Hukuncin Yanke Wa Mace Farce A Gaban Mijinta

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Na ji amsar Fatawa a kan matan da suke miƙa hannuwansu da ƙafafunsu ga waɗansu maza su yanke musu farce, to tambaya ta ita ce: Idan a gaban mijinta ne fa? Watau kamar ta kira mai yankewa ya yanke mata amma mijinta yana kallo?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

    A asali zamansu a haka tare su uku ba laifi ba ne. Keɓancewa a tsakanisu ce aka hana.

    « لاَ يَخْلُوَنَّ رَجُلٌ بِامْرَأَةٍ إِلاَّ كَانَ ثَالِثَهُمَا الشَّيْطَانُ »

    Wani namiji bai taɓa keɓancewa da wata mace ba face kuwa na-ukunsu ya zama sheɗan ne. (Sahih Al-Jaami’: 2546).

    Shafar jikinta da mai yakan ƙumbar zai yi ce matsala ko da kuwa da izinin mijinta ne, domin kusantar zina ce wanda kuma haram ne, kamar yadda Ubangijinmu Ta’aala ya ce:

     وَلَا تَقۡرَبُوا۟ ٱلزِّنَىٰۤۖ

    Kuma kar ku kusanci zina. (Surah Al-Israa’i: 32).

    Sai dai ko in akwai larura, kamar likita da zai karɓi haihuwa ko kuma wacce zai yi wa aiki, a inda mijinta ko wani muharraminta ba zai iya.

    A nan kuwa babu irin wannan larurar.

    Domin ko da ita ba za ta iya yanke ƙumbunanta ita da kanta ba, ai wata matar kamar abokiyar zamanta ko ƙawarta ko yarta ko yaruwarta tana iya yi mata, kamar yadda ta ke yi mata kitso, misali. Idan kuma hakan bai yiwu ba, sai mijinta ko ɗanta, ko dai wani muharraminta daga cikin maza ya yi mata. Amma ban da ma’aikacin gidanta, kamar mai gadi ko direba ko mai wanki da sauran duk wanda shari’a ta amince yana iya auren wannan matar in ba domin tana da miji ba.

    Allaah ya ƙara mana shiriya da fahimta a cikin addininmu.

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.