TAMBAYA (30)❓
Assalam malam
antashi lafiya,Allah ya karawa rayuwa albarka. Ina tambaya,mal Ina yawan
mafarkin miyagun mutane nabina, sai dasun biyoni sai intashi sama,toh malam da
inatashi da bacci tsoro nakeji,yanzukuma tsoro da bacin rai sukahade DANALLAH
miye nufin hakan? Jazakallahu khairan!
AMSA❗
Idan kikai
mafarki kina tseren-tsere da wani, sai kikai nasarar tsere masa (ma'ana bai
kamaki ba) to hakan yana nufin zaki yi nasara akan maqiyinki kuma zaki fi shi
daukaka. Mafarkin tashi a sama daga inda ka sani zuwa waje me nisa inda baka
sani ba yana nufin mutuwarka.
Idan mace ta
yi mafarki tana tashi a saman gidansu wani saurayi wanda ta sani hakan yana
nufin za ta aureshi. Mafarkin tashi daga kasa zuwa sararin sama ba tareda
fuka-fukaiba na nufin burin mutum zai cika. Idan mutum ya yi mafarkin yana
kwance akan gwado kuma shi da gadon sun tashi sama hakan na nufin rashin
lafiyarsa ko kuma wata rashin lafiya da za ta samu kafafunsa. Idan mutum ya yi mafarkin
tashi sama daga waje mara kyau zuwa waje mai kyau kamar gona ko masallachi
hakan na nufin samun riba mai kyau a sana'arsa
SHARHI
Kowa a
duniyarnan yanada maqiyi, kuma indai yanda kika fada ne cewar kin ga miyagun
mutane suna binki, sai kiga kin tashi sama, to hakan na nufin kina tsira daga
sharrinsu silar yawan azkar
Don haka ki ci
gaba da azkar na safiya da na maraice
Annabi SAW ya
ce duk wanda zai karanta "A'uzu bi kalimatillahit tamma min kulli
shaidanin wahamma wamin kulli aynin lamma" sau 3 da safe sau 3 da yammaci,
to ba abin da zai iya cutar da shi a wannan ranar har sai abin da Allah SWT ya
rubuta masa. Kuma an rawaito cewar Annabi SAW yana yiwa jikokinsa (Hassan da
Hussaini) irin wannan addu'ar kamar ynda ya zo a cikin hadisin Sahihul Bukhari
mai lambata 3371
Dukkan halittu
(khaliqai) basuda tasiri akan sauran halittu saidai su zamo sabab (sila) amman
al-Khaliqu shi kadai ne yake saka tasiri ko da sila ko kuma da QudirarSa
Ki dage da
neman kariya daga sharrin mahassada da miyagun mutane
Kada ki manta
da addu'o'in da Annabi SAW ya koyar ya yinda mutum zai kwanta bacci kamar
irinsu Mu'awwidathayn (Falaqi da Nasi a kara da Ikhlas sau uku uku a shafe jiki
ya yin kwanciya bacci) kamar yanda hadisin Sahihul Bukhari mai lambata 5748 ya
tabbatar da hakan
Domin kuwa
miyagun mutane suna amfani da wannan lokaci su turowa mutum abin da kan iya
cutardashi idan bai yi azkar ba
Annabi SAW ya
ce: "Babu abin da ke sauya qaddara sai addu'a"
Allah ya
karemu ya rabamu da sharrin kawunanmu, miyagun mutane da kuma sharrin shaidan
Wallahu ta'ala
a'alam
Amsawa:
Usman Danliti
Mato (Usmannoor_As-salafy)
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.