Ticker

    Loading......

Idan Ɗalibarsa ta yi Masa Laifi Sai ya ce Horonta Shi ne Ta Daho Abinci Daga Gida Ta Kawo Masa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Malami ne a makarantar Islamiyyah idan ɗalibarsa ta yi laifi ko ta makara sai ya ce, horonta shi ne ta daho abinci daga gidan mijinta ta kawo masa gobe! Mene ne hukuncin wannan a musulunci?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Domin ilimin da malami ke bayarwa ya samu shiga kuma ya zauna daram a cikin zukatan ɗalibansa har su iya amfana da shi, ya zama tilas wajibi ga malami ya zama mai mutunci da daraja a idon ɗaliban, a ko’ina kuma a kodayaushe.

Kodayake bayar da kyauta da karɓar kyauta sun halatta a tsakanin malami da ɗalibi a bisa wasu ƙaidoji da malamai suka sani, amma dai dole su kasance ta hanyar girmamawa da mutuntawa, ba ta hanyar roƙo ko bara ko dabara da wayo masu janyo wulaƙanci da zubar da mutunci ba.

Ko yara ƙanana za su iya gane cewa, wannan malami mayunwaci ne kuma mai mugun kwaɗayi da ƙwalama ne kawai. So kawai ya ke ya roƙi ɗaliban su riƙa kawo masa abinci, amma sai ya ɓoye a bayan wai horo yake bayarwa!

Sannan kuma wannan matar da ya ce yana horar da ita da hakan matar auren wani ne fa. Irin wannan aikin shi ke janyo waɗansu mazaje su yi zargi wani abu a tsakanin malamin da matan, musamman idan wani ya kama matarsa tana shirya wani abinci na musamman. Tun da dai ba za ta yarda ta kai abinci mara kyau zuwa makaranta ba.

Sannan kuma wace amsa wannan malamin zai bayar a lokacin da aka zarge shi da koya wa ko tilasta wa ɗalibarsa satar kuɗi ko satar kayan abincin miji?

In da gaske malamin nan yake yi meyasa ba zai bayar da hardar waɗansu shafuka daga cikin littafin karatu, ko kuma ya tilasta wa masu laifin kwafe waɗansu shafuka a cikin littafinsu na rubutu ba, a misali?

Wajibi ne wannan malami ya ji tsoron Allaah, kuma ya tsare mutunci da darajar aikinsa. Ya sani fa cewa: Larura ce ta sanya ya zama mai karantar da ajin mata. Shiyasa yawancin makarantu yanzu suka fara raba malamai maza daga koyar da ajujuwan mata, don kawar da irin wannan abin.

Allaah ya shiryar da mu.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments