Ticker

Hukuncin Yin Sallah A ɗakin Da Bangonsa An Lilliqeshi Da Hotuna

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin ya halatta ga musulmi yayi sallah aɗakin da bangonsa an lilliqeshi da hotunan mutane da dabbobi? kuma ya halatta musulmi yayi sallah darigar datake da hoto?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله وحده لا شريك له.

Baya halatta yin sallah a gurin dayake akwai hoton abubuwa masu rai sai inda lalura, saboda Abun da bukhari yaruwaito acikin sahihin littafinsa, (3322) da muslim ( 2106) daka Abi dalha Allah yakara yarda da shi daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: ( Mala'iku basa shiga gidan dayake akwai kare ko hoto acikinsa)

An tambayi fatawa lajnatul da'imah shin yahalatta ga musulmi yayi sallah aɗakin da bangonsa an lilliqeshi da hotunan mutane da dabbobi? shin kuma yahalatta musulmi yayi sallah darigar datake da hoton dabbobi?

Sai suka Amsa: Hotunan Abubuwa masu rai haramunne, sanya hotunan abubuwa masu rai a jikin bangwan ɗaki haramunne, haka yin sallah aɗakin da bangwansa akwai hoton abubuwa masu rai ba ta halatta saida lalura, haka yin sallah da tufafinda yake da hotunan dabbobi ko hoto mai rai bai halatta, saidai idan mutum yai sallar ta inganta tareda haramcin yinta awajan, yatabbata daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ( lokacinda yaga labulen ɗakin A'isha yana da hotuna yai fushi ya yayyagashi ya ce: ma'abota waɗannan hotunan za a dunga azabtar dasu ranar alkiyama ana cewa dasu ku rayar da abun da kuka halitta).

Fatawa lajnatul da'imah ( 1/705).

Saboda haka wanda yai sallah aɗakin da yake da hoto a jikin bango yana fuskantar bangon da hoton yake, sallarsa tayi, Amma kuma haramcin saka hoton da haramcin yin sallah awajanda yake da hotuna yana kansa za a rubuta masa zunubi akan hakan, abun da yake wajibi gareshi shi ne tuba da istigfari zuwaga Allah, sannan ya gaggauta cire hoton daka ɗakinsa dan samun yardar ubangijinsa Allah maɗaukakin sarki, Allah yakara shiryar damu baki ɗaya.🤲

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments