𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mecece
gaskiyar magana game da cewa wai ba a yin sallama ga mutumin da yake cin abinci
ko yake karatun Alƙur'ani?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Alalhaƙiƙa
sallama wani abu ne mai ƙima da kuma daraja a tsakanin 'yan'uwa musulmai, shi ya sa
shari'a take kwaɗaitar
da mu cewa mu riƙa yaɗa
sallama a tsakanin mu, domin yawan yaɗa
sallama yana ƙara soyayya da ƙauna a tsakanin 'yan'uwa musulmai kamar
yadda Mαnzon Allαh(ﷺ)
Ya ke cewa:
"لا تدخلوا الجنة
حتي تؤمنوا، ولا تؤمنوا حتي تحابوا، أولا أدلكم علي شيء إذا فعلتموه تحاببتم؟ أفشوا السلام بينكم" (رواه مسلم)
MA'ANA:
(Annabi(ﷺ) Ya ce:) ba za ku shiga
Aljanna ba har sai kunyi imani. Kuma ba za ku yi imani ba har sai kun ƙaunaci
junanku. Shin ba na shiryar da ku zuwaga abin da idan kun aikatashi zai sa ku
riƙa
son junanku? Ku yaɗa
(ku yawaita) sallama a tsakaninku:
Sannan kuma kamar
yadda shari'a ta tabbatar da cewa fara yin sallama Mustahabbi ne amma kuma amsa
ta wajibi ne, danhaka ke nan wanda ya fara yin sallama to ya fi wanda ya amsa
ta yawan lada, shi ya sa Malamai sukace a cikin dukkan ayyukan Ibada duk abin
da yake farilla ne ko wajibi to ya fi yawan lada akan wanda yake sunna ne ko
kuma mustahabbi, to amma a ɓangaren
sallama sai ya kasance mustahabbi ya fi farilla yawan lada.
Amma dangane
da hukuncin yin sallama ga mai cin abinci ko karatun Alƙur'ani, an samu wasu
daga cikin Malamai da suka ware waɗansu
abubuwa kamar guda (14) ko sama da haka waɗanda
suke ganin cewa makaruhi ne a yiwa Mutum sallama idan ya kasance a ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa kamar haka:
1-Idan Mutum
yana cikin cin abinci ko kuma wani abin sha.
2-Idan Mutum
yana cikin yin zakiri kamar hailala, tasbihi, ko kuma karatun Alƙur'ani.
3-Idan Mutum
ya shagaltu da karanta Hadisan Mαnzon Allαh(ﷺ)
sukace shi ma makaruhi ne a yi masa sallama.
4-Idan Mutum
yana cikin yin wata lakca ko tunatarwa.
5-Idan Mutum
yana cikin karantarwa ko yana ɗaukan
darasi kamar na ilimin Alƙur'ani ko Hadisi ko kuma Fiƙ-hu.
6-Idan Mutum
yana cikin yin wani bincike na Ilimi to shi ma makruhi ne a yi masa sallama saboda
kada a shagaltar da shi.
7-Idan Mutum yana
cikin yin wa'azi ga Mutane.
8-Idan Mutum
yana cikin yin muzakara (Mai-maita karatu) na ilimin da yaje ya koyo.
9-Idan Mutum
yana cikin yin ƙiran sallah (Azan).
10-Idan Mutum
yana cikin yin Sallah.
11-Idan Mutum
yana cikin yin Alwala.
12-Idan Mutum
yana cikin yin hira da wani mutum shi ma sukace makruhi ne a yi masa sallama
don kada a katse shi.
13-Idan Mutum
yana cikin biyan buƙatarsa kamar fitsari ko kashi.
14-Idan Mutum
yana cikin yanayi na yaƙi da abokan gaba.
To sai dai
kuma waɗansu daga
cikin Malamai sukace gabaɗayan
waɗannan abubuwa da
su waɗancan Malamai
suka ambacesu babu nassi ko guda ɗaya
da suka dogara da shi a kansa wanda yake tabbatar da maganarsu. Danhaka ke nan
maganar cewa makaruhi ne ba ta ma taso ba, danhaka waɗannan abubuwa su na nan a asalinsu na
halacci (Mustahabbi) domin nassosin da suka zo sukayi magana akan hukuncin
sallama (عام) ne
Kuma ba a samu
wani nassi da ya yi (تخصيص)
Na waɗancan abubuwan
ba, sannan Malamai sukace wani Sahabi ya yiwa Mαnzon Allαh(ﷺ) sallama a ya yin da
yake sallah, sai Mαnzon Allαh(ﷺ)
ya amsa masa amma ta hanyar yin ishara da hannunsa (✋🏽),
sai Malamai sukace idan kuwa har za a yiwa Mαnzon Allαh(ﷺ) sallama yana sallah kuma bai hana ba, to (من باب أولي)
A yiwa mai cin abinci da kuma mai karatun Al-ƙur-ani sallama.
Danhaka dai
magana mafi inganci ita ce ya halatta suma a yi musu sallama:
шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ
Mυѕтαρнα Uѕмαи
08032531505
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.