiwa mace sallama matukar akwai yaqinin cewa dasu da ita babu Wanda zai fitinu.

    An ruwaito daga Asma bintu Yazeed (radiyallahu anhaa) tace; Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) ya wuce ta wajenmu (Mata) sai ya yi mana sallama.

    (Abu Dawood, 5204). Albani ya ingantashi a Saheeh Abi Dawuda.

    Al-Haafiz ya ce acikin Al-Fath: Akan halaccin sallama tsakanin mata da maza: Abin da ake nufi da ya halatta shi ne idan babu tsoron fitina.

    Al-Haleemi yana cewa Saboda Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) Ma'asumi ne kuma an kiyaye shi daga fitina. Duk wanda keda yaqinin ya tsira daga fitina, to zai iya yiwa mata sallama. Idan kuma akasin hakan ne, to ya tsare kansa ya yi shiru.

    An ruwaito Al-Muhallab yana cewa: Ya halatta maza suyiwa mata sallama haka mata suyiwa maza sallama idan babu fitina.

    Domin Neman karin bayani duba:

    (Ahkaam Al-Awrah wa'l-Nazar na Musaa'id ibn Qaasim al-Faalih.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.